SO KO WAHALA? PART 7

44 4 4
                                    

*HAƊAKA WRITER'S ASSOCIATION*

*❤️😭SO KO WAHALA?😭❤️*

               NA

MARYAM MUHAMMAD SANI(Mum Amnash)
WATTPAD@mumamnas2486

             ▶️7️⃣

14/Shauwal/1442 - 26/5/2021

         Cikin nuna ko in kula ta ce "Hadizan Hajiya mana, da ka auro min bare ai gara wacce na sani kuma na saba da ita. Ko ba haka ba?"

  "Hum Hind ki na ba ni mamaki wani lokacin, amman tunda kin ce haka shikenan . Allah ya sa Hadizan ta yarda don bazan barki ki tafi ba sai an yi bikin ko kuma an sa rana."

   Ga mamakinsa sai ya ga ko a jikinta ,miƙewa ma ta yi ta cigaba da sabgoginta.

    Kamar yanda ya faɗa sati biyu da yin maganar ya je gidansu Hadiza ya sanar da ita ya na sonta. Ga mamakinshi ba wani jan aji ,ko nuna alamun fargaba ta amsa masa . Su ka yi musayar lambar waya ya tafi. Tun daga ranar su ka soma yin waya sama-sama tun ba  ya ƙaunarta har ya fara son ta a shi ma a hankali.

   Duk abinda ke faruwa Hindu ta sani, amma ta ƙudurce a zuciyarta ba za ta taɓa yin maganar da Hajiya ko ƴaƴanta ba . Idan sun ma ta zancen za ta nuna goyon bayanta ,idan su ka ɓoye mata sai ta san yanda za ta ɓullowa al'amarin.

    Hadiza kuwa daɗi ne ya ƙumeta, don ta yi boko har ta gaji . Ba aure ba aiki shi yasa ma ta ɗora master's . Yanzu ko da Allah ya kawo mata Baban Mama ya za'ayi ta yi sake ta rasa. Babban abin jin daɗin tasan sirrin komai na matarshi , a ganinta hakan ne zai ba ta damar ƙwace shi daga hannunta.

    Ko wata ba'a rufa ba Hindu ta gane ta yi babban kuskure . Don ta na lura a wasu lokutan idan ta shiga gidan Hajiya ,sai su dinga zunɗenta da yi mata dariya da zarar ta tambaya sai su wayance. Ita kanta Hadizar wani gani-gani ta ke mata ,duk da ƙoƙarin basajar da ta ke yi.

   A hankali Hindu ta fara zare jikinta daga gidan Hajiya. Da kansu su ka tsargu , sai kuma rashin mutunci ya fara biyo baya . Idan Baban Mama ya yi tafiya ta aika su zo tayin kwana, sai Hajiiya ta ce Babansu ya hana su. Dole ta haƙura ta koma rayuwarta ita kaɗai sai ƴarta tilo. Wannan ne musabbabin rigimarsu da gidansu Hajiya da Hadizar kanta.

   Idan kuma zaman ya isheta sai ta tafi gidan sirikarta ta yini ,sannan ta dawo gidanta.

Duk ƙoƙarinta na dakatar da Baban Mama ta kasa , dole ta haƙura ta miƙawa Allah lamuranta ba ki ɗaya.

BAYAN WATA TAKWAS

    Baban Mama ya turo magabatansa don a tsaida maganar auren su da Hadiza. Amma sai mahaifinta ya yi fur ya ce bai san zance ba ai ana barin halas don kunya. Da magabatan su ka matsa sai ya ce su tafi idan ya yi shawara zai kira su.

    Sosai ran Baban Mama bai yi daɗi ba,amman bai wani matsa ba . Ya na dai zuba ido ya ji, wane hukuncin Baban Hadizar zai yanke. Tun ya na jira ,har ya fitar da rai don a ƙalla an ɗebi wata takwas ba wani batu daga Baban. Da ya tuntuɓi Inno da maganar, sai tace masa ko tsohon mayene shi ya kamata ya bar maganar kawai. Tun daga ranar, tsakaninsa da Hadiza sai sama-sama ko a waya.

  A wannan tsakanin ne ya haɗu da Leema kuma kamar yanda ya faɗa mata a baya, ba wai sonta ya ke ba kawai dai ya ji jininsu ya haɗu ne.

   Duk yanda Baban Mama ya lallashi Hindu ta kafe ita tana son zuwa Kamaru . Da ya ga ba dama tilas ya haɗa mata kayan tafiya ta tafi. 

    **************

  Duk yanda Baban Mama ya so ƙaryata zuciyarshi abin ya ci tura. Dole ya yanke kawai zai tunkari Leema ya sanar da ita halin da ya ke ciki .

   A ranar ya shirya ya sanya sababbin kayansa tsaf ya fesa turare ya ja motarshi ya je gidan. A waya ya kirata , kusan zabura ta yi ta figi hijabi za ta fita, kamar jiranshi ta ke.

