SO KO WAHALA? PAGE 71

24 3 0
                                    

https://chat.whatsapp.com/EiQ3qtht0QSLRElOcqt3CP

*HAƊAKA WRITER'S ASSO...🖊️*

*❤️😭SO KO WAHALA?😭❤️*

              NA

MARYAM M SANI (Mum Amnash)
WATTPAD:@mumamnas3486

12/R-Thani/1443 - 18/11/2012

              7️⃣1️⃣

Tashin hankali da ba a saka masa rana, tuni Kaka ta fice daga hayyacinta. Tsoro ya bayyana miraran a saman fuskarta, ta kasa zaune ta kasa tsugunne.

Ganin haka yasa Isa yace "Ni fa tsokanarki nake yi. Wallahi wannan sojan da ki ka gani abokina ne, tare muks yi firamare da sakandare. Nima rabon da na ganshi an daɗe sosai, shi yasa ki ka ga mun tsaya mun gaisa."

"Uhm!" Kawai Kaks ta furta daga nan ta ƙunshe bakinta gam.

"Kaka ni tashi zan yi na tafi gida, gobe ina da gyara a Kasuwa da kwantan aiki. Idan ba ki yarda da bayanaina ba, da lambar Yaya Kabiru a cikin wayar Salaha ki kira ki tambaye shi. Shi ya turo kuɗi na siya mata waya da waɗannan kayayyakin." Ya ƙare yana  nunawa Kaka ledar dake gabanshi.

"An gode." Ta furta a taƙaice. Ganin kamar ya takurasu yasa ya miƙe, fuskarshi kadaran kadahan ya dubi Salaha dake gefe, ɗinkin hularta kawai take hankali kwance, tana sauraron duk maganganun da suke yi.

"Karɓi wannan wayar taki ce Yaya Kabiru yace na kawo miki. Saƙo maƙoƙo na isar, na adana miki lambarshi a ciki nasa Yaya K."

Idanunta a warwaje tace "Amma kasan Baba..." Hannunshi ya ɗaga ya dakatar da ita, sannan yace "Baba na fara nunawa kafin na kawo miki." Bai tsaya sauraran mai za tace ba ya ajiye wayar da kwalinta a kan ledar kayan ya fice. Kai tsaye bai san mai yake ji ba, haushi ne ko takaici? Yana zuwa gida ya kwanta zuciyarshi cike da saƙe-saƙe.


********

Sai da ya yi Sallar Isha'i sannan ya shiga gidan, tun daga yanayin tarbar da ta yi masa da ya dawo daga ofis yake cike da mamakinta, amma sai ya kanne bai ce komai ba.

Duk da Fareeda miskila ce ba safai ake jin damuwarta ba, amma yau damuwarta a fili take. Fuskarta ta gama fallasa sirrin asirin dake zuciyarta.

Ganin yanda yake bin ta da kallo ne yasa ta ɗan ƙaƙalo murmushi tace "Ya dai?"
"Babu komai." Ya furta ya nemi wuri ya zauna a ɗaya daga cikin luntsuma-luntsuman kujerun da suka yi wa falon ƙawanya.

"Na kawo maka abincinka nan?"

"Eh" ya furta a taƙaice yana ƙara nazarinta. Komai a sanyaye take yi tamkar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki.

Bai wani ci abincin mai yawa ba ya tattare kwanukan gefe, cike da matsuwar su shiga ɗaki ya ji damuwarta. Yasan halinta sarai, idan bai tambaya ba bai zama lallai ta sanar ds shi ba.

"Ina su Samha?" Ya tambayeta yana duban hanyar ɗakunan kwanansu.

"Tun da suka shiga Sallar Isha'i ba su fito ba. Na fi tunani aikin gidansu (Home work) suke yi, bari na kira su."

Kai tsaye ta miƙe ta nufi ɗakin, kamar yanda ta zata aikin suke yi. Fuskarta da ɗan murmushi tace "Dadinku ya dawo daga Masallaci tun ɗazu bai ganku ba, yana nemanku." Da sauri suka miƙe suka bi bayanta zuwa Babban falon gidan.

Sai da suka russuna suka gaishesa ya amsa sannan ya dubesu yace "Yau ba zaman hira kenan?"
"Dadi an kusa fara exam (jarrabawa), shi yasa muke ɗan yin bita." Farha ta furta tana wasa da ƙasan rigarta.

"Hakan ya yi kyau. Allah ya bada sa'a da nasara. Amma yanzu ku tafi ku kwanta da safe kwa ɗora kafin lokacin Makaranta. Ƙwaƙwalwa na buƙatar hutu, kun gaji da yawa a tafi a kwanta."

SO KO WAHALAWhere stories live. Discover now