SO KO WAHALA ? PART 5

43 5 0
                                    

*HAƊAKA WRITER'S ASSOCIATION*

*❤️😭SO KO WAHALA?😭❤️*

            NA

MARYAM MUHAMMAD SANI(Mum Amnash)
WATTPAD@mumamnas2486

       ▶️5️⃣

12/Shauwal/1442-24/5/2021

        Kamar yanda Baban Mama ya faɗa, ƙarfe shaɗaya na safe a ƙofar gidansu Anti ta masa. Cike da tsabar mamaki Leema ta fito, ta ce "Wai dama da gaske ka ke?" Murmushi kawai ya yi yace "Ga zahiri kin gani. "  Jikinta a sanyaye tace "To mu ƙarasa ciki." Ya bi bayanta ,a harabar gidan suka zauna akan wani dogon benci.

  Cikin jin nauyi ta gaisheshi, ya amsa mata fuskarshi a washe. Jikinta ne ya ba ta kallonta ya ke, ta katse shirun da tambayarshi "Ya Maman Mama da Mama?"
"Duk su na nan ƙalau, amman ba sa gari wata ƙila nan da wata ɗaya za su dawo. Ta je ganin gida ne. So ta na iya yin wata biyu zuwa uku in ta je, in ta dawo zan faɗa mata."

Cikin sanyin murya ta ce "To Allah ya dawo da su lafiya" "Ameen" ya amsa a taƙaice . Gyaran murya ya yi yace "Haleema a gaskiya , tun jiya da na ganki na ji a zuciyata jinina ya haɗu da na ki. Don haka ina ganin ya kamata kisan wane ne ni , ni ma nasan wace ce ke ko da a taƙaice ne. Da farko dai suna na....."

Fitowar Isa ce ta katse shi , rasss gaban Leema ya faɗi . Ko kallonta bai yi ba, kai tsaye ya wuce wurin Baban Mama ya miƙa masa hannu su ka yi musabaha,su ka gaisa sannan ya fice.
Da kallo Baban Mama ya bishi ya ce "Haleema ya sunan wannan ɗan uwan na ki ne?" Sai da ta yi murmushin da bai kai  zuci ba sannan ta ce "Sunan shi Isah, ƴan mata zar mu ke da shi."
Dariya Baban Mama ya yi ya ce "To ko da shi za'a yi ne?" "Wa wai Isah, caɓɗijam rabu da wannan mashiriricin wa ya ke biye ta tashi." "Duk abinda ta faɗa a kunnen isa ,amman sai ya yi biris kamar bai ji ba ya shige gida da biredinsa a hannu. Don kafin ya fito sai da mama ta roƙeshi kar ya kuskura ya yarfa Leema,shi yasa ko kallonta bai yi ba.

   Miƙewa Baban Mama ya yi yace "Kinga an turomin saƙo a na nemana yanzu, bari na wuce . Yaushe za ki koma ne? " "Gobe" ta bashi amsa a taƙaice ta na mamakin yanda aka yi ya san ba anan ta ke ba. "Muttaƙa" ta furta a fili ba tare da tasan ta faɗa ba.
"Kar kiga laifin muttaƙa ni na matsa masa ya faɗa min ke ƴar Kaduna ce ,ba Kano ba. Na so a ce sai kamar jibi za ki tafi don muɗan ƙara fahimtar juna don a zahiri ina son mu ƙulla ƙawance, mu ƙullah kasuwanci. Leema ba ƙawance kawai ba ina jin a zuciyata kamar zan iya bayyana miki damuwar da ta yi wa zuciyata yawa. Kuma bazan iya tattaunata da wani ɗan uwana ba saboda wa su dalilai . Da yau zanje wurin budurwata Hadiza zance , to amma saboda ke insha Allah bayan sallar maghriba zan zo mu tattauna."

Kasa magana Leema ta yi sai kallon mamaki da ta ke binsa da shi. Murmushin da ya zama ɗabi'arshi ya yi ya ce "Na san kina mamaki ne yanda ,daga haɗuwarmu jiya yau na saki jiki da ke ko? Ba wani abun mamaki ba ne ,haka ɗabi'ata ta ke .Ina da saurin sabo sai dai ba ni da saurin yarda .Amma ke, daga jiya zuwa yau, na ji na  gama yarda da ke . Sai anjima ki kula."

  Baban Mama na ƙoƙarin fita su ka yi karo da Haseen , haƙuri ya bawa Haseen ya fice da sauri . Da azama Haseen ya ƙaraso gabanta ya tsaya ,fuskarnan kamar hadarin tsakiyar damuna .

