SO KO WAHALA? PART 58

17 5 0
                                    

*HAƊAKA WRITER'S ASSO...🖊️*

*❤️😭SO KO WAHALA?😭❤️*
      
               NA

MARYAM M SANI (Mum Amnash)
*WATTPAD: @mumamnas2486*

*TALLA! TALLA!! TALLA!!!*

Shahararriya kuma haziƙar marubuciyar nan taku AMEERA ADAM ta sake zuwar muku da wani ƙayataccen littafi mai ɗauke da rikici da tirka tirka, ƙulle-ƙulle da makirci mai suna *ANYA BAIWA CE?* Anya Baiwace littafine na gidan sarauta, kuma littafin kuɗi ne. Ga mai buƙata zai same shi a farashi mai sauƙi kamar haka👇👇👇
Normal Group: #200
VIP GROUP: #400
ACCOUNT: First Bank 3090957579 AISHA ADAM
SHAIDAR BIYA TA: 07062062624
Amma don Allah don Annabi (S.A.W) idan kin san za ki fitar mata da littafi gwara a haƙura👏

                5️⃣8️⃣

11/R-Auwal/1443 - 9/10/2021

Hannayenta ya kama gam sannan yace "Ki yi haƙuri, in dai Yaya Kabiru ne zai yi fin haka. Abu ƙalilan za ka yi masa ya mayar da allura garma." Sai da ya furzar da iska sannan ya ɗora "Ke ma da laifinki, nasha kwaɓarki a kan makancewa a so, amma ina, sai ki ƙi ji ki ƙi gani sai kin wahala sannan ki saduda. Allah ya kyauta."
"Amin"
"Ba za ki tambayeni ni mai ya haɗa ni da shi ba?"
"Na san ko ban tambaya ba za ka faɗa mini ai."
"Haka ne." Ya furta yana jan jelar gashinta.

WANE NE ISAH?

Isah ɗa ne ga Alhaji Abdullahi (Abbanmu) da Hauwa (Mama). Su Biyar  Mama ta haifa Yaya Kubra tana zaune a Gombe, sai  Yaya Sadiya tana zaune a Dutse, sai Yaya Kabir, Zuhra (Aunty) sai Auta Isa. Duk Matan suna gidajen aurensu da ƴaƴansu.

Duk kusan haife haifen da Mama ta yi tare su ke yi da Hajiyan Khamis, sai dai ita ƴaƴanta maza sun fi yawa. Mata biyu gareta Maza biyar.

Isa yaro ne mai hazaƙa da basira, ya yi ilimin boko har matakin masters (digiri na biyu) Ilimin Addini ma ya yi tun daga Makarantar Allo har  ya yi sauka a Islamiyya da Allon don a tare ya dinga haɗawa.

Isa mutum ne mai barkwanci da sakin fuska, sai dai sam baya son hayaniya, ko abokai bashi da su da yawa. Abokan Khamis sune abokanshi, sai kuma na Makaranta da na unguwa.

Ba shi da sana'a sai gyaran wuta da kayan lantarki. Banda wannan ba abin da yake sai kwanciya a ɗaki. A wasu lokutan kuma yana kamawa Mama da Aunti aikin gida.

Shi da Leema sun shaƙu matuƙa gaya, saboda yanda take yawan zuwa gidansu ta yi kwanaki. Har wasu na zaton ita ƴar gidance. Har zuwa lokacin da Allah ya nuna ikonsu suka zama Mata da Miji.

MU DAWO LABARI

"Kamar yanda ki ka sani rikicinmu da Yaya Kabiru a kan aiki ne. Bayan na kammala digiri yace na je na same shi a Abuja ya yi wa wani ubangidansa magana za a sama mini aiki. Ba musu na saka kayana a Jaka na ɗau takardu ranar alhamis na dira a gidansa na Abuja da yamma. Ban daɗe da zuwa ba ya dawo. Muka gaggaisa girma-girma ya tusar baƙo, sai yace gobe da safe za mu fita tare, muka yi ta hira gwanin sha'awa."

Sai da ya huta sannan ya ɗora "Da daddare duk muka haɗe a teburin cin abinci, rashin sabo yasa na zauna a gefe na ce a ƙasa zan ci. Ƴar sa ta fari  Farha ta kawo mini abincin, kuskus ne ɗan yakot a faranti. Ban ce komai ba na fara ci, kan ka ce kwabo na siɗe. Amma daga Yaya Kabiru har Matarshi Farida babu wanda ya tambayeni ko na ƙoshi. Takaici ya sa na tattara ya nawa ya nawa na koma ɗakin da a ka sauke ni, na bar su suna ciye ciyen kayan ƙwalamarsu. Tun da na kwanta cikena ke kiran ciroma, abinka da ɗan tsohuwa. Amma haka na daure har bacci ɓarawo ya sace ni."

Leema ya kalla yace "Dariya ki ke yi mini ko?"
"A'a Yayana ja mu je."
"In taƙaice miki washe gari tun da na yi sallar Asuba ban iya komawa barci ba, don na riga na saba kullum ni da Mama Shida da rabi ko Bakwai na safe muke karyawa. Ko da na shiga Jami'a kafin na tafi sai na karya sannan na ƙara karyawa Zuwa goma ko Sha ɗaya.  Tun ina jira a ce Isa zo ga rabashe har na gaji na nufi madafar da ke tsakar gidan. Mai girkinsu na kalla nace "Bawan Allah wai har yanzu ba ka sauke sanwa ba?"
A maimakon ya bani amsa sai ya fara zare ido kamar an jijjiga ɓera a buta. Ganin bai gane abinda nake nufi ba, sai na ƙara maimaita masa tambayar da harshen nasara. Sannan ya bani amsa wai iya girkin ƴan makaranta Farha da Samha ya yi. Da na mu da na Yaya Kabiru sai anjima za a girka. Ban ƙara bin takanshi ba na fice rai na a ɓace.  Mai gadinsu na bawa ɗari biyu ya siyo mini biredi, na shiga kitchen ɗin na ɗau bota na lanbata na ci da ruwa."
"Me yasa baka girka da kanka ko kasa kukun ya girka maka ba."
"Kamar ba ki san halin matar gidan ba, ai komai kaffa-kaffa take yi da shi, daga Mijinta har dukiyarsa, idan a son samunta ne daga ƙauri sai gwiya. Ga ta tsani ka yi wa ƴaƴanta faɗa, wannan yasa ta tsaneni ko a dangi don fata-fata na ke yi wa su Farha idan suka yi laifi. Ranar da na je da gudu suka rungume ni, sam hakan bai yi mini ba amma na maze kawai. Wani ɗan uwanta ya zo shima Farha ta faɗa jikinsa har da kwanciya. Ai ko yana tafiya a gaban uwarta na yi mata faɗa, baki ga yanda ta hau ba kamar fulawar da aka baɗawa yis. Da na yi rashin Sa'a a ranar da za mu fita tare a ka kira shi daga ma'aikatarsu a ka tura shi zuwa Lagos. Ganin har litinin bai dawo ba, na tattara ya nawa ya nawa nawa na koma gida. Ko da na faɗawa Mama ba tace komai ba ta ja bakinta ta tsuke. A can Abuja kuwa ina tahowa Yaya Kabiru ya dawo, ganin bana nan ya fusata sosai. Matarshi ta ƙara tunzurashi ya kira waya ya zazzage ni."

SO KO WAHALADonde viven las historias. Descúbrelo ahora