SO KO WAHALA? PAGE 42

30 6 7
                                    

*HAƊAKA WRITER'S ASSO...🖊️*

*❤️😭SO KO WAHALA😭❤️*

                   NA

MARYAM MUHAMMAD SANI (Mum Amnash)

22/Al-muharram/1443 -      31/8/2021

          4️⃣2️⃣

Sai da ta nemi wurin zama sannan tace "Kamsusi Amara ƙirjin biki, ka kasa zama guri guda, wai ba kun gama shirya komai ba ne?" Fuska ya ɗan tsuke yace "Haba Aunty
, Amara kamar wata mace, ina ma laifin ki ce Aminin Ango. Yauwa Aunty gwara da ki ka zo, don idan ba ki jawa waɗannan mutanen kunne ba tsaf za su yarfa mu." Dariya Aunty ta yi tace "Khamis ka cika maimaita magana kamar tsoho, na riga na gama da wannan batun ka manta kawai."

  Tsam Khamis ya miƙe yace "Yauwa Aunty nima bari na tashi, ina da abin yi." A tare suka miƙe da Isah suka nufi waje suna ɗan tattaunawa.

"Khamis ba ka faɗa min shirye shiryen da ku ka tsara ba." Wata dariyar rainin hankali Khamis ya yi yace "Anjima ka gani, tunda ka mayar dani sakarai, nima bani da lokacinka." Bencin da ke gefensu Isa ya zauna ya zabga tagumi zuciyarshi cunkushe da tunani iri-iri.

Wani irin daɗi ne ya ƙume Leema lokacin da ta ji sallamarsu Zahra da ƙawayenta biyu, sai kuma zugar ƴan gidansu manya da yara. Ƙanƙamesu ta dinga yi cike da farinciki. Kai tsaye a sashin Aunty suka sauka, itama Leema ta tattaro kayanta ta dawo cikinsu, a ka cigaba da caccafkewa.

Zuwa ƙarfe ɗaya na rana gidan ya cika danƙar da Jama'a, sosai Hajiyar Khamis ta gayyato ƴan unguwar don su shaida auren Autan Mama.

  ***********

   Tun ƙarfe uku masu gyara waje suka zo, nan da nan suka kammala da yake sun kai su biyar. Zuwa ƙarfe huɗu da rabi Abokan Ango suka cika harabar gidansu Khamsusi, Ango kawai suke jira.

  Amarya Leema kuwa sosai ƴan uwanta suka yi mata faɗa, tilas ta ɗan saki ranta Zahra ta yi mata kwalliya mai sauƙi. Doguwar riga ta sanya, sai ta ɗora alkyabbar da aka yi mata ado da fulawoyin jikin atamfar. Takalma filat tasa sam bata wani cika ado a fuskarta ba, amma tayi kyau masha Allah. Zahra na fesa mata turare wayarta ta ɗau ruri, ajiye kwalbar ta yi a gefe ta ɗaga wayar "Ok ai mun gama tun ɗazu, zaku iya zuwa" ta ajiye wayar tace "Ya kamata mu miƙe Abokan Ango sun ƙaraso, Haleema ki tashi ku jera da Angonki." ta ƙare zancen tana dariya.

Miƙewa ƙawayensu suka yi, suka saka Amarya a tsakiya. Duk ƙwaƙwar mutum, ba zai hangi fuskarta ba don ta jawo hular alkyabbar sosai ta rufe rabin fuskar. Jefa ƙafarta kawai take yi, amma zuciyarta da tunaninta suna wani wurin daban. Zungurinta Zahra ta yi tace "Haleema kalli Angonki wallahi ya haɗu ƙarshe, gaskiya wani hanin ga Allah baiwa, kai..." Ƙarasowarsu Isah da Khamis ne yasa Zahra ta tsuke bakinta.

Ɗago da idanunta ta yi , karaf ƙwayar idanunsu suka gauraya, ras! Gabanta ya faɗi,  wani irin masifaffen kyau taga Isa ya yi, Shadda ce Shuɗiya mai haske (Blue sky)a jikinshi, an yiwa babbar rigar matsakaicin aiki da shuɗin zare mai duhu (dark blue), iyakar abinda ta gani kenan, ba zato taji ya kama hannunta. A hankali take ƙoƙarin zame hannun, sai da ya ɗan rage tsahonshi  sannan ya sa hannu ya janye mata hular alkyabbarta baya, muryarshi a ƙasa sosai yace "Me ki ke nufi? Ko kina son ki tabbatarwa da kowa ba auren soyayya muka yi ba? Kin dai san..." Khamis ne ya matso yace "Haba ku taho mu ƙarasa ana jiranmu fa, Haleema ki yi haƙuri ba daɗewa za ki yi ba, don taron namu ne na maza, hotuna kawai za ayi kiyi tafiyarki." Ba musu suka jera, Abokan Ango a gefenshi su Zahra a gefen Amarya. Gaba ɗaya wurin ya ɗau sowa da tafi, ta tsakiya suka ratsa har bakin gadon da aka tanada dominsu, sai da  suka zauna sannan ya cika mata hannunta. Ajiyar zuciya ta sauke da ƙarfi, har sai da Isah ya juyo ya zuba mata ido, amma sai ta ɗauke kai kawai.

SO KO WAHALAOnde histórias criam vida. Descubra agora