SO KO WAHALA? PART 20

35 1 2
                                    

*HAƊAKA WRITER'S ASSOCIATION*

*❤️😭SO KO WAHALA?😭❤️*

           NA

MARYAM MUHAMMAD SANI(Mum Amnash)
WATTPAD@mumamnas2486
BLOGSPOT@mumamnash.blogspot.com

17/Zilƙida/1442 - 26/6/2021

      2️⃣0️⃣

  Hannunsa ya ɗora a bakin ya dangwalo, ganin jini ya sa ya danƙaro wata ashar ya ce "Daga yau Yunus ba ni ba kai, ba ni ba Haleema, Allah na tuba banda sheɗan da yayi wasa da zuciyata ma mai zanyi da haleema, aba a bushe kamar muciya ga munin tsiya, Allah wadaran naka ya lalace wai raƙumin dawa ya ga na gida. Ina son ka sa a ranka daga yau ba ni ba kai, kar ka sake tuna kama san wani mutum mai suna Zayyad Ibrahim, na barka lafiya angon tsamurarriya."

Har ya kai bakin ƙofa ya dawo ya ce "Kar ka manta Yunus duk wani sirrinka ya na tafin hannuna, kuma dalilin da yasa na zargeka su na da yawa. Za ka iya tuno ranar da kazo ofis ɗinnan bayan ka baro wurin Leema, har na zuba maka yogot a jikinka da yamma?"Jin Baban Mama ba shi da niyyar tanka masa, sai ya ɗora ya ce "Shatin janbaki na gani raɗau a kafaɗarka, gudun samun matsala da iyalinka ko wasu su yi maka kallon mutumin banza shi yasa na watsa maka yogot a rigarka. Amma tunda har kana ganin zarginka da na yi laifi ne to ba komai, ai Ƴarka ta fari mace ce, ka jira ta girma ta fara zance, in da rai zan ga me za ka yi a lokacinda wani saurayi ya sata a mota ya... Tas! Baban Mama ya kwashe Zayyad da mari a fusace ya ce "Duk rigima da jidalin da za mu yi ya kasance tsakanin ni da kai ne kawai, kar ka ƙara saka iyalina a wannan sabgar. Da yardar Allah ƴata ba za ta taɓayin wani abu na assha ba, don ba irin tarbiyyar da zan bata ba kenan. Kaima ina nema maka fatan shiriya. A da na ɗauka ka daina halin bunsuran, ashe har yanzu kana kanyi, Allah ya shiryeka."

  Wata dariya Dr Zayyad ya yi sannan ya ce "Ameen Allah ya shirye mu baki ɗaya, kasan bunsuran da yawa, tunda kaima da kake sa Leema a lungun motarka AC na firfitaku ai ba dala'ilu ka ke biya mata ba."
Kasa magana Baban Mama ya yi don takaici, sai cizon yatsa da ya ke.

Dr Zayyad kuwa kai tsaye ya fice daga ofis ɗin ba tare da ko bakinsa ya wanke ba, zuciyarsa tas don ko ba komai ya ƙunsawa Yunus takaicin da zai daɗe yana cin ranshi.

Baban Mama kuwa baki ya buɗe tsabar mamaki, kasa magana ya yi, wai yau shi Zayyad ya ke farfaɗawa magana haka son ranshi. "Allah ya kyauta" ya furta a fili, da sauri ya fita daga ofis ɗin shima ya nufi motarshi, yana ɗora hannunshi akan sitiyarin ya fashe da kuka. Tuno kalaman Zayyad ya ke, a take wata nadama da danasani suka lilliɓeshi. A gefe guda kuma haushin Leema ya ke ji, don da ta riƙe mutuncinta da taya zai soma ɗora hannunshi a kanta. Allah maɗaukakin sarki ya yi gaskiya da yace "Kar ku kusanci zina" yau ga abinda soyayyar shan minti ta jawo masa. A fili ya fara istigfari "Astaghfirullah" ya tada motarshi ya wuce yana fatan kar Allah ya bawa wani namiji ikon cutar masa da ƴa, koda da furta mata mummunar kalma ce, balle ta kai ga ɗora hannu a kanta.

   ****************
   
   A cikin sati guda Leema ta kammala haɗa lefen Hadiza, sai Akwati da ya rage za su saya. Ta kikkira Baban Mama amma bai ɗaga ba, hakan ya sa ta masa video na sayayyar ta tura masa ta wattsapp. Aiko washegari sai gashi da wuri ya zo ya jidi kaya ya nufi gidansu da shi, a ranar ya siyo akwatuna suka harhaɗa, bayan kwana biyu su ka miƙa kayan gidansu Hadiza.

Tunda aka kai wannan lefe fa su Hadiza aka fara gwalangwaso da kwarkwasa, duk wanda ya zo gani da kanta ta ke buɗe masa, don akwai ɓarayin hoda masu ɗiban kayan amarya.

