SO KO WAHALA? PAGE 46

33 4 17
                                    

*HAƊAKA WRITER'S ASSO...🖊️*

*❤️😭SO KO WAHALA😭❤️*

          NA

MARYAM MUHAMMAD SANI (Mum Amnash)
*Wattpad @mumamnas2486*

28/Al-muharram/1443 - 6/9/2021

              4️⃣6️⃣

Matsowa Khamis ya yi yace "Wai haka tace? Kawai ka manta da ita wallahi. Isa akwai abinda nake son tunatar da kai, kai fa Mutum ne da baya zurmewa a soyayya, dole idan kai ka haƙura ka rungumi auren nan farat ɗaya, ba zai zamo haka a wurin Leema ba. Ka yi iyakar ƙoƙarinka wurin kyautata mata, ina nan da kai da kanta wata rana za ka bani labarin irin soyayyar da za ta nuna maka. Kayi haƙuri, ka yi haƙuri shi kaɗai zai taimaka wurin ingantuwar aurenku. Isa ni kaina ba zan ɓoye maka ba wallahi ban ji daɗin abinda ta yi ba, amma dai haƙurin shi ne mafita."

Murmushin yaƙe ya yi yace "Ba komai Khamis, ina godiya sosai insha Allahu zan yi yanda ka ce. Bari na tashi kai na ya fara ciwo, gwara na yi gida na kwanta."

"Allah ya sauwaƙe" Khamis yace ya biyo bayanshi don rakashi gida.

   "Haleema wallahi da ba don darajar auren da ke kanki ba, da idan na fara jibgarki mai ƙwatarki a hannuna sai Allah. Yarinya kin gallabi kowa, Mahaifinki kuka ya dinga yi shaɓe-shaɓe  saboda fasa aurenki da a ka yi, amma da a ka canja da Isa baki ga farincikin da ya dinga yi ba. Amma tunda kunnen ƙashi gareki, zan sanar da Gambo abinda a ke ciki, ɗazun nan ya tafi, idan bakya son auren a raba auren kawai. Kin ga idan ki ka koma sai Mutane su tabbatar da zargin da suke yi miki na yawon ta zubar."

Kuka Leema ta rushe da shi, tace "Don Allah Baba ki yi haƙuri kar ki faɗawa Gambo, na yi miki alƙawarin komai zai faru zan zauna da Isa har ƙarshen rayuwata."

Hannun Baba ta kama ta ɗora a ƙirjinta tace "Baba kin ji yadda zuciyata take bugawa, Baba kamar zan mutu na ke ji, Baba har yanzu zuciyata taƙi ta yakice Yunus na huta." Ta ƙare zancen da matsanancin kuka.

Rungume ta Baba ta yi tace "Addu'a, duk lokacin da ki ka ji irin haka to ki yawaita addu'a da karatun Ƙur'ani, Shaiɗan ne yake ƙara saka miki wannan ƙuncin, tare da ƙayata miki soyayya  Mijin da ba naki ba, kuma ko ban faɗa ba kinsan halaka ce."

Sai da Baba ta nisa sannan ta ɗora "Kar ki yadda a ce Isa da yake Namiji ya fiki biyayya ga Magabatanshi. Ni na ma ga ƙoƙarinsu da suka bari ya aureki, duk da sukarki da wasu Mutanen su ke yi. Zancen da na ke yi miki har dangin Yunus a zatonsu cutar Ƙanjamau gareki shi, yasa a ka fasa aurenku. Ba kuma su kaɗai ba, kawai dai nasu ne ya fito fili. Don haka a matsayina na Uwa ina shawartarki da ki rungumi Mijinki hannu bibbiyu, da yardar Allah za ki yi alfahari da hakan."

Ba Leema ba, har Zahra kuka take yi, sai da suka natsa Baba ta ƙara yi mata Nasiha sannan ta wawware kayan, aka bawa duk waɗanda suka zo, sauran kuma Baba tace "Zan kaiwa Mamanki ita ma ta bawa ƴan uwanta, da waɗanda suka dace." Miƙewa Zahra ta yi don ta basu wuri, dama Baba ce ta zaunar da ita. 

"A shagwaɓe Leema tace "A'a Baba wallahi sai kin zaɓi atamfa ɗaya a ciki, su Mama da suka ƙi zuwa wurina, ni kece kawai Baba ta."

Dariya Baba ta yi tace "Eh da wannan kuma fa, tunda Sirikina ne ya bamu ko ɗaya ba zan basu ba. Bari mu miƙe uku ta kusa garinmu da nisa." Ta ƙare zancen  tana murmushi, Leema tana gani suka tafi suka barta, har da ɗan kukanta.

  Suna komawa kuwa basu ɓata lokaci ba, suka haɗa yanasu-yanasu don tafiya. 

Mota guda Khamis ya kawo musu har ƙofar, ya biya kuɗin. Suka tafi suna alfahari da canjin da Leema ta samu.

Sai Bayan Sallar La'asar sannan Aunty ta kira Isa, ta sanar da shi duk yanda suka yi da dangin Baban Mama. Amma ga mamakinta sai da ta gama bayaninta tsaf, sannan Isa yace "Aunty na gode muku sosai Allah ya saka da alkhairi. Amma saboda wani dalili ba zai yiwu tayi amfani da waɗannan kayan ba. Ku siyar da su har akwatunan, ku bata kuɗin garar ta. Lefe bazan yi ba, tunda ba addini bane. A hankali zan siya mata kayan sawa daidai ƙarfina." Ya ƙare zancen ya na juyar da fuska gefe, duk yanda Aunty ta so ya bar Leema ta yi amfani da kayan, ƙeƙasa ƙasa ya yi ya tuma gefe yace shi atafau Matarshi ba zata saka waɗannan kayan ba.

SO KO WAHALAWhere stories live. Discover now