SO KO WAHALA PART 18

36 3 0
                                    

*HAƊAKA WRITER'S ASSOCIATION*

*❤️😭SO KO WAHALA?😭❤️*

           NA

MARYAM MUHAMMAD SANI(Mum Amnash)
WATTPAD@mumamnas2486
BLOGSPOT@mumamnash.blogspot.com

12/Zulƙida/1442 - 21/6/2021

              1️⃣8️⃣

   Sai da suka gama murnar su, sannan Hajiya ta ce "Kyawun alƙawari cikawa, Hadiza sai ki koma wurin Malam Labaran ki bashi kuɗinshi ." Sai da ta taɓe baki sannan ta ce "Ni bazan koma wurin wani Malam Labaran ba , kawai zan baki kuɗin shi ki kai masa , ni ba na son biye-biyen nan."

Hangame baki Hajiya ta yi ta ce "Lashakka fihi, anya Hadiza ba za ki butulce mana ba nan gaba? Daga ganin sarkin fawa sai miya ta yi zaƙi, kya bari ki shiga daga cikin sannan ki soma firirita da sanabe ko?"
Dariya Hadiza ta yi ta ce "Haba Hajjajunmu ya za'ayi na butulce muku, kawai bana son zuwa ne. Amma ba komai da daddare sai mu leƙa, mu bashi haƙƙinsa mu huta, ba kare bin damo."

   Ana sallar Isha'i kuwa, suka lulluɓa gyalensu suka yi gidan Malam Labaran, ba su tarar da layi ba. Mace ɗaya ce a ciki, tana fitowa suka shiga. Tun shigowarsu Malam ya ke bin su da kallo, har suka samu wuri suka zauna.

  Dubu biyu Hadiza ta zaro a cikin ƙaramar jakar hannu, ta miƙa masa haɗe da godiya . Fuskarsa a murtuke kamar ta shanu  ya karɓi kuɗin, jujjuyasu ya yi ya ce "Wannan na mene ne?" Hajiya ta ce "Kuɗin wancan aikin da aka yi mana ne, madallah mun gode." Wani yawun takaici ya haɗiye ya ce "Yanzu tsakaninku da Allah, ya kamata ku ɗauki  Naira dubu biyu ku bani? Amma ba komai ku je don tuwon gobe ake wanke tukunya." Ba kunya suka miƙe , Hajiya tana ƙara bashi haƙuri.

   Suna fita Malam labaran ya ciji yatsa ya ce "Malalatan banza malalatan wofi, ai gwara da ban wahalar da kaina kan aikinsu ba. Waɗannan ko kaji buloras (Broilers) aka ce su kawo bai zama lallai su kawo ba mts." Miƙewa ya yi ya shiga cikin gidanshi, abinci aka kawo masa harda farfesun kaji daban a filas. Dama gidan Malam ba ya rabo da nama, don tashin farko idan ka je wurinshi , to duƙa-duƙan kaji zai ce ka kawo guda uku, ko tantabaru. Kuma don wani rainin wayo, cewa ya ke baya son kazar hausa sai ta turawa. Shi yasa shi da iyalansa suke ɓul-ɓul kamar ka taɓa jini ya fito, saɓanin masu kawo kajin da wata ma sai ta shafe sama da wata shida ba ta ci kazar ba, don a wannan rayuwar yawanci cin kaza sai sallah da mauludi ko kuma a gidan biki. Amma haka suke sayowa Malam kaji da sunan za ayi yanka da ita, alhalin shi da iyalansa suke shan dabgensu .

  Ka'in da na'in Amarya Hadiza ta mayar da hankali kan shirye-shiryen bikinsu da masoyinta. Kullin zancenta ɗaya My Yunus, ƙannenta ma sai suka koma kiranta da ta My, musamman Abida da ta ga gadon barcinta.

******************

     Bai ɓoyewa Hindu ba, ya sanar mata da sa ranarshi da Hadiza. Ba ta ce komai ba illa fatan alkhairi, sai kuma jikinsa ya yi sanyi ya fara janta da hira, ganin ba ta cikin walwala ya sa ya ƙyaleta kawai.

Washegari da wuri ya tashi, brush kawai ya yi ya bi Hindu kitchen, ƙaramar kujera ya samu ya zauna.

Yi ta yi tamkar ba ta ji shigowarshi ba, ganin haka ya sa ya yi murmushi ya miƙe tsaye, fita ya yi kawai, don yasan bai zama lallai ta kulashi ba.

