SO KO WAHALA? PART 65

25 1 0
                                    

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/EiQ3qtht0QSLRElOcqt3CP

*HAƊAKA WRITER'S ASSO...*

*❤️😭SO KO WAHALA?😭❤️*

         NA

MARYAM M SANI (Mum Amnash)
*WATTPAD:@mumamnas2486*

19/R-Auwal/2021 - 25/10/2021

*TALLAH! TALLAH!! TALLAH!!!*
*KISHIN KUSHEWA ƙayataccen littafi ne da MAMAN DR marubuciyar DUDUWA, SAMEEHA DA GUDIL ta zo muki da shi a kan farashi mai sauƙi #100 kacal ACCOUNT:Zenith Bank Umma... SHAIDAR BIYA, TURA KATI KO ƘARIN BAYANI TA:07065014495*

              6️⃣5️⃣

  Wata ranar Juma'a da yamma Salaha na yi mata girki Isa ya shigo gidan. Kai tsaye madafar ya nufa, ganin Salaha ce ke girkin ya sa yace "Yau ke ki ke yin girkin?"
"Eh, Ina yini?"
"Lafiya ƙalau. Ya su Kaka?"
"Suna nan ƙalau."
"Masha Allah" Har ya yi gaba, sai kuma ya dawo. Fuskarshi ɗauke da murmushi yace "Salaha" kanta a ƙasa ta amsa "Na'am"
"Kar ki tafi ba tare da kin yi mini sallama ba, akwai maganar da nake son mu tattauna."
"To Yaya" ta furta jikinta a sanyaye.

Wani irin takaici ne ya ƙume Leema dake maƙale a jikin wundo tana kallonsu. Jikinta a sanyaye ta koma kan kujera ta zauna dafe da kanta dake ciwo sakamakon ranar da ta ɗebo ga kuma azumi.

Da sallama ya shiga ɗakin "Assalamu Alaikum"
"Wa'alaikumussalam" ta amsa a ciki-ciki. A gefenta ya zauna yana nazartar yanayinta, zamewa ƙasa ya yi ya fara matsa mata ƙafufunta da suka ɗan kumbura saboda zaman mota.

Janye ƙafarta ta yi tace "Don Allah ka ƙyaleni, baka ganin azumi ne wai." Ƙyalƙyalewa ya yi da dariya yace "To miye a ciki, babu ta yanda za a yi uzurin da ki ke ƙoƙarin kawowa ya samu gurbin zama a zuci a wannan lokacin, saboda kin sha tafiya,  ga azumi, ga ɗan karen kishi da nake hangowa a idanu..."

Ranta a ɓace ta miƙe, ta rasa dalilin da yasa Isa yake saurin fahimtar yanayin da take ciki. Abubuwa da yawa ba ta faɗa masa, amma sai ya canka. Ko don shaƙuwar da suka yi ne a baya...

"Ba faɗa mai ya kawo gaba? Indai ni ne ba baƙon zafi bane na  sanyi n. Bari na fita waje sahuna a likkafa, tunda Madam Leema a sama take. Na tafi, na dawo idan ansha ruwa. Ko ba komai, idan ciki ya ɗauka sai a ɗora da kayan marmari ko kuwa?"

Juya masa baya ta yi ba tare da tace kanzil ba. Ganin haka ya sa ya fito tsakar gidan, don ya yiwa kansa alƙawarin ko Malam Mahaifin Salaha ba zai san abinda ke tsakaninsu ba sai lokacin sanin ya yi.

"Salaha" A zabure ta juyo, don bata ji alamun sahunsa ba. Kanta a ƙasa tace "Na'am"
"Ina ƙofar gida ki fito ina jiranki idan kin gama."

Bayanshi ta bi da kallo, idanunta na cikowa da ƙwalla. Tsoronta Allah, tsoronta kar Isa ya ƙara janyo musu magana da jidali. Amman koma mene ne, za ta yi ƙoƙarin tare hanzarinsa idan har abinda take zato shi yake nufi."

Da hanzari ta kammala girkin, ta tattara komai ta share ta wanke kwanuka sannan ta ja madafar ta rufe. Jiki a sanyaye ta tsaya a ƙofar falon, haka kawai ta kasa shiga. Sai da iska ta ɗaga labule sannan Leema ta hango ta, a take haushin kanta da na yarinyar ya rufeta. Sai da ta ɗau kusan mintuna Uku sannan ta yunƙura ta fito, fuskarta kadaran-kadahan tace "A'a ya baki shigo ba, ko tafiya za ki yi?"
"Eh gida zan tafi."
"Shi kenan, ki ɗebi duk abinda ki ka yi ki tafi da shi."
"An gode" Salaha ta furta, da sauri ta nufi Madafar ta zuba soyayyiyar doyar a ƙaramin filas, sannan ta zuba miyarshi a wata roba ta saka a leda mai zane-zane ta fice da sauri.

Har lokacin yana tsaye a can gefen Masallaci, cikin sanɗa ta wuce, tana gab da shiga gida ya hangota, kafin ya kirata ta shige da sauri. 

Murmushi kawai ya yi ya saka hannunshi a cikin aljihunshi ya ɗau carbinshi ya cigaba da salati da hailala.

SO KO WAHALAWhere stories live. Discover now