SO KO WAHALA? PART 6

53 5 0
                                    

*HAƊAKA WRITER'S ASSOCIATION*🖊️

*❤️😭SO KO WAHALA?😭❤️*

                   NA

MARYAM MUHAMMAD SANI(Mum Amnash)
WATTPAD@mumamnas2486

             ▶️6️⃣

13/Shauwal/1442 - 25/5/2021

         Sai da su ka gaisa sannan Leema ta dubi Baban Mama tace "Baban Mama wannan shi ne Haseen ,wanda zan aura insha Allah. Haseen ga Baban Mama da na faɗa maka."

   Cikin farin ciki Haseen ya miƙa masa hannu su ka ƙara gaisawa ,daga nan su ka dasa hira duk su ukun,yawancin hirar akan kasuwanci ce. Sai kusan ƙarfe tara da rabi, sannan kowa ya shiga motarshi ya wuce.

   BAYAN WATA BIYU

   Ba ƙaramar shaƙuwa  Leema da Baban Mama su ka yi ba, don har gidanshi ta je. Sannan ta je ta gaida mahaifiyarsa ma da ta ke zaune a Ɗorayi.

   Wasu lokutan Leema har kayayyaki ta kan bashi ya kaiwa Mama. Mai ɗa wawa, hakan ya sa ba ƙaramin girmamata Hindu ta ke ba, zumunci ya ƙullu sosai a tsakaninsu . Su kan yi waya lokaci zuwa lokaci.

    Soyayyar Leema da Haseen ku wa sai abinda ya ƙaru, don ta riga ta yanke shawara shi za ta Aura . Har ta gabatar da shi a wurin mahaifanta a kaduna.

  ******************

    "Amman Haseen idan ka tafi yaushe za ka dawo, ni fa ba na son bin hanyar Abujar nan da mota wallahi. Mai ya sa ba za ka bi jirgi ba?"

  Sai da Haseen ya yi murmushi sannan ya ce "Haleematus-sadiya me ki ke tunani ,ba abinda zai faru sai alkhairi insha Allah. Nima na yi tunanin bin jirgin ,amma sai naga gara na je a mota, na dawo a jirgin kamar zaifi. Insha Allahu da na dawo zan turo magabata ayi-ayi na huta da wannan zaryar."

    Za ta ba shi amsa, Anti ta fito daga cikin gida za ta shiga ɓangarenta . Cikin mutuntawa su ka gaisa sannan ta shige ɓarinta.

  Sun daɗe da Haseen su na hira, sannan ya mata sallama ya tafi. Jikinta a sanyaye ta miƙe ta shiga gida. Washegari kuwa tun Asiba ta nufi Zaria , wurin aikinta.

   Dukkan mai rai mamacine! kuma kowacce rai da ajalinta idan ya zo ba za'a ƙara mata ko da daƙiƙa ɗaya ba. Kafin su ƙarasa gadar Abuja ,motar su Haseen ta bigi dutse ta  faɗa ruwan da ke gefen titin. Cikin gaggawa mutanen ƙauyen da ke gefen ruwan su ka firfito , su ka shiga don ba su agaji. Wasu kuma su ka kira ƴan kwana-kwana, kan ka ce kwabo su ka ƙaraso .

    An samu nasarar fitar da su duk gabaɗayansu ,sai dai tun da aka zaro Haseen bai numfasa ba ko sau ɗaya. Duk ƙoƙarin da likitocin su ka yi a kansa, bai farfaɗo ba. A bincikensu sun gano ya sa mu buguwa a kansa , banda wannan ba abinda ya same shi . Ko kurjewa bai yi ba, ko ruwa bai shiga cikinsa sosai ba . Kai tsaye su ka sanar da ƴan sandan da su ka kawosu . 

   Tsayawa faɗar ruɗun da Leema ta shiga ɓata baki ne ,ta yi kuka iyya yinta . A ƙarshe ta fawwalawa Allah ta dangana. Duk zaman makomin Haseen kusan da Baban Mama aka yi ,sosai shi ma ya ji mutuwar Haseen . Don Haseen mutum ne ,sai dai matsalarshi ta saurin fushi . Wannan ko dama ɗan adam tara ya ke bai cika goma ba .

   Tun da Haseen ya rasu ,Baban Mama ya ke ba wa Leema kulawa ta musamman. Kusan a kullum ya na kiranta sau biyu, a hankali shaƙuwa mai ƙarfi ta shiga tsakaninsu.

    LABARIN BABAN MAMA

   Yunusa Ɗalhatu shi ne cikakken sunan Baban Mama. Asalin kakanninsa ƴan ƙasar Kamaru ne kasuwanci ne ya kawo su ƙasar Najeriya. Anan duk su ka hayayyafa, su ka tara jikoki da ƴaƴa har Allah ya yi musu rasuwa.

   Mahaifin Baban Mama ƴar Zawaciki ya aura , ƴaƴansu uku  da shi Sa'ada, Yunus (baban Mama) sai ƙaramar ƙanwarsu Fatima ,Allah ya yi masa rasuwa.

   Bayan rasuwarshi da shekara ɗaya ƙaramar ƙanwarsu Fatima ta rasu ya rage su biyu ne jal da shi da yayar shi.

