SO KO WAHALA? PART 53

28 7 9
                                    

*HAƊAKA WRITER'S ASSO...🖊️*

*❤️😭SO KO WAHALA?😭❤️*

                     NA

*MARYAM M SANI (MUM AMNASH)*
*WATTPAD: @mumamnas2486*

17/Safar/1443 - 24/9/2021

              5️⃣3️⃣

  Tebur ɗin shi ya ɗauko ya kafa, sannan ya dasa ƙatuwar Leema ya danneta da manyan duwatsu. Don tun rannan sun shigo Kasuwar Khamis ya nuna masa komai, da taimakon Abokin Khamis Musa.

Wayarsa ya zaro ya kira Khamis, sai da suka gaisa sannan yace "Khamis na shiga kasuwa, na rasa yanda zan yi wallahi. Don Allah ka kira wanda kayana suke hannunshi kafin na je." Dariya Khamis ya yi yace "Tofa! Aiki ya samu Maza, wallahi babu wanda zai zo taya ka zama a Kasuwa, ka zage ka yi komai kan jiki kan ƙarfi. Allah ya taimaka, Allah ya bada nasara. Allah ya sa ka fara a sa'a. To ai shagon ma ba nisa daga teburanku, shi ne a ƙasan Ƙaton ginin (plaza) da ke bayanku. Bari na kira shi, Allah ya bada sa'a."
"Amin" Isa ya amsa a sanyaye.

  Masu kai komo kawai yake kallo, yana nazarin Kasuwar. Kasuwar Fam Santa (farm center) kasuwa ce ta sayar da wayoyi da duk wani abu da ya shafi wayar hannu. Akwai masu sayar da kayan sawa da takalma, amma ba su da yawa sosai. Mafi yawan masu hada-hada a cikinta Maza ne. Jefi-jefi Mata ke shigowa, yawanci wasu Matan ba sa iya shiga sai da rakiyar Namiji. Sai kuma Mata masu sayar da abinci, waɗanda ba su da yawa sosai.

Zumbur ya miƙe, ya nufi wurin Maƙocin Teburinshi. Hannu ya miƙa masa haɗe da sallama "Assalamu Alaikum"
"Wa'alaikumussalam" ya amsa fuskarshi ɗauke da alamun rashin sani. Murmushi Isa ya yi yace "Suna na Isa, ni baƙo ne a wannan kasuwar. Teburi na yana gefen na ka." Ya ƙare yana nuni zuwa ga teburinshi.
Fuska a sake yace "Masha Allah Malam Isa, Allah ya sa ka fara cikin nasara da aminci. Kasuwar nan tana da albarka, matuƙar ka kiyaye cuta da damfara Insha Allahu za ta kai ka inda ba ka yi tsammani ba. Suna na Jabir, na fi mayar da hankali a kan gyaran waya da sayar da ƙananun wayoyi." Fuskar Isa a sake yace "Muna ɗaya da kai, nima na fi yin gyaran wayoyi kuma yanzu ma ƙananun na sara da cajoji da abinda ba a rasa ba."

Sai da ya numfasa sannan ya dubi Jabir yace "Don Allah a cikin shagunan can wanne ne na Alhaji Sha'aban mai agogo?" 
"Wancan babban mai ƙofa biyu ne, hala a wurin shi ka yi sari?"
"Eh, abokina ne ya haɗani da yaronsa suka kammala mini komai. Bari na je na karɓo kayan, Allah yasa Musa ya zo."
"Ya zo, don naga wucewarshi. Za ka ganshi da farar shadda a jikinshi." Jabir ya ƙare zancen yana duban tsalelen tsadadden agogon da ke ɗaure a tsintsiyar hannun Isa. Ras! Gabanshi ya faɗi . Jikinsa a sanyaye yace "Malam Isa bari na ɗan ƙarasa kimtsa wurin. Kai ma ka shiga ka karɓo kayanka, Allah ya sa a fara a sa'a."
"Amin" Isah ya amsa, sannan ya nufi shagon Mai agogo don karɓo gilas ɗin shi da sauran kayan shi.

Babu ɓata lokaci ya nemi Musa, ya taya shi ɗebo kayan suka jera wayoyin a cikin gilashin, bayan sun ɗora a kan teburin.

Alhamdulillahi ba laifi, don an sayi wayoyi biyu a hannunshi kuma ya gyarawa wani saurayi guda ɗaya.

___________

Tun a mota ta ci kukanta ta ƙoshi a cikin Hijabi, tana sauka a Zaria ta kira Aunty Salama. Sannan ta nufi gidanta kai tsaye, don ta san matuƙar ta nufi Kaduna da ƙatuwar akwatinnan akwai babbar matsala.

Buɗe mata ƙofa Aunty Salama ta yi, fuskarta ɗauke da mamakin ganinta. Sai da suka shiga falon suka zauna, sannan ta dubi Leema tace "Da fatan dai ba barkono ki ka dako ba. Don an daɗe da wuce wannan lokacin. Duk macen da ta san kanta, tasan me take yi, to ba za ta fara wannan ɗanyen aikin ba."

Fuskar Leema a cunkushe tace "Nifa ba yaji na yi ba, aiki na dawo. Kuma ba zan koma ba sai nan da wata uku, in na ga da yuwuwar komawar."

Dariya Aunty Salama ta sa tace "A sani na aure yana kimtsa mutum, to ke dai ina jin sai kin haihu za ki yi hankali." Ta ƙare zancen fuskarta a tsuke, alamun ba wasa a maganarta. "Haleema me ya haɗa ku da Isa?"

SO KO WAHALAWhere stories live. Discover now