SO KO WAHALA? PART 10

43 2 7
                                    

*HAƊAKA WRITER'S ASSOCIATION*

*❤️😭SO KO WAHALA?😭❤️*

                 NA

MARYAM MUHAMMAD SANI(Mum Amnash)
WATTPAD@mumamnas2486

24/Shauwal/1442   -  4/6/2021

               1️⃣0️⃣

    Cikin nasara su Leema su ka kammala aikin Hajjinsu ,jirgi ya ɗebo su zuwa gida.

Murna a gun ahalinta, abin ba'a cewa komai. Kamar yanda ta yi alƙawari , dawowar ta da sati ɗaya ta kira ma'aikata aka farke rufin gidansu a ka ɗaga gidan.Ta sha yabo ba kaɗan ba, mahaifinsu ya yi ta gorantawa mazan gidan, da kwarzanta Leema. Ita kuwa daɗi kamar me , kafin a kammala aikin ta ɗebo kayanta ta nufo Kano.

    Da murna Aunty ta tare   ta , a ka shigar da kayanta sashin Aunty .

  Baban Mama kuwa tun ranar da Dr Zayyad ya turawa Leema hotunan nan ta waya , ba su sake waya ba. Shi ya sa a na tsegunta masa zuwanta ya hau shiri.

Rawar jikin da Hindu ta ga ya na yi ne ya sa ta kasa haƙuri ta ce "Wai Baban Mama ina za ka ne ka ke wannan saurin? Ko wurin Hadizar za ka je? " A taƙaice ya amsa mata ya ce "Aah wurin Leema zanje".

  Wani irin tuƙuƙi ne ya taso ya tokare mata maƙogaro , amma sai ta daure ta ce "Ka gaisheta, ka gaida su Aunty Insha Allahu nima gobe za ni na mata barka da dawowa." Ta ƙare zancen da miƙa masa turarensa da ya ke ƙoƙarin ɗauka, a kan madubi . Karɓa ya yi ya fesa ya miƙa mata ta ajje.

   Duk yanda ya so har yau ya kasa fahimtar Hindu, shekara har biyar da Aurensu amma idan ta yi wani abin sai dai kawai ya bita da ido. Ya kasa ganewa shin Hindu ta na sonshi ko ba ta sonshi? Tambayar da ta watso masa ce ta sa ya yi firgigit kamar wanda ya tashi daga barci. Murmushi kawai ya mata ,ya fice har da ɗan gudunshi. Murmushin ita ma ta bishi da shi, don ta na mamakin yanda ba ya jin nauyin jikinshi duk da ƙibar da ya ke da ita.

   Tuƙi ya ke amma hankalinsa na kan ta yanda zai tunkari Leema ,   murmushi ya yi tunowa da Dr Zayyad . Wayarsa ya ciro ya kirashi , amma a kashe dole ya haƙura ya ƙarasa. Ya kai kusan minti goma sha biyar a tsaye ,sannan ya yi shahada ya shiga gidan.

    Har ƙasa ya tsugunna ya gaida Mama , da fara'arta ta amsa ta ce "Kwana biyu shiru ba ka leƙowa ko don mutuniyar taka ba ta nan? " Ɗan shafa ƙeyarsa ya yi ya ce " Ba haka ba ne Mama aiki ne ya min yawa ." "To Allah ya taimaka bari na kira ma ita" Ba ta jira amsarsa ba ta yi gaba .

    Tun shigowarsa Leema ta maƙale a bakin ƙofa ta na leƙensa , sosai ya mata kyau , sai dai ya rame sosai tamkar wanda ya shiga tsarin rage ƙiba.

     A ƙofar ɗakin Mama ta tsaya ta ƙwanƙwasa musu ƙofar ,sannan ta juya ta koma cikin gida.

      Sosai ta haɗe rai kamar hadarin gabas , a ɗage ta gaishe shi " Barka ya ka ke ? " Duk da yasan shi mai laifi ne a wurinta ,amma abin ya masa ciwo . Sai da ya yi ƙoƙari sannan ya shanye ɓacin ransa ya ce "Lafiya , da fatan kema kin dawo lafiya? Dama abinda ya kawo ni kenan , bari na tafi don Hindu na jira na."

   Taɓe baki ta yi ,ko me ta tuna kuma sai ta bi bayanshi da sauri, ta tarar har ya isa wurin motarshi .

  Basarwa ya yi kamar bai ganta ba ya buɗe motarshi ya zauna. Jikinta a sanyaye ta ƙarasa jikin motar ,gilashin windon ta ƙwanƙwasa. Buɗewa ya yi ya tsaya ya na kallonta , ɗan kautar da kai gefe ta yi ta ce " A kwai kayan tsarabar Mama ba za ka tsaya ka tafar mata da shi ba? "

Bai ce mata komai ba ya buɗe gefensa , zagayawa ta yi ta zauna ta sha mur sosai. Ƙyalle ya zaro a aljihunsa ya goge gumin da ya tsattsafo masa ,sannan ya fuskanci Leema ya ce "Haleema na ga alamar ba ki yi murna da ganina ba ko? Ba wani abu laifina ne , duk da hakan ya kamata ki tsaya ki nutsu ki gane wani abu. Ni Yunus ban yaudareki ba , tunda tun farko na faɗa miki komai game da matata da kuma Hadiza."