Har ta kai bakin ƙofa Aunty ta ce "Ke wai me ya ke damunki? Ina za ki je ki ke wannan saurin?" Gefen kujera ta zauna ta ce "Aunty Baban Mama ne ya zo" Kasa magana Aunty ta yi don takaici, ta shige ɗaki ta barta a nan.  Ɗan jim ta yi sannan ta fice da sauri .

   Ɗan waige-waige ta fara sai kuma ta hangi motarshi daga can gaba kaɗan da gidan. Ƙarasawa ta yi ta ƙwanƙwasa glass ɗin ,buɗe mata mazaunin gefansa ya yi. Ba wani ɗar ta buɗe ta shiga , don  sun saba fita dama a motarshi.(Wannan babban kuskure ne a shiga motar saurayi a rufe. Da sunan ZANCE  komai zai iya faruwa Allah ya datar da mu. Ameen)

     Sai da ta nutsu sannan ta ɗan muskuta, ya zama tana kallonshi ta ce "Baban Mama ina yini?" "Lafiya ƙalau Haleematu, ya mutan gidan?" A hankali ta amsa ta ce "Su na nan ƙalau. Me yasa yau baka shiga ciki ba ka tsaya a nan?" Ajiyar zuciya ya sauke ya ce "Haka kawai na ke jin gara dai , ki fito waje. Haleema akwai muhimmiyar maganar da na ke son yi da ke . A gaskiya Ina son ki, ina ƙaunarki" "Ni !" ta faɗa a firgice wani daɗi na tsirga mata har tsakiyar kanta. Amma sai ta sunkuyar da kanta don kar yai saurin gano halin da ta shiga.

  Juyowa ya yi sosai ya na dubanta ya ce "Leema na fara sonki tun bayan rasuwar Haseen, amma sai na ɗauka tausayi ne. A yanzu na tabbatar sonki na ke ,kuma so ba na wasa ba. Kin sanni ,kin san halina, kinsan gidanmu ,kinsan komai nawa mai zai hana mu yi aurenmu a kurkusa. "
 
    Baban Mama kenan wannan wace irin soyayya ce? Ba ma wannan ba ita Hadiza ya za ka yi da ita? Kai ai aure ba abin wasa ba ne ballantana ka ce ka na son wannan gobe ka canza. Gaba ɗaya hakan bai dace da kai ba, a matsayinka na kamili kuma magidanci." Hawaye ne ya ziraro mata, don har zuciyarta ta ji ta na son Baban Mama. Cikin dabara ta goge ba tare da ya gani ba.

Cikinn sanyin murya ya ce "Leema ban san me zance miki ki gane abinda na ke nufi ba. Ban san wacce tambayar zan amsa miki ba, amma bari na fara da maganar Hadiza, don ta  na da muhimmanci sosai. A wancan lokacin , ta waya mukayi maganar Hadiza da ke. Maganarki da ki ka ce idan na auri Hadiza auren cin amana za mu yi . Da maganar da Inno tamin , shi ya sa na ajje maganar Hadiza a gefe. Kuma...."

  Ranta a haɗe ta ce " Tsaya-tsaya to idan kuma Mahaifin Hadizar ya tuntuɓeka mai za ka ce masa? "
"Ba ma zai tuntuɓa ba , kusan wata tara fa da yin waccan maganar kawai ki sa a ranki ta wuce. Sannan maganar ni magidanci ne hum, in ana cin ɓaure ba'a tona cikinsa. A bar kaza cikin gashinta kawai, amman ke ma ba yarinya ba ce ,nasan kin san komai ." Iska ya furzar daga bakinshi ya jingina da bayan motar , a hankali ya ji yanayinsa ya na sauyawa . Ƙamshin turarenta mai shegen daɗi da ya haɗu da nasa ya bada wani ni'imtaccen  ƙamshi ne ya sa ya ji duk kansa ya fara masa zafi . Hannu ya sa ya rage AC .

   Hankalinsa ya maida kanta , kamar yanda ya ke da ,ita ma a jingine ta ke , idanuwanta a rufe tana murza zoben azirfar da ke hannunta. Cikin fitar haiyaci ya miƙa hannunsa ya fara murza zoben na ta da ƴan yatsunta a hankali."
  
  Cikeda masifa Aunty ta ce "Mama wallahi babu abinda zai hana na ci ƙaniyar yarinyar nan ,don tsabar ta raina mana hankali yau ba ma a gidannan su ke zancen ba. Wallahi ba za ta ja mana magana a dangi ba, a dinga cewa don ba ke kika haifeta ba mun bar ta ta na yanda ta ke so." Cikin sanyin murya Mama ta ce ki yi haƙuri, da ta shigo zan mata faɗa. Ba daɗi kar Alhaji Musa ya ji kina faɗace-faɗacen nan." "Shi kenan"  ta shige ɓangarenta don yau mijinsu a gidanta ya ke.

ALLAH YA GAFARTAWA IYAYENMU

MUM AMNASH🖊️

SO KO WAHALAKde žijí příběhy. Začni objevovat