SO KO WAHALA? PAGE 49

40 5 12
                                    

*HAƊAKA WRITER'S ASSO...🖊️*

*❤️😭SO KO WAHALA?😭❤️*

                    NA

MARYAM MUHAMMAD SANI (Mum Amnash)
*WATTPAD: mumamnas2486*

3/Safar/1443 - 10/9/2021

            4️⃣9️⃣

  "Haleema za ki iya zama na two hours (Sa'o'i biyu) na je gida na dawo, ko za ki shirya mu tafi? Yaya Kabiru ne ya ke kira na, anjima kaɗan zai tafi."

Idanunta taf da hawaye tace "Ba wata damuwa ka yi tafiyarka, ka gaida su Mama."

Da sauri ya shiga ɗaki ya sanya kayanshi ya fice daga gidan, ranshi a cunkushe.

Tun da ya fita Leema ta cigaba da kuka, tana danasanin mallakawa Isa kan ta da ta yi. Tasan masifar Yaya Kabiru zai yi wuya ba a kan zancen aurenta da Isa ya zo ba, don lokacin da a ka yi baya ƙasar, kuma babu wanda ya sanar da shi.

  Yana sauka daga adaidaita sahu, ya tarar da Khamis a ƙofar gidan. Murmushin ya yi yace "Ango barka da fitowa, ai na ɗauka sai wani satin za mu ƙara ganinka." "Khamis bari na shiga ciki, kiran Mutuminka, ko za ka zo muje?" Tsalle Khamis ya yi yace "Wa ni? Rufa mini asiri, idan ka ganni a lahira kai ni a ka yi. Nima da tamu da shi, shiyasa tun da naga motarshi a waje na kasa shiga gidan. Hajiya ce ta aikoni wurin Mama, yanzu da na koma za ta tiso ni a gaba ta kai ni wurinshi. Gwara na zauna idan ya fito na gaisheshi a tsaye na yi wuf na shige gidan."

Dariya Isa ya yi yace "Ashe a na tsoron inna..." "Ba ko tantama" Khamis ya faɗa yana dariya.

A tsakar gida ya tarar da Mama da Aunty, duk ya tsugunna ya gaishesu, suka amsa cike da farin cikin ganinshi. Yana ƙoƙarin miƙewa, Yaya Kabiru ya fito fuskarshi a murtuke kamar hadarin gabas, har ƙasa Isa ya tsugunna yace "Yaya ina kwana?" "Lafiya ƙalau, nemi wuri ka zauna. Wannan karon a gaban Mama za a yi komai, kar na tafi ka ƙulla mini wani sharrin."
  
Murmushi Isa ya yi ya zauna a tabarmar da ke shimfiɗe a tsakar gidan.

"Mene ne sana'arka?" Kai tsaye Isa yace "Gyare-gyare da buge-buge na ke yi, kuma Alhamdulillahi Khamis ya nemo mini wuri a Kasuwar Farm center zan fara zuwa."

Wani mugun tsaki ya ja yace "Ka ji haushin halinka, wai buge-buge kamar wani ɗan tasha, kai wane irin shasha ne? Ok tsaya ma tukunna, a matsayina na madadin ubanka me yasa ka tafi ka yi aure ba tare da ka sanar da ni ba.  Baka da kunya ko kaɗan, nace ka kaimin takardunka (CB) ka jirani na two days (kwana biyu) ka ƙi jira kai ga Ɗan sarki Fahat ka ɗebo jiki ka dawo gida. Kai kenan sai dai ka kwanta na nemo ka ci, ba za ka amfanawa kanka ba, ba za ka amfanawa wani ba. Wace Yarinya ka  aura?"

Duk da yanda zuciyarshi take tafasa, haka ya daure yace "Haleeman Mama ta Kaduna..." "What! (Me!) kana nufin wannan ƴar iskar yarinyar ka aura? Ban san lalacewar taka har ta kai nan ba, wannan yarinyar ko ni mai shakaru Arba'in da biyar tafi ƙarfina ballantana kai. Kai wane irin gidahumi ne da za ka auri Mace sa'arka, da kamila ce ma da sauƙi shashashar yarinyar da tarbiyya ta yi wa ƙaranci za ka ɗauka a matsayin Matar Aure. Ba laifi ka je ku zauna, ko me ya biyo baya ba hannuna a ciki, tunda ko auren babu wanda ya sanar da ni, a yanar gizo na tsinci hotunan, ban ma gane ta ba an yi mata kwalliya kamar birinya, da nasan ita ce da babu abunda zai kawo ni a kan wannan maganar. Yauwa ka je ka ƙarata ka yi tayi, shashasha, sokon banza."

Ban da hawaye babu abinda Isa ke yi, da ma yasan haɗuwarsu da Yaya Kabir ba za ta yi kyau ba don mutum ne mara fahimta.

Gyaran murya Mama ta yi tace "Kabiru tun da ka sauka ba ni hankalinka nan, wannan duk faɗan ba Isa za ka yi wa ni za ka yiwa, saboda ni na shiga na fita nasa a ka ɗaura musu aure ba tare da shawartar Isa ba."

SO KO WAHALAKde žijí příběhy. Začni objevovat