Ajiyar zuciya ya sauke ya  ɗora da "Haleema ban san da wacce ma'ana ki ka fassara yaudara ba, amma a tawa fassarar yaudara na nufin shigowa da ɓoye-ɓoye da munafurci a cikin dukkan wata alaƙa. Yaudara na nufin cin amana ,ta hanyar ɓoye wani abu a zuci ,da bayyana akasinsa a fili. Na yarda na amince idan har kin kamani da ɗaya daga cikin siffofin nan , ki datse alaƙarmu bazan zarge ki ba. Amma ina son ki sani ina sonki ,son da baki bazai iya furta shi ba. Haleema indai har kina so na to ina so don Allah ki taimaka....."

Kukan da ta rushe da shi ne ya sa ya ja bakinshi ya tsuke. Sosai zuciyarshi ta fara zugi da raɗaɗi saboda zubar hawayenta .

Bai san yanda aka yi ba ,kawai ya tsinci kanshi da matsawa gab da ita ya rungumeta tsam a jikinshi. Ita ma ba ta turje ba ta kwanta a kafaɗarshi ta na raira kuka mai ɗaci . Da farko ya rungumeta da nufin lallashi ,amma me ? a hankali ya ji yanayinshi ya na sauyawa . (To hattara dai ƴan mata da samari, masu keɓewa a mota da sunan zance a fesa uban turare a rufe mota ruf . To shaiɗan dai ya na nan ya na jiran ƴar ƙofar da zai tunzuraku . Ya ɗora ku a keken ɓera ,ko da wasa kar ki yarda saurayi ya ce zai rungumeki wannan HARAMUNNE !)

  Duk yanda ya so zameta daga jikinshi ya kasa, don wani irin nauyi jikinshi ya masa , a fili ya furta "Astaghfirullah A'u'zu billahi minasshaiɗanirrajiim" A hankali ya zareta daga  jikinshi ya jinginata da kijerar da ta ke zaune akai . Hannu ya sa ya goge mata hawayen da ke zuba a idonta , cikin kasalalliyar murya ya ce "  Ki yafeni Leema , ki shiga cikin gida gobe na dawo kar a ji kin daɗe . Har ta buɗe ƙofar ya riƙo yatsun hannunta ( HARAMUNNE!) ya ce "Gobe idan Allah ya kaimu zan zo da wuri za mu fita." Kai kawai ta ɗaga masa ta shige gida da sauri.
  Tiris !  ta tsaya ganin Aunty a harabar gidan ta na kai komo.

Hijabin jikinta Aunty ta kalla ,ta ja dogon tsaki ganin yanda ya cukurkuɗe , ƙwafa ta yi ta ja hannunta ƙiii zuwa ɗaki.

**********

     Yau cikin nishaɗi Hindu ta yini , hakan ya sa ta tsiri shara da gyare-gyare . Tas ta share gidanta ta goge , ta salla wanka a ka ɗau ƙwalliya. Ba abinda ba ya son gyara ,duk da baƙa ce ba ƙaramin kyau ta yi ba . Ana kiran sallar magriba ta yi sallarta sannan ta harhaɗa magungunanta da wata ƙawarta ta bata ta shanye duk.

   Tunda ya shigo gidan ya ga canji a ko ina ,bai ƙara rikicewa ba sai da yaga Gayun da Hindun ta sha. Da ƙyar ta lallaɓashi ya yi wanka ya ci abinci sannan su ka ɗunguma ɗakin kwanansu.

   Kayan da ya ajje a gefen gado ta ɗiba don ta zuba a kwandon wanki , ƙamshin da ta ji kayan su na yi ne ya sa gabanta ya yanke ya faɗi ras!  a fili ta ce "Turaren mata kuma? " Tsaki ta ja ta watsa kayan ta koma ta zauna a gefen gadon.

Ta yi tunanin Baban Mama zai tambayeta dalilin sauyawarta, amma sai ta ji shiru sai ma ƙoƙarin canja musu akala da ya ke . Ba ta hanashi ba ,sai ma ta biye mishi su ka lula duniya mai dogon Sango, tun kan tafiya ta yi nisa ya fara sambatu da kiran sunan Leema , tun Hindu ta na kokonto har ta tabbatar Leema ya ke kira. Ƙarfinta ta tattara ta daddage ta hankaɗa shi da ƙarfi.........

*Allah ya gafartawa iyayenmu*

Mum Amnash( Ƴar Faragai)

SO KO WAHALAHikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin