SO KO WAHALA? PART 15

44 4 2
                                    

*HAƊAKA WRITER'S ASSOCIATION*

*❤️😭SO KO WAHALA?😭❤️*

           NA

MARYAM MUHAMMAD SANI(Mum Amnash)
WATTPAD@mumamnas2486
BLOGSPOT@mumamnash.blogspot.com

7/Zulƙida/1442 -  16/6/2021

      1️⃣5️⃣

   Cikin hanzari Hadiza ta tura maganin ƙarƙashinta ta ɓoye , Abida kuwa yi ta yi kamar ba ta gani ba ,ta wayance da neman hijabinta, ta ɗauka ta nufi ƙofar fita. "Abida" Hajiya ta kirata, da sauri ta juyo ta tsugunna a kusa da Mama . Gyaran murya Mama ta yi ta ce "Abida ke wacce irin yarinya ce? Ana nuna miki gabas kina nufar yamma, idan ba haka ba mai zai hana ki ƙi bawa ƴar uwarki haɗin kai. Uhum idan ta auri Ɗantalikin nan muma mun huta da wahala , ki ka sani ko har jami'a ya biya miki kinga ai mun huta ko?" Dariya ce ta kusan ƙwacewa Abida amma sai ta daure ta kanne, ta ce "Eh Mama duk na gane abinda ki ke nufi, sai dai wani hanzari ba gudu ba, indai Yaya za ta auri Baban Mama don kuɗi, to wallahi garama ta  haƙura ,don bashi da su . Kinga gidan da ya ke ciki na haya ne ,ita ma Yayar na haya zai kama mata. Na biyu motar da ya ke hawa ta kamfaninsu ce ba tashi ba ce. Na uku bayan ya Auri Yaya akwai yarinyar da su ke tare ,ita ma aurarta zai yi. To kinga Mama ta ko ina matsala ke zagaye da auranshi, amma idan Yaya ta ji ta gani, to zan tsaya mata sai inda ƙarfina ya ƙare."

Cikin jin daɗi Hajiya ta rungume Abida , sai dai a ƙasan zuciyarta wasi-wasi ke damunta don tasan Abida ba ta ƙarya , zai wuya ta ƙirƙiri zance ta ɗorar. Wata zuciyar ta ce to banda abinki Abida ai yarinya ce, kuma a wurin Matarshi ta ji komai , bai zama lallai ta faɗa mata gaskiya ba , duk da dai ita ma Hindun ba safai ta ke ƙarya ba .

Ajiyar zuciya ta sauke ta ce "Yauwa Abidedena tashi ki yi wankinki in anjima ma ƙarasa tattaunawa. Murmushi Abida ta yi, ta miƙe ta fice .

" Anya Hajiya ma yi saurin yarda da yarinyar nan, kar ki manta taurin kai gareta kamar jinjirin jaki ,amma farat ɗaya ta bamu goyon baya ba ayar tambaya kuwa? Nidai gaskiya ban yarda da ita ba wallahi . " A fusace Hajiya ta ce "To Hadiza je ki yi duk yanda ki ke so , tunda ni Uwarki ban iya ba . Abidar nan dai ƴar'uwarki ce , in ta tona mana asiri ai kanta ta tonawa. Ni na gaji da sha'aninki kinji , abu tamkar cin ƙwan makauniya ya ƙi ƙarewa, ki je ki ƙarata ni na yi nan." Ta kaɗe zaninta ta yi waje , a maimakon Hadiza ta ba ta haƙuri sai ta gyara kwanciyarta ta rufe idonta ruf tamkar mai bacci.

************

    Tun da ta sauka a Kano ta ke jin wani nishaɗi na ratsa ta , ko ba komai ta shigo garin masoyinta ai . Hankalinta bai fara tashi ba sai da ta hau Adaidaita sahu ta kusa ƙarasowa gidansu Auntin Kano , addu'a ta yi ta yi ta nufi ƙofar gidan ƙirjinta na bugawa fat-fat ,da ƙyar ta ke ɗaga ƙafarta.

Ta na zura kanta su ka haɗu da Isa, da tsananin farin ciki ya tare ta ya ce "Kaga su Hajiya Dubu manyan ƙasa, har kin gama yajin kin dawo? Ai na ɗauka ba za ki ƙara dawowa ba." Ya ƙare zancen da dariya , jakarta ya ɗaukar mata su ka nufi cikin gida.

Wannan karan har da doya da dankali ta siyo musu , Isa na gani ya ƙyalƙyale da dariya ya ce "Wai Bayahudiya yau har da cin hanci ki ka taho mana da shi , to ai mutuniyar ta ki ba ta nan . Ta tafi can gidan Kishiyarta dubo ta ba ta da lafiya , ƙila ma sai dare za ta dawo."

Ɗan yaƙe kawai Leema ta yi ta nufi kicin ta ɗebo abinci ta zauna ta fara cakula. Isa da ke dubanta ya ce "Bayahudiya ta ya za'ayi ki yi ƙiba, ba kya son cin abinci , sai ki ɗebo kaɗan kamar za ki bawa na goye." Wata dariya ya fara har da riƙe ciki , da mamaki Leema ta dube shi, cokalin hannunta ta ajje ta fara binsa da kallo, girgiza kai ta yi ta ce "Anya Isa ba ka fara shaye-shaye ba  kuwa , don ruwa ba ya tsami banza, idan ko ba ka zuƙe-zuƙe zan miƙa ka sakatiric gaskiya."

SO KO WAHALANơi câu chuyện tồn tại. Hãy khám phá bây giờ