SO KO WAHALA? PAGE 30

39 3 3
                                    

*HAƊAKA WRITER'S ASSOCIATION*

*❤️😭SO KO WAHALA?😭❤️*

           NA

MARYAM MUHAMMAD SANI(Mum Amnash)
WATTPAD@mumamnas2486

    6/Zul-Hajj/1442 - 17/7/2021

 
                 3️⃣0️⃣

   Kanta a ƙasa ta amsa cikin in'ina "Na'am" basarwa Aunty tayi suka gaggaisa da duk mutanen ɗakin, suka ajje kayan dubiyar da suka kawo masa suka miƙe don tafiya.

Yunƙurawa Baban Mama ya yi yabi bayansu, sai dai ina tuni sun miƙi doguwar barandar sun nufi hanyar fita, girgiza kanshi kawai yayi don yasan yau kashin Leema ya bushe, ta ɗebo ruwan dafa kanta. Shi kanshi ya so yayi mata magana ta tafi gida, amma gudun kar ya yarfata yasa ya ƙyaleta.

  Suna isa gida Aunty ta shige ɓangarenta ta rufe ƙofa, dariya Isah ya yi ya cewa Mama "Gaskiya yau a kwai magana a gidannan, Leema ba ta jin magana taurin kai yawa jinjirjirar jaka. Amma ta haɗu da daidai it..." Katseshi Mama tayi tace "Ya isa haka, koma meye ina ruwanka ni bana son shisshigi wallahi." Jan bakinshi ya yi ya tsuke ya shiga nashi ɗakin ya kwanta yana hakaito irin wulaƙancin da Aunty za ta yiwa Leema.

   Leema kuwa tun fitar su Aunty hankalinta idan ya yi dubu ya tashi, ba shiri ta yiwa su Inno sallama ta goya jakarta don tafiya gida.

Har ta ɗora hannunta a mabuɗin ƙofar ta juyo ta kalli Baban Mama sai kuma ta fice da sauri.

Miƙewa yayi ya bi bayanta, a hankali ya kira sunanta "Haleema" juyowa tayi idanunta sun kaɗa sun yi jajir, sai da ya  ɗau kusan minti biyu sannan yace "Haleema ya za ki yi da Aunty?" Jikinta a sanyaye tace "Ba yanda zan yi da ita sai dai na bata haƙuri, nasan ban kyauta ba da na zarto nan, to amma ya zanyi da raina? Hankalina ba zai taɓa kwanciya ba matuƙar na zarce gida ba tare da naga yanayin jikinka ba..." kasa ƙarasawa tayi saboda shessheƙar kukan da take yi, sai da ta goge fuskarta sannan tace "Yunus meye laifina da mutane ke neman tsanata akan sonka? Me nayi da zafi haka, ba laifina bane laifin zuciyatane, Wannan wacce irin soyayyace?  SO KO WAHALA? Ina jin zan iya fuskantar ko wane irin ƙalubale matuƙar a kanka ne. Kar ka damu, zan tafi gida yanzu, kuma suna da ikon hukuntani da kowanne irin mataki matuƙar ba rabuwa da kai bane." Gyara zaman jakar goyonta tayi ta tafi da sauri, kasa magana Baban Mama yayi ya bita da kallo kawai, tausayinta ya ke ji wallahi da ba abinda zai sa ya aureta duk da tarin ƙaunarta da ya ke.

Mene ne amfanin hankali da tunani? Aunawa da lissafa duk wani abu da zuciya ta bijirowa mutum da shi, shin zai yiwu? Me zai faru idan an yi? Barin ko yin wanne yafi alkhairi? Amma wasu da zarar sun faɗa so, shi kenan sai su makance, su kurumce, su fita daga hayyacin... Muryar Dr Zayyad ce ta katse masa tunaninsa yace "Lallai Yunus jiki ya yi sauƙi, dama tun jiya nake nemanka wallahi ta  samu fa, mu je ofis na faɗa maka"
  Bin bayanshi ya yi suka nufi ofis ɗin Dr zayyad.
  Tun fitarshi Likitan da ya ke dubashi ya zo, takardar sallama ya basu yace "Mama za ku iya tafiya gida, amma akwai buƙatar na ƙara gwada BP ɗinshi sai ku wuce" Godiya Inno ta yiwa Likitan ta fito neman Baban Mama, kusan ko ina duk ta duba amma baya kusa da ɗakin. Dole ta haƙura ta koma ciki, Hindu ta dubi Inno tace "Inno baki ganshi ba ko? Allah yasa ba raka amaryar tashi ya tafi ba, kinsan Laila da Majnoon." A fusace Hadiza ta juyo kamar zata make Hindu, kome ta tuna kuma sai tayi shiru, fuskar nan kirtif kamar kunun kanwa.

Murmushi Hindu tayi tace "Inno bari na tattare kayan nan nayi gaba, zan je na ɗora girki kafin ku ƙaraso." "Eh kema da gaskiyarki Ƴar albarka, ki wuce sai mun ƙaraso."
Har Hindu ta kai bakin ƙofa ta juyo tace "Amarya sai kun taho" ba ta jira amsar Hadiza ba tayi gaba abinta.

 
   Cikin sanɗa ta shiga gidan kai tsaye ɗakin Mama ta shige, ta zauna gefen gado tayi tagumi da hannayenta biyu, da taji motsi sai ta zabura, sai taji shiru sannan hankalinta zai kwanta.

SO KO WAHALAWhere stories live. Discover now