SO KO WAHALA? PART 26

40 2 0
                                    

*HAƊAKA WRITER'S ASSOCIATION*

*❤️😭SO KO WAHALA?😭❤️*

           NA

MARYAM MUHAMMAD SANI(Mum Amnash)
WATTPAD@mumamnas2486
BLOGSPOT@mumamnash.blogspot.com
*Watsapp link* https://chat.whatsapp.com/Gty1kpVjvrb2myAy87gOou

28/Zulƙida/1442 - 7/72021

       2️⃣6️⃣

Murmushi Aunty ta yi tace "Masha Allah Amarya yanzu muke shirin zuwa gidannaku ai,   Baban Mama barka da rana"

Kasa amsawa yayi kawai ya zube gwiwoyinsa a ƙasa yayi shiru.

Inno tace "Ai shigowa ciki za ka yi sosai, don abin bana tsugunne bane, kai tsaya ma me yasa zaka taho da wannan yarinyar? Kwata-kwata ko sati biyu ba tayi a ɗakinta ba amma ka ɗebota kun taho, ni bana son shashanci."

Kalaman Inno sun ɓatawa Hadiza rai, amma ganin da baƙi sai ta nemi gefen gadon Inno ta zauna, ta bawa su Auntu baya tana karkaɗa ƙafa cike da izza.

Baban Mama kuwa kasa zama ya yi sosai, banda lugude ba abinda ƙirjinsa ya ke yi, don yasan halin Aunty musamman idan aka tsokano ta. Daurewa yayi ya gaida Aunty, kadaran kadahan ta amsa, sannan tace "Yunusa muhimmiyar magana ce ta kawo mu, duk da nasan kaima ka gane hakan don ruwa baya tsami banza. Za muyi magana a sirri ko za ka yiwa Madam magana ta bamu wuri?"

Kafin yace komai Hadiza tace "Hajiya ba na jin akwai wani abu da ya shafi mijina da ba za a yi a gabana ba, don mun riga mun zama ɗaya ni dashi, saɓanin wancanenka. Ko da yake ance wai inda aka san darajar koko a can ake farau-farau, bari kiga..."  iyafis ta zaro a jakarta ta sanya shi a wayarta ta fara sauraren waƙa tana rangaɗa kai kamar ƙadangaruwa.

Da ido Inno tayi ta yiwa Baban Mama magana kan ya fitar da Hadiza, amma ina shi baima gane me takeyi ba. A haka har suka shafe minti huɗu ba wanda yace komai, duk yanda ya so su haɗa ido da Leema abin yaci tura don tamkar bata wurin, ko inda ya zauna bata ƙara kalla ba.

Aunty ce tayi gyaran murya tace "To Bayin Allah mu dai ba zama muka zo ba, don haka ina ga bari muyi abinda ya kawo mu, mu wuce. Yunusa ina son na tambayeka don Allah don Annabi akwai kuɗin Haleema a hannunka?" Kai tsaye ya amsa, don a ganinsa ai bashi hanji ne kuma yana cikin kowa "Eh akwai kuɗaɗenta a wurina, ɗaya na kasuwancin da muka yi sai kuma na adashi."

Murmushi Aunty tayi tace "Hajiya Inno kin fara jin ƙamshin gaskiya a kan maganata?" Inno dai ba baka sai kunne, don jikinta ya mutu murus ga kunyar da ta lulluɓeta, kai kawai ta ɗaga alamun yarda da batun Aunty.

Idanunta ta mayar gefen Hadiza, ganin ta zubo mata ido yasa ta saki murmushi, a take Hadiza ta ɓata rai ta soma magana ƙasa-ƙasa da ba a jin abinda ta ke faɗa(Ƙunƙuni).

Aunty ba ta kulata ba tace wa Baban Mama "Bari na yi maka gwari-gwari Yunusa, ina kuɗin Haleema, ina alƙawarin da ku ka yi za ka dinga bata duk wata? Rashin ɗaukar wannan alƙawarin da muhimmanci shi ya janyo mata duk jidalin da take ciki a yanzu. Kwata-kwata ba kuɗi a hannunta, da ba don Allah ya taƙaita ba da tuni tana ofishin Ƴansanda. Don haka salin alin ka bamu dubu ɗari yanzu mu yi gaba. A da niyya na yi idan ka zo na maka wankin babban bargo, amma saboda wani dalili na janye na ke binka da lallama, ka fita ka kawo min kuɗi salin alin." 

"Don Allah Aunty ki yi haƙuri, wallahi banyi da nufi ba. Haleema ki yafe min, uzururrukan biki da nayi shi yasa kikaji shiru amma zan baki kuɗinki cif cif da yardar Allah."

Bai jira cewarsu ba ya fice da sauri kanshi na ɗan juyamai.

  Ganin haka yasa Hadiza ta fara magana ƙasa ƙasa ganin ba wanda ya kulata yasa tace "Kawai dai wannan baƙin ciki ne wallahi, anga ya aure ni bai auri wata ba, kawai sai a wani ce ana binsa kuɗi, don a hanamu more rayuwarmu. Ni wallahi duk girman mace in tamin sai inci kut..."

SO KO WAHALADonde viven las historias. Descúbrelo ahora