SO KO WAHALA? PART 51

29 5 0
                                    

*HAƊAKA WRITER'S ASSO...🖊️*

*❤️😭SO KO WAHALA?😭❤️*

                   NA

MARYAM MUHAMMAD SANI (Mum Amnash)
*WATTPAD: @mumamnas2486*

10/Safar/1443 - 17/9/2021

               5️⃣1️⃣

   Jikinshi a sanyaye yace "Babansu Musbahu Abokinmu ne ya rasu. Zan tafi Insha Allahu ba zan jima ba zan dawo." Da sauri ya ɗora alwala ya tafi.

  Jagwab Leema ta zauna a kujera, babu abinda take tunawa sai uwar wahalar aikin da suka sha. Kallo ta kunna don rage kewa, ba ta tashi ba sai da a ka kira sallar Magriba. 

Isa bai dawo ba sai Takwas da rabi, lokacin har ta fara gyangyaɗi a kan kujera. Da sauri ta miƙe tana murza idanuwanta, don ta ɗan tsorata.

A gefenta ya zauna yace "Ki yi haƙuri ban dawo da wuri ba, har kin fara barci ko?"
"Gyangyaɗi dai na fara. Yauwa ya za a yi da wannan abincin?"
"Haɗe mini shi wuri ɗaya, na fita na nemi Almajirai na basu." 

A kwando ta zuba filas ɗin shinkafar da miyar , ta miƙa masa fuskarta a cunkushe. Karɓa ya yi ya fuce da sauri, don layin na su ya yi tsit ba hayaniyar Mutane.

Waige-waige ya farayi, a tsaye ya hango Malam Ɗalha yana kai kawo. Da sauri ya ƙarasa wurinshi ya russuna yace "Malam barka da dare"
"Barka kadai" Ya amsa fuskarshi ɗauke da busasshen murmushi. 
Kan Isa a ƙasa yace "Don Allah Malam wace Makarantar allo ce take kusa? Abinci muka dafa mai yawa za mu yi baƙi, to kuma sai Baban Abokinmu ya rasu, shi yasa ba su samu damar zuwa ba."

Kan Malam Ɗalhatu a ƙasa yace "Am...am... ba nisa Makarantar, daga layi na biyu bayan na mu akwai Makaranta. "
"Na gode Malam. Bari na yi sauri na je, dare na ƙara yi."

Har Isa ya kai ƙarshen Layin ya juyo, cak ya tsaya ganin Malam na biye da shi. Kan Malam a ƙasa yace "Malam Isa idan ba takura don Allah ka bani na bawa Yara tun ɗazu suke damuna."

Jikin Isa a sanyaye yace "Ba komai Malam, mu je na rakaka da shi." Har ƙofar gida ya raka shi, sannan ya juya a sanyaye ya nufi gida. Zuciyarshi cushe da tunanin halin da Magidanta ke ciki a wannan lokacin.

Yana shiga gidan ya ji Baba tana mita "Aradun Allah gwara zaman ƙauye a kan na birni, a ƙalla dai da daddare mutum zai gantsari tuwonsa miyar kuka da daddare. Da safe a ja ɗumame, da rana kuwa ko zogale a ka cakuɗa da ƙuli tsaf zai riƙe ciki, musamman a kora da kunun Goma ko Ashirin." Ɗaya daga cikin Jikokinta ne yace "Ke Baba kin cika mitar tsiya, ga ki dai tsohuwa amma kaf gidannan babu wanda ya kai ki rakin yunwa. Idan ba kya son zaman nan ɗin ba sai ki koma ƙauye ba. Wa ya riƙe ki? Duk lalacewar Masa ai tafi kashin shanu, babu yanda za a haɗa zaman ƙauye da na birn..." Sallamar Malam ce tasa ya tsuke bakinshi  yana gallawa tsohuwar harara.

"Yauwa Ɗannan gwara da Allah ya kawo ka, Aradu ba zan iya zama da yunwa ba. Tunda na fuskanci kai ma ɗan birnin billahil-lazi ne. Yo me za a yi da birni ba kuɗi, aljihu a bushe ba ko ƙarfanfana. Ai ni gobe sai kwanan Turakawa, don..." hangame baki ta yi ganin ƙaton kwandon kaba a hannunsa.

Fuskarshi a washe yace "Baba Bawan Allan nan da suka tare ne a ƙarshen layi, ya fito da shi yana neman Almajirai. Da ƙyar na iya karɓowa saboda kunya, na ƙi jinin roƙo a rayuwata."
"Ka ƙi jinin roƙo ko kuma ka ɗau girman kai ka ɗorawa kanka. In za a ji kunyar komai, to banda batun ciki, don da ruwan ciki a ke jan na rijiya. Ka ga buɗe min wannan kwanon mai zubin sunduƙi, ƙamshi ya cikan ciki yawu na neman fara tsartuwa."

