SO KO WAHALA? PART 62

31 5 0
                                    

*HAƊAKA WRITER'S ASSO...*🖊

*AMNASH JOINING ORDER*👇👇👇
[10/18, 12:07 PM] Mum
Amnash: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/EiQ3qtht0QSLRElOcqt3CP

*❤️😭SO KO WAHALA?😭❤️*
      
               NA

MARYAM M SANI (Mum Amnash)
*WATTPAD: @mumamnas2486*

*TALLA! TALLA!! TALLA!!!*
Shahararriya kuma haziƙar marubuciyar nan taku AMEERA ADAM ta sake zuwar muku da wani ƙayataccen littafi mai ɗauke da rikici da tirka tirka, ƙulle-ƙulle da makirci mai suna *ANYA BAIWA CE?* Anya Baiwace littafine na gidan sarauta, kuma littafin kuɗi ne. Ga mai buƙata zai same shi a farashi mai sauƙi kamar haka👇👇👇
Normal Group: #200
VIP GROUP: #400
ACCOUNT: First Bank 3090957579 AISHA ADAM
SHAIDAR BIYA TA: 07062062624
Amma don Allah don Annabi (S.A.W) a riƙe amana👏

12/R-Auwal/1443 - 18/10/2021
                6️⃣2️⃣

Da ƙarfin tsiya ya kutsa cikin mutane ya kamo Isa ya rungume, hawaye na gudana a kuncinshi. Da taimakon wanda ya kirawo shi da Jabir suka sa shi a mota. Da gudu ya finciki motar ya nufi A.K.T.H, Jabir na baya rungume da Isa duk rigarshi ta ɓaci da jini. Ganin haka ya sa ya ɗora hannunshi a kan ciwon don tare zubar jinin. Suna zuwa a ka yi ɗakin taimakon gaggawa da shi, sai da ya dawo hankalinshi sosai a ka yi masa allurar barci sannan Khamis ya kira Aunty da Yaya Kabiru ya sanar da su.

Kuka Aunty ta dinga sharɓa wiwi, da yake Alhaji a gidanta yake shi ya rarrasheta ta shirya suka nufi Asibitin.

Duban Khamis Alhaji ya yi yace "Khamis ka wuce wurin aikinka kawai, zan jira ya farfaɗo sai mu wuce gida. Tunda ciwon da sauƙi sosai, jinin ya daina zuba."

"To Alhaji bari na tafi, Insha Allahu da rana zan dawo."

"Zo Khamis." Alhaji ya kira shi, duban fuskarshi ya yi yaga yanda ya yi zuru-zuru ga ɗan jini ya ɓata masa gefen rigarsa.

"Khamis ka koma gida ka canja kaya ka nufi wurin aikinka. Duk da kana da uzuri kwana biyu kana wasa da aikinka, hakan bashi da alkhairi duk da kana da uzuri mai ƙarfi. Ka yi haƙuri nan kusa abokinka zai samu lafiya ka ji."

"Allah ya sa" ya furta ya fita da sauri idanunshi sun yi jawur.
Haka suka zauna har azahar sannan ya farfaɗo, nan ma ban da sambatu babu abinda yake. Sai bayan Azahar Alhaji ya tafi ya bar Aunty a wurinshi.

BAYAN SATI ƊAYA

Lamarin ciwon Isa ya ƙara ta'azzara, da ba don tsananin addu'a ba, da kai tsaye haukacewa Isa zai yi, don bala'in da ake kunno masa ba ɗan ƙarami ba ne.

Duk yanda Bala ya so Boka Ƙudugis ya bashi haɗin kai ya illata Isa gaba ɗaya, abin ya ƙi yiwuwa. Tilas ya ɗauki shawarar wani hatsabibin abokinsa, ya  canja boka, ganin Ƙudugis na da shakka da tsoro a kan sha'anin. Abokinsa ne da yake zaune a kudu ya haɗashi da Obi, kuma Allah ya ara masa dama don aikin ya ci, ko yana ma kan ci a kan Isa.

Yaya Kabiru bai zo ba sai ƙarshen sati, sosai hankalinshi ya tashi ganin abinda ke faruwa. Dole ƙanwar na ƙi ya ɗauki masu gadi guda biyu ya ajje su a gidan. Don idan Isa ya zabura Mama ko Aunty ba sa iya riƙeshi, sai dai su yi ta kuka.

Tun ran Alhamis Aunty ta kira Leema tace ta yi zamanta ba sai ta zo ba. Har za ta musa mata, ganin abinda zai fusata Aunty bashi da yawa ya sa ta tsuke bakinta ta haƙura, dama laulayi ya sata a gaba dauriya kawai take, kuma ba wanda ta faɗawa.

Ranar Asabar kuwa ƴan gidansu suka yo zuga suka zo duba Isa, duk da wasu sun zo tun kwanciyarsa ta farko a Asibiti. Ba don Leema ta so ba ta biyo su, bisa umarnin Mahaifinta da ya rufe ta da faɗa a kan tace ba za ta je ba.

SO KO WAHALAМесто, где живут истории. Откройте их для себя