SO KO WAHALA? PART 24

36 2 0
                                    

*HAƊAKA WRITER'S ASSOCIATION*

*❤️😭SO KO WAHALA?😭❤️*

           NA

MARYAM MUHAMMAD SANI(Mum Amnash)
WATTPAD@mumamnas2486
BLOGSPOT@mumamnash.blogspot.com
*Wattsapp link* https://chat.whatsapp.com/Gty1kpVjvrb2myAy87gOou

25/Zulƙada/1442 - 4/7/2021

     2️⃣4️⃣

Ranar haka ta yini tana buga wayarshi, tana shiga amma mirsisi ya ƙi ɗagawa daga ƙarshema sai ta daina shiga ko ta kira.

  Zuwa la'asar ta gama yin laushi, don ɗaukan wani maƙocinsu ne, kuma ɗan tasha ne, a ƙallah a yau kawai ya kirata ya kai sau goma. Da tayi yunƙurin bashi uzuri zai zaraf yace bai san wannan ba, kuma bazai karɓi kuɗi da giɓi ba.

  Yinin ranar haka ta yini ba rini ba matsa sai tunani da ya cushe mata ƙwaƙwalwa.

  Sauƙinta ɗaya Aunty bata nan ta je gidansu Maleeka, da sai ta isheta da tambaya.

  Tun kafin Aunty ta dawo Mama ke tambayarta, amma amsar ɗaya ce ba komai.  Da Aunty taga haka sai tace "Kar wanda ya ƙara tambayarta idan ta yi wari maji, duk da bansan me ya ke damunta ba nasan tabbas yana da alaƙa da Baban Mama. Gwara ku zuba mata na mujiya ku ƙyaleta."
Duk wannan maganar da Aunty take a gaban Leema take yi, hakan yasa ta fara zubar da ƙwalla, gaba ɗaya suka fashe suka barta ita kaɗai a tsakar gidan kamar mayya.

  Washegari Litinin  da wuri ta nufi tasha ta ɗau hanyar Zariya, kai tsaye Asibiti ta nufa. Ko gaisawa basu gama yi da abokan aikinta ba, kiran waya ya shigo wayarta. Gabanta ya yanke ya faɗi, zaro wayar tayi ganin Babarsu ce yasa ta ɗaga da sauri, ko gaisuwarta bata amsa ba tace "Haleema wai kina Kano ne? To ko a ina kike ki taho gida a yau, don yanzun nan Ghali yabar gidannan, yana ta zazzagar garari wai zaki cinye masa kuɗin adashin Uban gidansa. Haleema don Allah ki taimaka ki bawa Ghali kuɗinshi, nasan kinfi kowa sanin waye Ghali, sai kin dawo Allah ya rufa asiri." "Ameen" Leema ta amsa ta mayar da wayar jaka ta rufe.

Ana tashi daga aiki ta hau mota ta wuce Kaduna, tana isa a ƙofar gidansu ta hango Ghali a zaune ƙafa ɗaya kan ɗaya. Sai da fitsari ya kusan ƙwace mata, amma sai ta dake.

Shiko Ghali yana hangota ya fara washe baki, don ya ɗauka tafe take da kuɗinshi.

A soron gidan ta tsaya, Ghali ya ƙaraso suka gaisa kamar abin kirki, hannu ya zura cikin aljihunshi ya ɗauko kuɗi dubu Ashirin da biyar ya miƙa mata yace "Ga karan adashinki nan, don bana son ko naira biyar tayi giɓi a kuɗinnan, cif-cif nake son na turawa Alhaji." Ganin bata karɓa ba yasa ya zaro baƙin glass ɗinshi ya toshe idonshi yace "Na gane abinda kike nufi yanzu, wato dai ba kuɗina ba labarinsu ko? To wallahi ki kuka da kanki duk abinda ya biyo baya kar kice ban duba haƙƙin maƙotaka ba. Kin ci albakacin ina ɗan sonki kaɗan, don haka na baki nan da kwana uku ki turo min kuɗina, idan ba haka ba hahahaha! Ba zan faɗi me zanyi ba sai dai ki gani a aikace."

Ya fice fuskarsa kirtif kamar an aiko masa da manzon mutuwa, bayansa tabi da kallo har ya ɓacewa ganinta. Muƙut ta haɗiyi wani yawu mai ɗaci sannan ta wuce cikin gida.

************

     Baban Mama kuwa hankalinsa kwance ya ke kamar tsimma a randa, don duk inda ake son mace ta kai to Hadiza ta wuce a wurinshi. Shi yasa ko fita baya iya yi, ko baƙi akayi sai dai ya shige bedroom ya zauna. Duk baƙo mai hankali sai ya tattare ƴan silifatunshi (takalma) ya tafi ko mutum ya yi gidan Hajiya da yake duk a layinne tazarar ba yawa.

Ko Hindu bata fiye ganinshi ba, da safe ne kawai yake leƙota su gaisa ya kai Mama Makaranta, daga nan bata ƙara ganinsa sai gari ya ƙara wayewa. Sai taci sa'a zai leƙo ya mata sai da safe.

  Hindu kuwa kacokan ta mayar da hankalinta kan ibadarta, da kula da kanta da gidanta. Idan taji damuwa na neman sakota a gaba sai tayi nafilarta ko raka'a biyu ce , idan kuma tana jin nishaɗi sai ta hau yanar gizo ta sha karatun ƙagaggun labarai sannan ta sauka.