    Rayuwar matsi ,talauci da ƙaƙanikayi ba irin wadda ba su gani ba . Amma a hakan Baban Mama ya daure ya ɗaura ɗanbar yin karatu mai zurfi. Yayarsa kuwa Sa'adatu ,wani ɗan uwansu da ya zo daga Kamaru, ya nuna ya na sonta . Da mahaifiyarsu ta ƙi ,amman dangin Babansu su ka yi caaa dole ta saki . A ka yi auren ya tafi da ita can Kamaru ya rage daga shi sai babarshi da su ke kira da Inno .

Allah ya taimaka Inno ta sami wani bazawari ta aura anan ɗorayi , su ka yi zamansu da Yunus. Da daɗi ba daɗi haka Inno ta daure zama da wannan bawan Allah cikin ikon Allah suka haifi Ƴaƴa har ukku. Daga nan haihuwar ta tsaya mata.
  
   Kusan ba sana'ar da Bai yi ba, tun daga ɗiban ruwa,dako ,tallah duk yunus ya yi don ya tara kuɗin makaranta. Cikin ikon Allah ya kammala karatunshi tsaf a B.U.K Kano, ya karanci Phamacy.

      Ya na kammalawa ya samu aiki, a wani shahararren kamfanin da ya ke samar da magunguna .

  Wata ɓoyayyiyar baiwa da Baban Mama ya ke da ita ,ita ce ta iya zane-zane . Ba abinda ba ya iya zanawa ko ya ƙirƙira. Wa su daga cikin abokanshi har sha'awar karantar ɓangaren zanen gidaje su ka masa . Amman Allah bai nufa ba.

   Shekarar shi ɗaya da fara aiki ya je Kamaru don dubo yayarshi sosai da sosai ta ji daɗi . Anan maƙotansu ya haɗu da Hindu su ka ɗaura alaƙar soyayya. Dama kuma su na da ƴar dangantaka ta kakanninsu. Itama iyayen Hindu  da su na Najeriya a Jahar Borno, yawaitar rigingimun boko haram ya sa, su ka koma Kamaru da zama.

    Kamar a yi kamar ba a yi ba, a ƙarshe dai bayan shekara biyu. A ka yi auren Hindu da Baban Mama ,su ka tare a Gwazaye.

   Shekara ɗaya da Aurensu Hindu ta haifi ƴarta mace, aka sa mata sunan Inno Saudat. Yarinyar baƙa ce kamar iyayenta ,sai dai tabarkallah ta na da farin jini sosai. Don kusan kullum ba ta yini a gida, a hannun su Hadizan Hajiya ta ke yini, tsakaninta da Hindu sai dai ta ba ta mama.

   A tsakanin wannan lokacin ,a ka rufe kamfanin da  Baban Mama ya ke aiki. Sosai su ka shiga tashin hankali don ma ,ya na da tattali ya na da kuɗi sosai a account ɗinshi . Wanda ya ci burin sayen gida da shi .

  Sha'awarar abokinshi Dr zayyad ya bi, dole ya nemi kasuwancin da zai fara. Dr ya haɗa shi da ƙaninshi Aminu, su ka fara gwada kasuwancin kayan sawa musamman atamfofi da lesuka. Wannan ya sa ba ya zama sosai, ya na kuma tafiya zuwa wa su garuruwan don ɗabbaƙa kasuwancin shi.

   Duk lokacinda ba ya nan sai zaman ya ishi Hindu ,don ma ƴaƴan maƙotanta su na shigo mata. Izini ta nema a wurin Baban Mama ya yarje mata , ta ke shiga gidan Hajiya maƙotanta. Idan dare ya yi kuma sai ƴanmatan Hajiya biyu su biyota gidanta don su tayata kwana.

  Hindu mace ce mai saurin yarda , musamman ga maƙotanta su Hajiya, yanda ta ke ɗaukar Hajiya tamkar uwar da ta  haifeta. Babu wani sirrinta da ta ke ɓoyewa Hajiya, ko shawara sai abinda Hajiya ta zaɓar mata. Sannan ƴarta ta shaƙu da Hadiza, shi ya sa ta sakar musu sosai ba abinda ba sa yi a gidanta. Da zarar Baban Mama ya dawo za su tattara ya nasu ya nasu , sai kuma ya sake wata tafiyar.

****************

    "Baban Mama don Allah ina son ka barni na je ganin gida, ka ga rabona da can tun arba'in ɗin Mama fa."

   Wata dariya ya sa ya ce "Kina ba ni mamaki Hindatu to ke banda abinki , idan kin tafi da wa zan zauna? Ba zan barki ki tafi ba ,tunda in kika tafi sai kin share sama da wata Uku. Wancan karan nasan me na ji, idan kuma kinga na barki sai dai idan kin yarda na ƙara aure."

Wani abin mamaki ,murmushi ya ga ta yi tace "Wallahi da na ji daɗi sosai da sosai ni idan ka yarda ni zan zaɓa  maka matar da za ka aura . Kaga shi ke nan ,sai ka barni na yi tafiyata ."

"Anya Hind kina so na kuwa? To wa ce ki ka zaɓa min? Karfa daga baya ki zo ki kuka da kanki." Ya ƙare ya na son tabbatar abinda ta faɗa.

ALLAH YA GAFARTAWA IYAYENMU

MUM AMNASH🖊️

SO KO WAHALAWhere stories live. Discover now