Raf raf raf ya tafa mata har sau uku sannan ya dubi tsakiyar idonta ya ce  " Sadiya ko a ce Leema, rayuwarki ta na ba ni mamaki , sau tari ansha faɗa min cewar babu aure a tsarinki ,amman wahalalliyar zuciyata sai ta ƙaryata hakan. A da mu uku mu ke takara a kanki ni, Dr salis sai Alhaji Labaran  to amma ga na huɗu ya tunkaro mu."

Cikin mutuwar jiki ta ce "Haseen ka kwantar da hankalinka, wannan mutumin da ka gani business za mu ƙulla da shi ,shi ya sa ka ga ya zo da safen nan. Ka yi tunani mana,idan wurina zai zo ai sai dai ya zo da daddare ko kuwa? Yanzunma ba mu gama tattaunawa ba aka kirashi a waya ya tafi. Ya ce min da daddare zai dawo ,ina son ka dawo da daddaren zan gabatar da kai a wurinshi."

Duk da Haseen ya ji daɗin bayaninta, amma sai bai nuna mata ba, ficewarshi ya yi ko sallama bai mata ba. Jagwaɓ ta koma ta zauna a kan bencin ta lula duniyar tunani. Gefenta Isa ya zauna , ɗan tausayinta ya ji ,amma sai ya maze ya ce "Sadiya" figigit ta yi sannan ta ce "Lafiya ko ka zo kamin halin na ka ne?"
Girgiza kanshi ya yi ya ce "Kin san baki da wani abokin shawara da ya fini ko? To ina son ki saurareni Haleema. Dama sau ɗaya ta ke zuwar wa mutum a rayuwa, amma da ya ke kina da sa'a ta zo miki har ba bu adadi kina wasa da ita. Ki duba irin son da Alhaji Yakub ya nuna miki, amman a ƙarshe ki ka daƙileshi ,ki ka ce ba za ki je gidanshi a ta uku ba. Bayan kin ɓata masa lokaci. Allah ya gani Haleema ,tun daga lokacin na raina wayonki , duk da nasan komai sai Allah ya nufa. Ba zan gaji da faɗa miki gaskiya ba lokaci ya na ƙure miki ya kamata ki yi amfani da shi kafin rayuwa ta......" Kukan da ya ga ta soma ne ya kastse shi, girgiza kai kawai ya yi kukanta na shiga har cikin zuciyarshi.

  "Isah ba kai kaɗai ba da yawa daga cikin mutane da dangi da ƴan uwa, duk su na zargi na da ƙin yin aure. Wanda a zahiri hakan ne, amma a baɗini ba haka ba ne. A ra'ayina ba zan auri namijin da ra'ayinmu ya banbanta ba. Ba don komai ba sai don ba na son na yi aure na fito ,ko na auri mijin da zan sha wahala a hannunsa . Bari na ba ka misali , kaga Alhaji labaran mutum ne har mutum,amma kuma ya na  sa ido a kan kuɗaɗen da su ke hannuna. Da bakinshi ya ke cemin wai idan mu ka yi Aure, sai mu dinga haɗa kuɗi muna kasuwanci. Dr Salis kuwa matarshi ke juyashi ga ta da masifar tsiya. Kaima kasan hakan tuntuni, sai ɗan wahalarka Haseen shi kuma ya kai a aureshi sai dai zuciyar Haseen ta yi yawa. Gashi idan ya yi fushi ba ya  bincike , a cikin fushi ya ke yanke hukunci . A soyayyarmu da Haseen mun rabu da juna har kusan sau goma a shekara biyu, sai daga baya sannan ya ƙara dawowa. Ka ga zama da shi zai yi wuya. To a shawarce a ganinka wa zan zaɓa?"

"Humm to ai da wuya ki sami abinda ki ke so ɗari bisa ɗari, sai dai ki zaɓi wanda ya fi kwanciya a zuciyarki . Ko kema kya huta da wahala, gararanba ba Aure ai ba daɗi abin wallahi. Au to shi kuma na ɗazu da safe fa?"
  Sai da ta yamutsa fuskarta sannan ta ce "Wai so ya ke mu zama abokai." Dariya Isah ya yi ya ce  "To sai ki faɗa masa a bahaushiyar al'ada da kuma addininmu babu abota tsakanin mace da namiji . Kai har rana ta fara taraddamu, tashi mu shige gida."

   A tare kuwa su ka miƙe suka yi ciki.

******************

    Da daddare kuwa Haseen da wuri ya iso wurin Leema ,bai daɗe da isowa ba Baban Mama ma ya ƙaraso . Kallon-kallo su ka fara yi , kafin daga bisani Baban Mama ya miƙa masa hannu.........

ALLAH YA GAFARTAWA IYAYENMU

Mum Amnash🖊️

SO KO WAHALAWhere stories live. Discover now