SO KO WAHALA? PAGE 44

31 4 7
                                    

*HAƊAKA WRITER'S ASSO...🖊️*

*❤️😭SO KO WAHALA?😭❤️*

               NA

MARYAM MUHAMMAD SANI(Mum Amnash)
*WATTPAD:@mumamnas2486*

25/Al-muharram/1443 - 3/9/2021

          4️⃣4️⃣

Bakinta ta tura gaba fuskarta a haɗe tace "Me ya kawo zancen tozarci? Gaskiya bana son mayar da ƙaramar magana babba." Ta ƙare tana ƙoƙarin zamewa daga jikinshi. Tsam ya ƙara riƙeta duk da yasan hakan zai iya haifar masa da matsala. Ganin babu abinda za ta iya yasa ta sunkuyar da kanta ƙasa. A zuciyarta tana tsinewa mai maganin da ta harhaɗo mata magungunan da suke neman jefata cikin bala'i da abin kunya.

Ɗan sassauta mata riƙon ya yi, yace "Ba za ki bani haƙuri ba?" Murmushin yaƙe ta yi tace "A kan me zan baka haƙuri? To na ji Alhaji Isah Autan Mama Allah ya baka haƙuri. Sai a ƙyaleni na samu na sarara, ko kuwa?" Murmushi ya yi yace "Yanzu kuwa, banda ke ma wacce Amarya ce take yin faɗa da Angonta a daren farko?" Bata bashi amsa ba, ta miƙe ta nufi cikin ɗakinta ta shiga banɗaki, sabon magogin baki ta gani(brush) ta ɗauka ta wanke bakinta ta fito. Jakar kayanta ta buɗe, ganin bata ga abinda ta ke so ba, yasa ta zazzage komai a kan gadon, ƙwafa tayi tana jujjuya sabuwar pink ɗin rigar baccin da Zarah ta sako mata, ƴar ɓingil bata da wani tsaho. Cike da takaici ta yi ƙwafa ta  ɗau rigar da fallen zani ta shiga banɗaki.

Wayarsa ya ɗauka ya nufi ɗakin, kayan da ta baza a kan gadon ya ture gefe ya kwanta rigingine.

  Saƙonnin fatan alkhairi ya ke bi yana godiya, buɗe ƙofar banɗakin da tayi ne yasa ya ɗaga kanshi, a hankali ya sunkuyar da kanshi wani irin yanayi na game masa ilahirin jikinsa, tun daga ɗan yatsan ƙafarshi har zuwa ƙwaƙwalwarshi. Runtse idanunshi ya yi gam, ya mirgina ya koma rubda ciki.

A gefen gadon ta zauna ta ɗan shasshafa turarenta, sannan ta kwashe kayan ta dannasu a jakar ba tare da ta ninke ba. Ta na gamawa ta kwanta a gefensa, ta juya baya.

Mamaki abin ya bashi, ko da yake mene abin mamaki kai da bata ɗauke ka a matsayin Miji ba, taya ya za ta ji kunyarka ko nauyinka? Miƙewa zaune ya yi, yana bin bayanta da kallo. Abubuwa da dama da suka faru na dawo masa tamkar a lokacin suke guda na, wani abin ya yi dariya, wani ya ji haushi.

Wayarshi ya duba kusan ƙarfe ɗaya da rabi, addu'o'in bacci ya tofa mata daga inda ya ke zaune, sannan ya kwanta  abubuwa da dama na kai komo a zuciyarshi.

Ko cikakken barcin awa biyu bai yi ba ya farka, miƙewa ya yi ya ɗauro alwala ya tayar da sallah. Sai da yayi raka'a takwas sannan ya yi shafa'i da wutiri Hannayensa ya ɗaga sama ya fara Addu'a, bayan ya yiwa Annabi salati "Ya Arhamarrahimin, Ya Arhamarrahimin, Ya Arhamarrahimin Allah ka sanya albarka a aurenmu, Ya Allah ka karkatar da zuciyoyinmu zuwa ga ƙaunar juna. Ya Ubangiji ka sanya ƙaunata a zuciyar Haleema, Allah ka ya ye mata duk damuwar da ke cikin ruhunta. Ya Allah kasa wannan canjin da ta samu ya zamto mafi alkhairi a gareta. Ya Allah kai ka ce mu roƙe ka za ka amsa mana, ya Allah kar ka bani ikon kunyata Mahaifiyata, Allah yasa Iyayenmu su yi alfahari da wannan auren, Allah ya wanzar da farin ciki a dukkan gidajen auren Musulmi. Allah ka bani ikon kyautatawa Matata da dukkan ƙarfi na da lafiyar jikina, da dukiyata da komai nawa. Ya Ubangiji na karɓi kyautar da ka yi mini, ina da tabbacin hakan zai zamo alkhairi a garemu baki ɗaya, ya Allah..."

Jin kamar shessheƙar kuka yasa ya juya, da sauri ya goge hawayen fuskarshi, sannan ya miƙe ya kunna fitilar ɗakin.

A gefen gadon ya tsugunna daidai saitin fuskarta, a hankali ya kira sunanta "Haleema" ba ta amsa ba amma ta ɗan buɗe idonta kaɗan, juyarda fuskarshi ya yi jiki a sanyaye yace "Me ya ke damunki?" A maimakon ta bashi amsa sai kawai ta rushe da kuka. Miƙewa ya yi ya zauna a gefen gadon, hannunta ya kama yace "Me ya ke damunki? Ki sanar da ni don Allah." "Muryarta a can ƙasa tace "Cikina ne ya ke ciwo" "Ayya sannu kin ji, Allah ya sauwaƙe, nafi tunanin yunwa ki ke ji bari na samo miki abinda za ki ci." Girgiza masa kai tayi ta maƙe kafaɗarta, iska ya furzar daga bakinshi yace "To ko shagwaɓa ce?" Da sauri ta saki hannunshi ta juya masa baya, murmushi ya yi a zuciyarsa yace lallai na yarda mace duk girmanta yarinya ce a wurin Namiji, kuma ba a rabasu da shagwaɓa. Ajiyar zuciya ya sauke, jin kiraye kirayen sallar Asuba, banɗaki ya nufa ya ɗoro alwala.

SO KO WAHALAHikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin