SO KO WAHALA? PART 74

33 1 1
                                    

*HAƊAKA WRITER'S ASSO...🖊️*

*❤️😭SO KO WAHALA?😭❤️*

                  NA

MARYAM M SANI (Mum Amnash)

5/J-ula/1443 - 11/12/2021

                7️⃣4️⃣

"Subhanallahi!" Suka furta da sauri suka yi baya, ƙiris ya rage ƙaton itacen ya sauka a kan su.
"Assha! Allah ya taƙaita Alhaji sannunku da zuwa. Ku yi haƙori wallahi na zata ɓarayi ne. Da yake kwanakin baya haka a ka zo a ka sace mana dabbobi. Ku shigo daga ciki."

Ba musu suka bi bayan Baba Ubale, wani ɗaki da yake zaure na biyu ya kai su ya shimfiɗa musu tabarma sannan ya fice da sauri ya nufi ɗakin Kaka.

Ga mamakinshi sai ya tarar da su zaune suna hira Adamalliya har da ɓaɓɓaka dariya.

"Ikon Allah! Wai na kwance ya faɗi. Baba da alama fa ba ɓarayi ba ne, baƙi ne daga birni."

"Dama wa yace maka ɓarayi ne? Wai yaron da yake son ƴar wajenka Salaha ne fa, to tsoron abin da ka je ya zo ya sa ta gudo ƙauye don kar a ƙara kwata irin ta Izawaƙa. Amma da yake tsakani da Allah yake son yarinyar ai ka ga ya biyo sahu..."

Ko gama saurarar Adamalliya bai yi ba, ya fita da sauri kamar ya tuntsura. Yaro ya aika ya kira masa Maƙocinsu Biliya a gona. Daga nan ya siyi ruwan leda sannan ya nufi gida.

Sai da ya ajiye musu ruwan sannan yace "Ku yi haƙuri na barku ku kaɗai."

"Ba komai Baba." Khamis ya amsa.

"Madallah! Bari na yi muku iso sai ku ƙarasa ciki."

Sai da ya sanar da su Kaka suka ƙara kimtsawa sannan ya yi musu jagora har cikin gidan.

A tabarmar karaunin da a ka shimfiɗa a gefen gadon karan dake kafe a ɗakin suka zauna. Fuskar Yaya Kabiru a washe ya gaishesu "Barkanku da warhaka."

"Barka kadai yaro." Adamalliyya ta amsa sannan ta ɗora "Ya hanya? Ya ku ka baro mutan gidan?"

"Lafiya ƙalau, Alhamdulillah. Hajiya Kaka gamu mun zo gareki ɗauke da ƙoƙon bararmu ko Allah ya sa mu dace."

"Insha Allahu kun ma dace, tunda har ku ka tako wurin Ubanta Ubale magana ta ƙare. Dama da kun biye ta Laure to ko za a yi auren sai ta baku wahala don sam ba ta da kan gado..."

Kaka da ke lulluɓe da zani kamar amarya ta zame lulluɓin ta katse Adamalliya "Ai ke kan gadon gareki. Har ke ce za ki nemi faɗa mini magana? Wai tukunna ma kin manta a gaban surukai muke?"

"A'uzu!" Adamalliya ta furta ta ɗora hannu a kan bakinta.

Dariya Khamis ya yi yace "Haƙuri za a yi Kaka, ai mu na gida ne, tun da muna biɗar ta gida."

"Khamis Kamsusi uban magana! Wai ina abokinka Isa? Ko a waya ba kira ba labari."

"Caɓɗijam! Wai Isa? Ai tun da ki ka tafi ya daina ko waiwayar gidanku dama yace wurinki yake zuwa. Tunda ba kya nan ya bar zuwa."

"Allah sarki Isa! Yaron kirki kenan. Nima ina nan hankalina na can garesu. Duk a zaton su guduwa na yi, amma ni zuwa na yi na sanar da iyayenta da can dangin Mahaifiyarta don su san da shirin aurar da ita. Kakanta Baffajo Baban Marigayya Gyatumarta duk lokacin da na je don mu gaisa ya dinga ɓarka kuka kenan yana roƙon Allah kar ya mutu ba tare da an aurar da Salaha ba. Shi yasa bana son zancen wani Karatu, ko don tsohonnan ya sauke nauyin da ke kanshi da ranshi. Zuwa da ka ya fi saƙo. Tun da Allah ya kawo ka daurewa za ku yi mu je can rigarsu, ba nisa sosai, sai ka gaishesu a matsayin dangin uwa."

SO KO WAHALAМесто, где живут истории. Откройте их для себя