   Baban Mama ko da wasa bai yi niyyar cinyewa Leema kuɗi ba, sai dai yana niyyar tura mata Inno ta aiko su Jamila su tuna masa a satin za su koma makarantarsu, da yake bodin suke yi.Dole ya fasa tura mata ya basu dubu hamsin ɗin su yi siyayya, ga siyayyar ƴan bodin da yawa, haka suka karɓa suka kaiwa Inno kuɗin. Da  murna ta karɓe washegari suka je kasuwa ta siya musu komai.

    Duk kiran da Leema take yi masa yana gani, kunya ce tasa ya kasa ɗagawa don bai san mai zai ce mata ba. Hadiza kuwa da taga ta damesu da kira, sai ta sa lambar Leema a jerin baƙaƙen lambobi (Black list) shi yasa ko ta kira bata shigowa. A tunanin Baban Mama ya ɗauka Leema ta nemi rance ta cika, shi yasa ya basar kawai, so yake da ya samu kuɗi ya tura mata.

****************

  Dole ƙanwar naƙi abinda Leema bata so dai shi ya faru, da shawarar Babarsu ta ɗauki dubu ɗari a kuɗaɗen ajiya na mutane da ke hannunta ta cika ta  haɗawa Ghali kuɗinshi. Don barazanar da ya ke mata ta isheta, duk da baya ce mata komai amma kullum yana zaune a ƙofar gidansu, wani lokacinma a kusa da Babanta.

  Da ido yake mata alama ko ta bashi kuɗinshi ko ya faɗawa Babanta, shi yasa har ƴar rama tayi sai hanci zirit kamar anja eriya.

Tana kiran Gali kan ya zo ya karɓi kuɗinshi ya yi zaraf ya faɗa soron gidan, yace "Ki fito ina zaure" Da sauri ta zari hijab ɗinta ta yaɓa ta zuba kuɗin  a leda ta nufi soron gidan, ba ta ɓata lokaci ba ta miƙa masa kuɗin. Da sauri ya karɓa, har ta juya yace "Dawo dawo da sauran aiki, ai bazaki tafi ban ƙirga ba, don gudun samun matsala. Don kema naga son kuɗin tsiya gareki kamar tirejara akawunt na Najeriya, yauwa gara ayi filla filla yanda kowa zai fahimta, miraran-miraran."

  Cikin takaici tace "Kaga Ghali ba komai ka tafi da kuɗin gida ka ƙirga, ai akwai karan adashi na a wurinka, to ka barshi idan ka tabbatar da cikar kuɗin sai ka bani." Ba ta jira cewarsa ba tayi shigewarta cikin gida, Ghali kuwa dariya ya yi yace "Yaro man kaza, yo banda abin Halidubu me ye abin fushi, itafa Naira ba ruwanta da sabo ko wata alaƙa yanzu da ta gifta kaji jidali ya tashi." Haka ya wuce ya na sambatu, har ya faɗa gidansu.

**************

Washegari Juma'a da wuri Leema ta shirya ta zuba kayanta seti uku a jakar goyo, don Kano za ta wuce kai tsaye don tana sa ran shigowar wasu kuɗi za tayi sari.

   Tun tana mota take ƙara gwada kiran wayar Baban Mama, amma har yanzu bata shiga ba. Ƙudurcewa ta yi a ranta ita dai da kanta ba za ta nemeshi ba, idan ya nemeta shi kenan.

   Tana ƙarasawa wanka ta yi tayi sallah ta sa kaya marasa nauyi sannan ta je ɗakin Aunty, anan suka dasa hira. Ƙarar wayar ta ce ta katse su ta ɗaga da sallama "Assalamu Alaikum" "Wa'alaikumussalam Haleema da fatan kin yini lafiya, don Allah kuɗaɗennan da na baki ajiya nake so ki turo mini yanzu. Kinga za'a yiwa Zubaida ofareshan (CS) yauwa ki taimaka don Allah."

A take kanta ya fara juya mata hawaye suka ɓalle kamar an buɗe famfo, don ta ta cikin kiɗima Aunty tace "Ke wai lafiya ko mutuwa aka yi ne?" Girgiza kai kawai take, sai da Aunty ta mata wuƙa-wuƙa sannan ta kwashe komai ta faɗa mata.

Dariya Aunty ta yi sosai tace "Ai na daɗe da sanin wannan labarin, amma ban miki magana ba don ina son namiji ya fara nuna miki kaɗan daga cikin shika-shikan rashin mutuncinsu. Banda ke dabba ce ya za'ayi a wannan marrar ki ɗauki kuɗi kusan miliyan ɗaya ki bawa mutum, da duka kuɗinki ne ma da sauƙi, amma har da sashi a adashi, da yake ke ƴar iska ce ƴar kanki baki da mafaɗi. Yanzu me kike son na miki? Ni ba shashasha ba ce irinki da zan nemo miki rancen kuɗi ki zo ki barni a ciki ko ki barni da jin kunya. Ba ke shashasha ba, kina tunanin kuɗi suna sawa a so mutum soyayyar gaskiya? Sai dai a yaudari mutum, kuma ita aka yi miki yanzun. Ke a tunaninki wannan mutumin yana sonki? Ko ɗaya baya sonki kuma ba aurar ki zai yi ba tunda gashi yayi amfani da ke wajen cikar muradinshi. Kinga yanzu kin zama bola, shegiya daƙiƙiya tashi kisa kayanki mu tafi gidan uwarshi don ya fito miki da kuɗinki." Dama Aunty idan ranta ya ɓaci tofa sai dai mutum yayi haƙuri da duk abinda za ta furta don ba sauƙi.

  Jiki ba ƙwari Leema ta miƙe ta kimtsa suka hau adaidaiya sahu suka nufi gidansu Baban Mama...

ALLAH YA GAFARTAWA IYAYENMU

MUM AMNASH🖊️

SO KO WAHALAKde žijí příběhy. Začni objevovat