   Ta na kammala haɗa kayan karin kumallo, ta kai su falo ta ajje sannan ta nufi ɗakinta ta yi wanka, ta yiwa Mama sannan suka fito.

  Tare duk suka karya, suna gamawa ya tafi kai Mama Makaranta, har ya dawo tunanin abinda zai yi ya farantawa Hindu rai ya ke.

Da sallama ya shiga gidan, ƙasa-ƙasa ta amsa masa duk da tana tsakar gida a lokacin. Kai tsaye falon ya shiga ya zauna, ganin baza ta kai masa ba ya sa ya fito tsakar gidan, hannunta kawai ya kama suka shiga falon.

  A ƙasa suka zauna, suna fuskantar juna, sai dai kanta a ƙasa ya ke taƙi ɗagowa. Murmushi ya yi, ya sa hannunsa ya ɗaga kanta, "Hindu ina son ki ɓuɗe idanunki ki kalleni, nasan yanda ki ke ji a zuciyarki, ke ɗin ta dabance a cikin mata dubu. A yanzu ba wani abu da zan iya yi miki na burgeki, amma ki daure ki ƙara haƙuri ki bani wata damar, Insha Allahu  ba za kiyi nadama ba. Allah ya saka miki da alkhairi, ya biya miki buƙatu na alkhai..."

Fashewa ta yi da kuka harda shessheƙa, jikinsa ne ya ƙara yin la'asar , gaba ɗaya ya rasa mai zai yi kawai sai ya rungumeta, ƙoƙarin ƙwacewa ta ke, amma ya hanata damar hakan, har sai da ta nutsu ta daina kukan don kanta sannan ya share mata hawayenta ya ce "Ki yi haƙuri, ki faɗi duk abinda ki  ke so zan siya miki." Kamar ta ce ba ta so, wani tunani ta yi sai kuma ta yi murmushi, don kaso tamanin na ƙuncin da ta ke ciki ya wuce, saboda kukan da ta yi.

Duk da ya san tana da saurin sauka idan ta yi fushi, amma ya yi mamakin saukarta a take. Kiran wayarsa Leema ta yi, sarai ya gani amma sai ya sa wayar a sailant don kar ta dameshi, don ya san halinta kamar zawo take ita ma wurin rashin haƙuri.

Sai da Hindu ta gama nazartarsa sannan ta ce "Yayana kuma mijina, bani da kowa a garinnan sai Allah sai kai, waɗanda na riƙe kamar iyaye, yanayi ya sa sun zama sirikanka. Wani abin takaici har suna goranta min akan wasu sirrikana da suka sani. Amma na godewa Allah da babu tarihin wani abu na assha a rayuwata. Kuma har yau ina kallon Hadiza a matsayin ƙawa kuma ƴar'uwa a wurina. Ina fatan itama ta riƙeni a yadda na ɗauketa."

Sai da ta sauke ajiyar zuciya sanan ta ce "Tabbas ina da buri nima kamar kowacce macce da aka tashi ƙarowa ƴar'uwa.
Buƙatun ba yawa ina son ka siya min firinji(fridge), sai kujerun nan ka bayar a gyaramin. Kaga ba daɗi aga ɗakin sarautar matanka a haka 
ko mijin?" Duk da bashi da kuɗin, samun kanshi ya yi da amsa mata kawai. Godiya ta yi masa da addu'o'in neman nasara, ya amsa cike da jin daɗi, don ko ba komai ya gama da wannan matsalar, saura ta Leema kuma.

  Ganin wayar ta na haske ya sa ya ɗauka, da sauri ya fita don ya amsa kiran.

   "Assalamu Alaikum Ango ka tashi lafiya?" Da mamaki a kan fuskarshi ya ce "Lafiya ƙalau, ya mutan gidan?" A yangance ta amsa "Lafiya ƙalau" murmushi ya yi don shi kanshi ya fara tausayawa kanshi zuwa yanzu, don da alama zai haɗawa kanshi jagwal.

Dakewa ya yi ya ce "Kina gida ne? Ina da magana mai muhimmancin da zamu tattauna." A taƙaice ta amsa masa "Eh ina nan, kuma dama nima ina son ganinka....

ALLAH YA GAFARTAWA IYAYENMU

MUM AMNASH🖊️

SO KO WAHALADonde viven las historias. Descúbrelo ahora