  Gaba ɗaya unguwar surutu su ke, wasu ma kasa daurewa suke su je har gida su sami Hindu da zancen. Amma iyyaka tace musu "To me ku ke so ayi yanzu? Na hanashi auren ko me? Duk ɗan Adam baya wuce ƙaddararshi, idan ƙarin auren na daga cikin ƙaddarar mijina, to taya zan hanashi. Don Allah ku bimu da addu'a kawai. A take sai jikin mutum ya yi sanyi ya ɗauki takalmanshi ya fice, da wannan ta kashe bakin ƴan gulma.

Su ma kansu su Hadizan sunyi shaguɓen har sun gaji, ganin ba zata kula su ba yasa suka mayar da hankali kan shirye-shiryen bikinsu.

  Sai da aka yi sati da kai Lefen Hadiza sannan Leema ta shigo Kano, don ƙorafi ya yi yawa a kanta a gun aikinsu, duk da ƙawayenta na aiki a madadinta wasu lokutan.     Idan aikin safe za ta yi tana iya zuwa Zariya ta kwana, da ta tashi daga gurin aiki ta hau mota ta nufo Kano.

   Abinci ta ci kawai ta yi wanka ta shirya, ta na ƙoƙarin fita Dr Zayyad ya cuso kai. Kujera ta ɗauko ta kawo masa ya zauna sannan su ka gaisa. Kai tsaye ya ce "Haleema mun ɗan sami saɓani da mutuminki fa, amma ya wuce na dai zo na sanar da ke ne don kar ki ƙara tuntuɓata kan sabgar da ta shafeshi" za ta fara bashi haƙuri ya ɗaga mata hannu ya ce "Kiyi haƙuri ba wannan ya kawo ni ba, Allah ya sada fuskokinmu da alkhairi"

   Ya na sa kai su ka yi karo da Maleeka, ta yi taga taga kamar za ta faɗi, cikin azama ya kamata ya miƙar da ita. Faɗan Aunty ne ya sa ya cikata "Ai ni bansan ke wace irin yarinya ba ce Maleeka, son jiki kamar mage, zaman Abuja ya lalataki, za ki ci ƙaniyarki ne." Tura baki ta yi gaba don Aunty ta yarfata a gaban wannan gayen, har ƙasa ya russuna ya gaida  Aunty, da fara'a ta amsa don mutuminta ne, Baban Mama ne ya haɗa su. Idan za ta je AKTH ganin likita, shi ya ke mata komai, shi yasa take girmama shi.

Leema kuwa baki ta taɓe irin abun bai dameta ba kai tsaye ta nufi ɗorayi gidansu Baban Mama, sai da ta kusa isa sannan ta sanar da shi. Da yake yana gida lokacin ba shiri ya faɗa mota ya nufi gidan Innon shima, kusan a tare suka isa, don tana shiga ya shigo shima.

Cikin karramawa Leema ta gaida Inno sannan ta gaida Baban Mama, daga nan suka dasa hira tamkar ba surukai ba. Ƙarar wayar Leema ce ta katse hirar ɗauka ta yi da sallama "Assalamu Alaikum" daga ɗaya ɓangaren aka amsa mata "Wa'alaikumussalam don Allah Hajiya Haleema ki yi haƙuri, an gama kayan gadon tuni, masu sekelaton kujerar ne basu gama da wuri ba. Kusan kullum ina jele tsakanin Gandu da Maganda. Amma angama za ki iya zuwa ki ɗauka." "Shikenan ai, amma iyayen amaryar nan sun ji ba daɗi da ƙyar na taushesu, nan gaba ka kiyaye na gode. Yanzu  ba na gida da daddare ka shigo sai mu tattauna, na baka sauran kuɗinka." Sallama su ka yi ta katse kiran tana ƴar mita.

Da fara'a Inno ta dubeta ta ce "Ƴar nan har harkar kayan ɗaki ki ke yi ne?" murmushi Leema ta yi ta ce "Ina ɗan taɓawa, kafinta na ne yanzunma ya kira, an kammala kayan wata amarya, Insha Allah gobe zan tura su Dutse."

  Ƙare yashe baki Inno ta yi ta ce "To ko kafintan na ki zan bawa gyaran gado na? Duk ya kwararraɓe ai da Baba ya na da kuɗi wallahi sake minshi zai yi kafin bikin nan. Duk da tambayar ta yiwa Leema wani iri amman sai ta ce "Ba komai Inno zan tambayar miki shi" Wani irin takaici ne ya lulluɓe Baban Mama da ido ya ke ta yiwa Inno magana ta yi shiru, amma sai ta yi kamar ba ta gani ba...

ALLAH YA GAFARTAWA IYAYENMU

MUM AMNASH🖊️

SO KO WAHALAWhere stories live. Discover now