SO KO WAHALA? PAGE 68

48 5 3
                                    

*HAƊAKA WRITER'S ASSOCIATION*

*❤️😭SO KO WAHALA?😭❤️*
                  NA

MARYAM M SANI (Mum Amnash)
*WATTPAD:@mumamnas2486*

27/R-Auwal/1442 - 3/11/2021

                   6️⃣8️⃣

*SAUYIN ZUCIYA*
*Littafin kuɗi ne!*
*It's all about Love, dislike nd romantic story💋*

*Nrml grp 300, Vip grp 600, Speacial grp 1k*

*Duk da kasancewarsa bawanta ne! amman tun kallon farko da tayi masa taji ta tsaneshi bata son ganinshi ko kaɗan! har ta kai ga wata rana ta saka ƙanwarsa mai suna ifteehal ta gyara turakar Gimbiya Abeela! yayarta ce ta samu matsala a kwakwalwarta sanadiyar hatsarin da sukayi, bata iya tuna komai! Ifteehal kwata-kwata bata huce shekara biyu ba! ko da ta dawo ta tarar da Ifteehal ta rufewa Gimbiya Abeela ido da ɗankwalinta suna wasan ɓuya, Gimbiya Abeela ta zame ta faɗi, ganin haka yasa ta kama Ifteehal ta dinga buga kanta da tiles*

*Shin Ifteehal mutuwa za ta yi! ko kuma za ta rayu?*
*Shin Bassim wane yanayin zai shiga idan yaji abun da Gimbiya Afsheen tayi wa ƴar uwarsa?*

*Idan Ifteehal ta mutuwa ya zai yi da rayuwarsa? ba shi da kowa sai ita! yana da shekara takwas ita kuma Ifteehal tana jaririya aka tsincesu a bola, haka suka taso cikin baƙin ciki da ƙuncin rayuwa! yau kuma ace an wayi gari! ƴar uwarsa da ta rage masa ta mutu ta barsa*

*Ana haka Gimbiya Abeela tayi tozali da Bassim! babu abun da bakinta ya fara faɗa sai kiran Bassim da tayi da mijinta! shin ya Gimbiya Afsheen za ta ji al'amarin nan ita da mai martaba tunda halinsu ɗaya dashi*

*Gimbiya Abeela za ta auri Bassim ko kuma ba za ta aureshi ba?*

*Ana wata ga wata! Hajiya Asabe matar ƙanin mai martaba wacce take da yara guda biyu mace da namiji gaba ɗayansu ƴan fancy life ne! babu abun da suka iya sai yawon club dan ita Iklima har mata nema take🥺basu da wani buri irin su ga bayan mai martaba da iyalansa babban ɗanta wanda ya zama kamar bunsuru wajen neman mata take so ta ga an haɗa a matsayin sarki*

*Shin burinsu zai cika kuwa?*
*Gimbiya Afsheen zata ankare da shirinsu kuwa? tunda ita gaba ɗaya hankalinta yana kan Bassim dan bata da wani buri irin ta ga bayansa shi da ƙanwarsa! to gashi ita ma ana so a ga bayanta ita da iyayenta da ƴan uwanta*

*Labari ne mai dogon zango, wanda tsayawa nayi muku bayanin yadda yake to zamu daɗe ban gama ba, idan kuna buƙatar karantashi ku turo kuɗinku ta wannan account number 0017770369, Aisha muhammad Yusuf, Unity bank, sai ku turo shaidarku ta 08122188717 ko kuma hoton kati ta number ban da vtu plss*

________________________

  Ƙarfe Goma ƴan biki suka dawo, gaba ɗaya gidan ya rikice da hayaniya.

Da sauri Hajiya ta tari Mama tace "Ga ƴar ki Fareeda can ta haɗa kaya za ta tafi."

Jikin Mama a sanyaye tace "ina Fareedar?"
"Tana sashen Zuhra na hanata tafiya."

Kasancewar Mama ba ta shiga ɗakin Aunty yasa ta sanar da Hajiya duk abinda ya faru. Ga mamakinta sai Hajiya ta yi murmushi tace "Bar ni da ita." Kai tsaye ta tura ƙofar falon ta shiga. Har ta zauna Fareeda ba ta ko kalli inda take ba, don ta san Hajiya ce kanwa, tunda ita za ta saka mijinta ya danƙaro mata kishiya da tsakar rana.

"Fareeda na ji abinda ya faru, don Mama tana wurin komai ya faru. Sai dai kar ki manta, Mama ba ta sanya baki ko zaƙewa a kan duk abinda ya shafi Kabiru, duk da ba shi ne ɗan da ta haifa na farko ba, yana da yayyi mata har biyu. Wannan dalilin ya sa bata ce komai ba, tunda abu ne a ka yi shi a bainan nasi a wurin biki. Laifi na biyu ɗingurungum na ki ne, saboda ba kya shiga cikin duk wata sabga ta dangi, hakan zai sa ƴaƴanki su zama ware a dangi. Mu kuma a matsayinmu na manya ba za mu lamunci hakan ba. Fareeda ba zan ɓoye miki ba, ba ƙaramun tashin hankali muka shiga ba da muka ji labarin kin ce ke kin gama haihuwa daga Farha da Samha. Lillahi warrasuli mu dai muna son jikoki masu yawa. Kin ga tursasa ki ki haihu shiga hurumin rayuwarki ne. Amma babban dalilin da ya sa zan sa ɗana ya ƙara aure shi ne, saboda mu din ga ganinshi a Kano a kai a kai. Wannan ba laifinki bane, kuma ba wai za mu sa ya ƙara don ƙuntata miki ba ne a'a don masalahar kansa da ta mahaifiyarsa zan sa ya ƙara. Don haka ina shawartar ki da ki saki jikinki, a ƙarasa bikin nan lafiya da ke. Allah ya yi muku albarka, idan kina da ƙorafi ko wata matsalar, kar ki ɗauke ni a matsayin sirika, ko ƙawar sirika ki dube ni a matsayin uwa kawai. Da yardar Allah zan samar miki da mafita."

SO KO WAHALADonde viven las historias. Descúbrelo ahora