SO KO WAHALA? PART 40

32 2 4
                                    

*HAƊAKA WRITER'S ASSO...*

*❤️😭SO KO WAHALA?😭❤️*

                   NA

MARYAM MUHAMMAD SANI (Mum Amnash)

INA TAYA ƊAUKACIN HAUSAWAN DUNIYA MURNA DA ZAGAYOWAR RANAR HAUSA, ALLAH YA ƘARA ƊAUKA HAUSAWA DA HARSHEN HAUSA

17/Almuharram/1443 - 26/8/2021

          4️⃣0️⃣

   Tun Aunty na jiran Inno ta idar da sallah, har ta haƙura ta miƙe tace "Bayin Allah ga katin biki ku bata, Biyu na Matan Yunus ɗayan kuma nata ne, ni sauri na ke tafiya zanyi kwa gaisheta."

Karɓa suka yi suna bin katinan da kallo, ɗaya daga cikinsu tace "Kutt! Na fa Haleemar da da Yaya zai Aura ne, lallai mutanen nan basu da kunya."

Wata Dattijuwa na jin haka tace "Maza ku kirawo min ita Makira, sun gama tsara abinsu tsaf, sun san ƴar su tana da ƙanjamau suka dinga tatsarshi don sun ga maraya ne. Itama Innon b..." Ba shiri Inno ta katse sallarta tace "Ke raba kanki wasa da wuta, don wannan da ta fita ta fiki..."

  Shigowar Aunty tare da yarinyar da ta kirawota ne yasa Inno ta tsuke bakinta tana ƙiƙƙifta ido kamar bazawarar da taci karo da Naira.

Cikin dakin Aunty ta shiga ta zauna tace "Inno ina yini, na shigo kina sallah." Kafin Inno tace wani Abu Dattijuwa Tsahare ta yi farat tace "Ba ita tasa a kirawo ki ba ni ce, tuna miki zanyi dama maganar Lefen Yaro da kuɗin aurenshi da suke hannunku, tunda abun bai yiwu ba sai ku dawo mana da su, ba ƙira babu abinda zai ci gawayi."

Dariya Aunty tayi tace "Ta kwana gidan sauƙi, nima na so nayi muku zancen, saurin da nake yi ne yasa ban muku ba. Kuma so nayi bayan bikin sai a tattauna, amma ba damuwa Inno shiga ki fito mini da kayan garar yarinya. Yanzu zan taro Ƴarƙurƙura, idan muka kai gida sai na zubo muku kayan lefenku na kawo muku."

Kallon kallo a ka fara tsakanin Inno da Tsahare, Aunty bata bi takansu ba ta fice neman mota.

Har ɗaki Mama ta samu Isah tace "Ya kamata ka karɓi katunan nan ka bawa Haleema nata, duk da nesa bata magani amma in ta kama sai ka je Zariya ka kaiwa ƙawarta Zarah ko ƙawayenta Biyu ne suka zo ina laifi?"
Miƙewa ya yi ya ce "Mama ta ya zan tafi har Zariya kai kati, kawai ta ɗau hoto ta tura musu. Nifa Mama kaina ciwo ya ke yi." Ya ƙarasa da marairaicewa, hannunta ta ɗora a goshinsa ta ji da ɗan ɗumi. Miƙewa ta yi ta nufi ɗakinta, magani ta ɗauka har ta nufi ƙofa ta dawo ta dubi Leema tace "Karɓi maganin nan ki kaiwa Mijinki kanshi ne ke ciwo." Ba musu ta karɓa idanunta taf da hawaye ta nufi ɗakin, zurfin da tayi a tunani yasa ko sallama ba tayi ba, ta ɗaga labulen ta shiga.

******************

   Sai kusan ƙarfe biyar Baban Mama ya baro Asibiti wurinsu Dr Zayyad , kai tsaye gida ya so wucewa, amma dole ya biya gidan Inno don tun safe da ya je ya ga alamun damuwa tattare da ita.

A bakin titi ya hango wata kamar Aunty, har ya ɗan gota wurin ya dawo da baya ya ajiye motarshi ya fito. Kamar yanda ya saba cikin girmamawa ya gaisheta "Aunty ina yini?" "Lafiya ƙalau Yunus ya su Hindu?" "Lafiya ƙalau Aunty. Idan tafiya za ki yi ki hau na kaiki" Da ƙyar ta ɗan ƙaƙalo murmushi tace "A'a ƴar ƙurƙura na ke nema tun ɗazu ban samu ba. Ƴan uwanka sunce mu dawo maka da lefenka, to shi ne nake son na kwashe gararta da kayan ɗakinta idan na kai gida sai na ɗebo muku lefenku."

A kiɗime yace "Aunty me yasa baki kirawo ni har gida na zo mun yi magana ba Aunty?" Yaƙe ta ƙara yi tace "Nifa ba wannan ne ya kawo ni ba, katinan cikin jakarta ta nuna masa tace "Abokan Isah ne suka tsiri haɗa dinner, to son a sani irin nawa yasa nace bari na kawowa inno nata da nasu Hindu, tunda mun zama ƴan uwa, na taƙaice maka zance har na kai ƙarshen layinku yarinya ta biyo ni tace ana kirana dole na koma. Ina zuwa wata tsohuwa tayi mini maganar kaya. Yunusa kasan bani da kyau, bana son kana mutuntani kaga kamar ina wulaƙanta ahalinka. Shi yasa ban ja maganar ba na fito neman mota, ina ƙara godewa Allah da Leema bata ɗinka ko ɗaya daga cikin kayanka ba, abubuwan da ta taɓa basu da yawa."

SO KO WAHALAWhere stories live. Discover now