SO KO WAHALA PART 25

44 3 2
                                    

*HAƊAKA WRITER'S ASSOCIATION*

*❤️😭SO KO WAHALA?😭❤️*

           NA

MARYAM MUHAMMAD SANI(Mum Amnash)
WATTPAD@mumamnas2486
BLOGSPOT@mumamnash.blogspot.com
*Watsapp link* https://chat.whatsapp.com/Gty1kpVjvrb2myAy87gOou

26/Zulƙida/1442 - 5/7/2021

        2️⃣5️⃣

   Tunda suka hau Adaidaita sahun ba wanda yace kanzil, har aka sauke su a bakin titin suka gangara cikin layin. Gaban Leema ba abinda ya ke banda faɗuwa, tsoronta ɗaya kar Aunty ta saki layi a gidansu Yunus.

Aunty ce kaɗai ta iya yin sallama "Assalamu Alaikum" Inno da bata ɗau murya ba ta fito da sauri tana amsawa "Wa'alaikumussalam" Ganin Leema a bayan Aunty yasa Inno ta washe baki ta hau yi musu maraba "Sannunku sannunku, lale marhabin ku shigo daga ciki".

Bin bayanta suka yi, a cikin ɗakinta da yasha sababbin kayan ɗaki ta shimfiɗa musu tabarma, zama suka yi aka gaisa ita kanta Inno ganin Leema ta zo ba ɗan ƙulli yasa ta fara shan jinin jikinta. Amma sai ta maze a zuciyarta tana tunanin ƙila kan auren Baban Mama suka zo mata Allah ya sanya alkhairi...

Tunaninta ne ya katse jin Aunty tace "Da farko dai suna na Zahra wacce aka fi sani da Auntin Kano, da fatan an kammala biki lafiya"

Da fara'a Inno tace  "Lafiya ƙalau wallahi, dama fuskarce ban sani ba amma ai muna da labarinki a wurin Ƴar albarka,  Ango da amarya suna can gidansu lafiya ƙalau."

Wani murmushi Aunty tayi tace "Madallah haka ake so, to Hajiya Inno sallah ta wuce ta bar wawa da bashi, don baya ta haihu"

Cikin in'ina Inno tace "Ƴar nan yi min bayani da yaren da zan gane, ban gane waɗannan maganganun naki ina suka dosa ba, Ƴar albarka wai me ya ke faruwa ne?"

  Kasa magana Leema tayi sai hawaye da take ɗaukewa lokaci lokaci. Miƙewa Inno tayi tace "Bari na bayar a karɓo muku fiyowata"
"A'a barshi don tafiyarmu da yawa, ƙila daga nan muje can gidan Amarya mu sami Yunusan a can. Hajiya Inno dalilin da yasa muka zo nan ƙorafi na kawa akan ɗanki Yunus, Yunusa ya yi kwance-kwance ya saka baiwar Allah nan a tsaka mai wuya.."

Zaraf Inno ta yi tace "Allah sarki Haleema ƴar albarka, wallahi nima banji daɗi ba, naso ace ita Yunus ya fara aura, don yarinyar nan akwai tarbiyya wallahi, ga kyauta abin hannunta bai rufe mata ido ba. Dama nima na so zuwa na baku haƙuri, sannan na yi muku godiya. Wallahi ƴar nan ita ta siya min gadon nan  na zamani, ta taimakeni ta gyaren ɗaki gashi nan gwanin sha'awa. Allah dai ya ida nufi, Allah ya kai damo ga harawa yaci yai birgima iya son..."

"Inno wai Haleeman ce ta saya miki waɗannan kayan ɗakin?" Aunty ta ƙare tana nuna Leema da ke gefenta zaune kamar an tsamota daga ruwa.

Wata ƴar dariya Inno tayi tace "Ƙwarai da gaske, ai kowa ya ji sai ya yi mamaki, kuma ya yaba mata "

Wani irin tafarfasa zuciyar Aunty take amma sai ta yi ta addu'a a zuciyarta har abin ya lafa mata. Tafa hannayenta biyu tayi tace "Babbar magana, wai kallo ya koma sama, yo ni ina zaton wuta a maƙera sai gashi na sameta a masaƙa amma ba damuwa, yanzu taimakon da nake son kiyi min shine ki kiramin Yunusa ki ce masa yazo kina nemanshi, kar kice munzo nafi son ayi komai ga wuri ga waina."

Jiki a sanyaye Inno ta ɗau wayarta ƙirar tekno ta kira lambar Baban Mama.

Ɗan janye Hadiza ya yi daga jikinshi sannan ya ɗaga, ko amsa gaisuwarsa ba tayi ba tace "Yunus ko ina kake kazo gida yanzu" ta kashe ta ajje wayar. A sanyaye ta dubi Aunty tace "Baiwar Allah ki sanar dani abinda ya yi muku don nasan ta inda zan kamo bakin zaren."

   Yamutsa fuska Aunty tayi tace "A da nayi tunanin sanar da ke, to amma sai na gane duk taron kwaram da hama ne. Duk da haka zan sanar da ke tunda a matsayinki na uwa kina da haƙƙi kisan abinda ya ke faruwa da ɗanki."

Ajiyar zuciya Inno ta sauke tace "Hakane Ƴarnan"

Miƙewa tsaye Auty ta yi ta harɗe hannunta a ƙirji tace "Hajiya Inno ɗanki Yunusa ya karɓi kuɗi a hannun wannan shashashar yarinyar nan har Naira miliyan ɗaya, ta bashi tsabar kuɗi har Naira dubu ɗari biyar a hannu da sunan ɗaukan adashi. Abin bai tsaya nan ba ta kwashi Kuɗi mai tsoka daga wanda take juyawa don riƙe kanta da iyayenta har ma da ke da ɗanki, ta haɗa masa Lefe bashi na Naira dubu ɗari biyar bisa sharaɗin duk wata zai dinga bata Naira Dubu ɗari na zubin adashi da kuma biyan bashi..."

"Ƙarya ki ke yi, ta ina ɗan marayan Allah zai iya biyan wannan maƙudan kuɗaɗe, to da ya karɓa ma mai yayi dasu? Kawai don bai auri ƴarku ba sai ku fara binshi da sharri, to wallahi bazai yiwu ba, ai yana hanya yiiiii yiiii" ta ɓarke da kuka tamkar mai jiran ƙiris, cikin shessheƙa ta ɗora "Yara na son junansu, don mugun abu kuna son datse alaƙarsu don mugunta..."

"Hajiya! ina son ki buɗe kunnenki da kyau ki saurareni, kuɗi dai ɗanki ya ci, wallahi ko zaki maidashi cikinki sai ya biya kuɗinnan. Bari ina ganin girmanki don a ƙallah nasan ko baki haifeni ba kin kusa, da ba don haka ba wallahi da na nuna miki cikakkiyar kalata Antin Kano nake, kaf zuriyarmu ba wanda bai sanni ba wurin tsage gaskiya da ƙwatowa mai haƙƙi haƙƙinshi ko da hakan zai zama sanadiyyar haɗewar sama da ƙasa." Zaman rigarta ta gyara sannan ta ɗora
"Kin ganni nan ni kaina tsoron kaina nake, don wallahi rikici na yafi rikicin tsohuwar mota, idan kuma na rikice hohoho da mutum ya taɓani gara  ya rungumi taransifomar da take tartsatsi ana tsaka da ruwan sama. Inno ban so na saki a cikin tafiyar nan ba, amma tunda kin shigo ba laifi dama ɗan kuka ke jawa uwarsa jifa, to a wannan karan ita kukar da kanta ta jawa kanta tunda har ta fitar da ƴaƴan..."

Cikin tsawa Inno tace "Ya isheki haka! Bana son fitsara, ga Haleema nan a gabanki ki tambayeta duk abinda tayi mana roƙarta muke? Ita tasa kanta a matsayinta na ƴar siyasar da take kamfen, kuma halak ne cin kuɗin kamfen ƙarƙari ko ka ci ka zaɓi shugaban da kake ganin zai fi kawo maka abin alkhairi."

Wata shegiyar dariya Aunty tayi tace "Ba shakka barewa ba tayi gudu ɗanta ya yi rarrafe ba, da nice naci kuɗin kamfen haka to da ba shakka dole ne na haɗa duk ƴan takarar na miƙa musu kujerar, kinsan me yasa?"

Bata jira cewar Inno ba ta ɗora "Saboda da alama duk tana buƙatar ƴan takarar, musamman ta wajena, amma idan kina musu mu jirayi ƙarasowar ɗaya algungumin kuma munafikin mata."

************

    A ɓangaren Baban Mama kuwa, hankalinsa a tashe ya miƙe suka shiga wanka da Hadiza, suna fitowa ya zira kaya ya ɗau mukullin mota zai fice. Ba shiri Hadiza ta fashe da kuka tace "Gaskiya sai na bika, idan ka tafi hankalina bazai..." "Taho muje" Ba ɓata lokaci ta ɗora baƙar riga akan kayanta ta naɗa mayafi suka faɗa mota suka nufi gidan Inno.

A gidan Inno kuwa ganin musayar magana ba zai musu ba, sai kowa ya ja bakinsa ya tsuke ana jiran raba gardama ya zo.

  Leema kuwa banda shessheƙa ba abinda take, ita tunaninta ɗaya kar Baban Mama yace ya fasa aurenta...

Ƙarar wayarta ce ta katseta da sauri ta zabura ta ɗauka, ba suji mai tace ba sun dai ji ta ƙara fashewa da kuka.

A fusace Aunty tace "Shegiya ƴar iska, mai janyowa mutane jarfa garin son gwanintarki da neman suna don bu... nawa ne a account ɗinki yanzu?"
"Dubu ɗari da hamsin ne, kuma dubu ɗari uku zan tura masa"

Waya Aunty ta zaro tace "Dallah rufemin baki shashasha gidahuma da bata san mai duniya take ciki ba, don uwarki samin account number ɗinshi anan, kar matarshi ta mutu ta rataya a kanki. Sannan ki tura masa ɗari da hamsin ɗin, zan sa a tura masa sauran."

Jiki na rawa ta turawa Yaya Lamiɗo kuɗin, Aunty kuma ta kira Alhaji cikin kwantar da murya tace "Don Allah Alhaji ka ranta mana dubu ɗari da hamsin ta accout ɗin da ta turo maka a text, emajansi ne CS za'a yiwa  Matar yayan Leema kuma don shashanci tabar kuɗin a gida." A take kuwa Alhaji ya tura kuɗin don ya ji maganar rashin lafiya ce, kuma Aunty bata masa wasa da kuɗi.

Ganin haka yasa jikin Inno ya yi sanyi, kamar kazar da aka tsamo a ruwa...

Tunaninsu ne ya katse jin ana cewa "Wayyo Baby ka riƙeni kar na faɗi, ƙafartawa bata warke ba uhum uhum.." Kafaɗarta ya kama suka nufi ɗakin Inno a zabure Leema ta miƙe tana kallon Hadiza.

Wata shegiyar dariya Hadiza ta yi tana binsu da kallon tsana da rainin hankali...

ALLAH YA GAFARTAWA IYAYENMU

MUM AMNASH🖊️

SO KO WAHALAWhere stories live. Discover now