SO KO WAHALA? PART 54

25 4 0
                                    

*HAƊAKA WRITER'S ASSO...🖊️*

*❤️😭SO KO WAHALA😭❤️*

                  NA

MARYAM M SANI (Mum Amnash)

29/SAFAR/1443 - 27/9/2021

_ASSALAMU ALAIKUM ƳAN UWA INA BUƘATAR ADDU'ARKU GA KAWUNA YA CIKA SHEKARA GUDA DA RASUWA ALLAH YA GAFARTA MASA TARE DA  IYAYENMU DA DUKKAN MUSULMAI AMIN_

                  5️⃣4️⃣

Sai da ya natsa da dariyar da yake yi sannan yace "Haba Kaka duka-duka nawa Salahar take? Don Allah ki daina surutu a kanta. Nan fa ba ƙauye ba ne."

Kaka ta geɓare baki tace  "Dama faɗan da ya fi ƙarfinka ai wasa ka ke mayar da shi. Ta fa kammala Sakandare, to ina ya Allah babu, suka yi jarrabawa ɗaya kawai ta faɗi ta ci takwas, shi ya sa ta dage da ɗinkin hula don ta samu kuɗin biyan Makaranta." Kaka  ta ƙare zancen a sanyaye.

Da sauri Salaha ta fita daga ɗakin, zuciyarta cike da takaicin rashin sirrin Kaka. Daga ganin mutum ta hau bashi labarinta, ba gaira ba dalili.

Jikin Isa a sanyaye yace "Kaka ki daina ɗaga hankalinki, karatun Mata yana da muhimmanci. Kin ga Mata ta ɓangaren aikin jinya ta karanta, yanzu abashin da take ɗauka ya kai kusan Dubu Ɗari. Da albashinta take taimakon kanta, har da ƴan uwa da abokan arziƙi."

Gwalalo ido Kaka ta yi tace "Danƙari! A'a'a dama haka a ke samun kuɗi da bokon? Ka ce dai karatun yana da amfani. Da Tsalha zai iya da ya biya mata wallahi, ka ga idan ta fara aikin gwamnati a dinga ragargazar daɗi a gidannan."

Tausayin Kaka da dariya ce suka zo wa Isa a lokaci guda, amma sai ya danne dariyarsa yace "Kaka ai ba don aiki kaɗai ilimin Mace ke da muhimmanci ba. Aikin ma ai sai mai rabo a wannan lokacin. Ni ma ai rasa aikin na yi shi ya sa..."
"Dakata ɗannan! Yi mini magana da yaran da zan gane. Wato shi karatun ma idan an yi babu tabbacin samun aiki kenan? Aradu ba zan bari ta yi ba. Da zarar ta samu Miji aurar da ita za mu yi kowa ya huta. Ni na rasa wannan jaraba ta Mazan birni, babu saurayin da yake zuwa gun yarinyar nan da sunan zance, duk da kyawun da take da shi. Amma idan ta je ƙauye, hum, ni kaina Kakata yanke saƙa take yi. Tsabar tururuwar kawo hasafin da samari masu ƙaunarta ke yi mini. Amma nasan duk naci na Gyatuminta ba zai yarda a aurar da ita a ƙauye ba."

Fuskar Isa ɗauke da murmushi yace "Haba Kaka ina zaman ƙauye zai yiwu a wurin Salaha? Ki yi ta yi mata addu'a Allah ya kawo mata Miji na gari." "Amin" Kaka ta amsa a taƙaice tana ɓantarar daushen goronta.

Isa bai bar gidan ba sai da ya cika cikinshi ya yi nat da tuwo a ɗakin Kaka. Duk da rashin daɗin miyar, haka ya daure ya cuccusa. Hakan ba ƙaramin daɗi ya yi musu ba.

  Banda juyi babu abinda yake yi a kan gadon. Filon Leema ya janyo ya rungume shi tsam a ƙirjinsa. Ajiyar zuciya ya sauke, ya lalubi wayarshi da ke gefe ya buɗe saƙon da Leema ta turo masa tun da safe. Har ya fara rubuta mata amsa sai kuma ya goge, ya ajiye wayar a gefe, zuciyarshi cunkushe da tunanin Leema.

Wayarsa ya ƙara ɗauka ya shiga ma'adanar hotuna, hutanansu ya dinga bi yana kallo. Wasu su ba shi dariya, wasu su bashi haushi. Wasu hotunanma bai san lokacin da suka ɗauka ba, tsayawa ya yi yana bin wani hotonta da kallo. Sanye take da ƙananun kaya kanta ba ɗankwali, fuskarta ɗauke da murmushi. Runtse idanunshi ya yi yana tuna lokacin da ya ɗauketa hoton. Ajiyar zuciya ya sauke, ya danna mata kira.

Ƙara biyu ta yi (ringing) ta ɗaga wayar tamkar jira take yi. Muryarta a can ƙasa tace "Assalamu Alaikum"
"Wa'alaikumussalam wa rahmatullah. Ya ki ke?"
"Lafiya" ta amsa a taƙaice. Shiru suka yi na ƴan daƙiƙu sannan yace "Me ki ke yi har yanzu ba ki yi barci ba?"
"Tunaninka" ta furta ba tare da san lokacin da ta yi suɓul da baka ba. Dariyar da ta ji yana yi ce tasa ta daki gefen kanta cike da takaici. Sai da ya natsa sannan yace "Nima gare ni hakan take. Na kasa barci, tunaninki ya mamaye mini kowanne gurbi na zuciyata. Ina kwance rungume da filonki, ina shaƙar daddaɗan ƙamshinki. Kin san me?"
Bai jira amsarta ba ya ɗora "Ji na ke yi ina ma a ce na yi tsuntsuwa na ganni kwance a gefenki, kin san me zan yi idan na..." Da sauri ta katse shi tace "Wai ba ka jin barci? Ni dai barci nake ji, gobe aikin safe zan yi. Asuba ta gari.

SO KO WAHALAWhere stories live. Discover now