Murmushi Malam ya yi ya dubi Salaha da ke gefe ɗaya, ta ɗaure cocilan a goshinta tana ta ɗinkin hularta yace "salaha zo ki gwada buɗewa Baba filas ɗinnan, kar ya karye. " Tsam ta miƙe ta tsugunnah a gaban filas ɗin, ta danna mabuɗin da ke saman murfin sannan ta cire, ta ƙara buɗe na miyar ta ajje a gefe." Duk da yanda take jin yunwa gefe ta koma ta takure, don ganin haɗaɗɗen abincin da ke maƙare a cikin filas ɗin, ya taso mata da yunwa cikinta har ƙugi yake.

Hasken wutar da a ka kawo ne ya gauraye ɗakin, tuni Isuhulle ya ƙara fiddo ido ganin didimar da take gaban Baba. Yana ƙoƙarin matsawa, Baba tace "To ƙanin kura uban kwaɗayi, dangin alasawa. Kai dai da a Maye a ka haifeka da an shiga uku. Dubi yanda maƙogaronka yake sama da ƙasa, saboda tsabar kwaɗayi.

Zuwa lokacin Isuhulle ya cika ya yi dam da takaici, don dai yana jin masifar yunwa ne da ko ɗawisu Baba ke ci ba zai kalleta ba. Amma haka ya daure har ta karkasa abincin ta bawa kowa. Ajiyar zuciya Malam ya sauke, ya nufi ƙofa zuciyarshi fal da farin cikin rufuwar asirinshi.

"Kai Tsalha dawo ka ci abinci, da ruwan ciki a ke jan na rijiya, kuma ai ba a da'awa sai da dawa. Banda lalacewar mutanen birni ai kana Limami kamata ya yi su dinga tara maka abinci har sai ka ture." Gefe guda ya zauna, Baba ta tura masa ragowar abincin ya zauna ya fara ci a hankali.

Baba da ke sakace ce ta yunƙura tace "Kai Tsalha Allah ya sakawa waɗannan baƙi da alkhairi da ba su zo ba. Wato na daɗe ban ci abinci mai daɗin wannan ba, da ba don kar na yi ƙarya ba da na ce ban taɓa ci ba ma." Dariya su Isuhulle da ke gefe suka saka, suna zolayar Baba.

_________________________

   Tun da ya koma ya ga tana wani shan ƙamshi, a kusa da ita ya zauna yace "Amarsu me ya faru ne a ke fushi da ni?"
"Babu abinda ya faru, kawai gajiya ce." Murmushi ya yi yace "To ko na miki tausa?" Kafin ta bashi amsa ya fara mammatsa mata jikinta. Janye jikinta ta yi tace "Barshi na gode, nasan ƙarshe cewa za ka yi a yi ladan gabe." Girgiza kanshi kawai ya yi, yace "Gobe idan Allah ya kaimu da wuri zan fita, sai ki tashi ki haɗa abin kari da wuri." "To" ta amsa ta yi cikin ɗaki ta kwanta, sai da ya kammala duk abinda zai yi sannan ya bi bayanta.

  Washegari da ya tashi ƙarfe bakwai ya yi mamakin ganinta a madafa tana feraye dankali, ya so ya karɓeta amma sai ya janye hannunshi yace "Sannu da aiki."
"Yauwa" ta amsa tana mita ƙasa-ƙasa filas ya ɗauka ya juye ruwan zafi a botiki ya nufi banɗaki.

Har ya gama kimtsawa ba ta gama soya dankalin ba, agogonshi ya duba bai gani ba, sai ya hau bubbuɗa lokokin da ke jikin mudubin. kwalin magani ya gani, har ya rufe ya ƙara buɗewa ya ɗau kwalin maganin. Jikinsa rawa ya fara yi bayan ya karanta maganin mene ne. Da ƙarfi ya ƙwalla mata kira "Halima!" A guje ta ƙaraso, don kiran bai yi kama da na lafiya ba. Maganin ya watsa mata yace "Wannan na meye? Haleema ashe har ƙin da ki ke yi mini ya kai haka?"

Girgiza kai kawai take, da ƙyar ta iya cewa "Don Allah ka yi haƙuri ni fa duk abinda na yi..." Tsawar da ya daka mata ce tasa ta rufe bakinta gum, cike da tsoron abinda ka je ya zo.

   Su Hindu kuwa tuni sun koma India, zamansu suke cikin jin daɗi da walwala. Sosai ta dage take kula da Mijinta da ƴaƴanta abin sai son barka.

Hadiza kuwa abun duniya duk ya bi ya isheta, babu abinda ta fi so irin ta ji ta kusa da Baban Mama, amma sai gashi ya gujeta. Kayanta ta tattare ta koma gidansu da zama.

Duk yanda Babanta ya so hanata, ƙi ta yi fur, shi ma ganin ba ta da cikakkiyar lafiya yasa ya ƙyaleta.

KU YI MALEJI DA WANNAN PLEASE

ALLAH YA GAFARTAWA IYAYENMU

MUM AMNASH🖊️

SO KO WAHALAHikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin