SO KO WAHALA? PAGE 43

32 4 8
                                    

*HAƊAKA WRITER'S ASSO...🖊️*

*❤️😭SO KO WAHALA?😭❤️*

                    NA

MARYAM MUHAMMAD SANI (Mum Amnash)
*Wattpad @mumamnas2486*

24/Al-Muharram/1443 - 2/9/2021

          4️⃣3️⃣

Da ƙyar ya miƙe suka nufi gidansu Khamis, kai tsaye ya shiga banɗaki sai da ya ɓata musu lokaci sannan ya yi wanka ya shirya.

Suna ƙoƙarin fitowa Musbahu ya shigo hannunshi riƙe da ledoji,  biyu yace "Ga kazar Amarya sai ku hanzarta dare fa na ƙara yi." Ko kallonshi Isah bai yi ba, ya nufi gidansu kai tsaye.

    Har cikin ɗakin Mama ya shiga ya tsugunnah a gabanta, ya buɗe baki zai yi magana, sai hawaye shar-shar. Hannunta ta ɗora a kanshi tace "Allah ya albarkace ka tare da iyalinka, Allah ya baka zuri'a ɗayyaba. Yanda ka yi mini biyayya, Allah yasa ƴaƴanka su yi maka sama da biyayyar da ka yi mini."

Hanneyenshi ta kama ta damƙe tace "Isa don Allah ka so Haleema, ka ƙaunace ta. Isa..." kasa ƙarasawa ta yi hawaye na zuba a fuskarta.

Aunty na shigowa tace "Wai haryanzu baku tafi ba? Dare na ƙarayi Shaɗaya ta wuce sosai, gwara ku yunƙura."

Jiki a sanyaye Khamis ya matsa don ya miƙar da shi, amma sai ya rungume Mama tsam yana kuka "Mama, Mama" kawai ya ke furtawa, shafa bayanshi ta fara yi a hankali tausayinshi yana ƙara ratsata. Haƙiƙa duk cikin ƴaƴanta tafi son Isa, saboda a koda yaushe suna tare tunawa da abinda ya fi jin kunya tayi, murmushi tayi ta matsar da bakinta kusa da kunnenshi tace "Haba Aunta, ka girma fa ka daina kuka ka ji, nan da wata shekarar ka zama Baba kai ma ka samar mini da Jikoki mafi..." Kafin ta ƙarasa ya miƙe, kanshi a ƙasa ya bi ta gefensu Khamis suka fita. Kai tsaye Musbahu ya shiga mazaunin Direba, Isa da Khamis kuma suka zauna a baya.

  Leema kuwa bata wani ɓata lokaci ba tayi wankanta, tasa Atamfarta mai kyau riga da zani ta ɗaura ɗankwalinta sannan ta feshe jikinta da turarurruka kala-kala masu matuƙar ƙamshi.

Sai da Zahra ta ƙwanƙwasa ƙofar sannan ta murɗa, a bakin gado ta tarar da ita ta ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya.

Ƙarasawa ciki tayi ta zauna, tace "Leema ga saƙonki daga wurin Aunty Salama, tace duk da takarda a ciki, abinda baki gane ba sai ku yi waya."

Wani shegen tsaki ta ja tace "To ni amfanin me za su yi mini? Waɗanda na ɗibga ma da kinsan bala'in da suka sakani da kin tausaya mini."

Murmushi Zahra ta yi ta kama hannunta tace "Haba Haleema, idan ki ka yi wani abun kamar baki da ilimi. Dama baki karɓi wannan auren a matsayin ƙaddararki ba? To ni dai bani da abin faɗa miki, illa ki farga ki tuna taimakon da Allah ya yi miki ya tsamo ki daga kududdufin matsaloli, ya azurtaki da santalelen Miji matashi mai jini a jika. Ra'ayin ki ne ki yi abinda ya dace ko kiyi akasin haka. Maganar magunguna da ki ke yi, a lokacinda na dinga hanaki amfani da su ai baki saurareni ba, idanunki sun rufe da son farantawa Namiji. Ni barka na yi miki, tunda har aka yi miki gatan da aka ɗaura miki aure da ɗan uwanki..." Turo ƙofa Baba ta yi tace "Ku yi sauri ku fito Zahra sun ƙaraso fa" Da sauri suka fita falon suka zauna, su Baba kuwa tuni suka yi waje suka shiga motar Musbahu.

A tsakiya suka saka Angon, da sallama suka shiga ɗakin, Zahra ce ta amsa musu sannan suka shiga.

Musbahu ne ya ja musu doguwar Addu'a, suna amsawa da Ameen har ya kammala sannan ya dube su yace "To dukkan godiya da yabo sun tabbata ga Allah, Isah, Haleema ina tunasar da ku yin imani da Ƙaddara yana daga cikin cikar imani. Aure rayuwa ce mai cike da komai farinciki, walwala, soyayya , a wasu lokutan har da damuwa da baƙin ciki. Shawarata a gareku ku yi ƙoƙari farin cikin da ke cikin aurenku ya rinjaye kishiyarsa, sai ku lulluɓe sauran damuwarku da haƙuri. Haƙurin dai shi Iyayenmu a kullum suke jaddada mana, don kusan shi ne ya ke kusa da ruhin aure. Bazan ja da yawa ba Isa Allah ya albarkaci Aurenku, Allah ya bada zuri'a ɗayyi ba. Khamis tashi mu tafi, Shabiyu ta kusa mun bar tsohuwa a mota.

Jiki a sanyaye Isa ya bi bayansu, lokacin tuni Khamis ya fice, sai kuma ya dawo  riƙe da ledojin Amarya ya miƙawa Isah, karɓa ya yi kanshi a ƙasa.

SO KO WAHALATempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang