KgEpisode seven
Tashare hawayenta sannan tatasu tace
"Nagode hajia dakika ban wannan damar "general ne yace
"Hajia shigo ciki akawo maki ruwa kisha kici abinci zansa koh sajan
rosel ne yamaida ki "Shiga ciki tayi takushi sannan yasa sajan rosel yamaidata
Cikin Dare
General ne yashigo part din salame tana zaune tana ma raheena wasa yayi sallama ta amsa tace
"Husby na mai ya kawoka tsohon Daren nan 12:00 harta yifa nasan dai duk yarda akayi babbar maganace takawoka "yace"Haka ne wata magana dama nakeso yida ke inason yarinyar nan ayi sunan bikinta ayanka mata rago yanda duk akeyiwa diyana "saitace
"Tab ai husby na wannan babbar magana ce kana ganin hajia bazatai fada ba gashi dakyar tabari kuma kasan halin asmau sarai dai koh"yace
"Karki damu da hajia tayarda da komi itadai kawai shine tace baxata taba daukarta jikantaba .batun asmau dakike magana kyaleta bazata iya komii ba tunda hajia tayarda yanzu da zance "tace"Tohh alhaji shikenan saidai yanda za'agayawa mutane na haihu"yace
"Aff Abu mai sauki kice ma kannan ki da sauran abokkan arziki kice kin haihu. Idan sukasa tambaya kice Dubai kika haihu""Tace tohh husby angama shikenan yaushe za'ai suna "yace
"Yau juma'a Dan haka wata juma'a za'ai suna"tace"Toh Allah yakaimu "
RANAR ALHAMIS
Yan uwan hajia salame ne duk sun hallara gidan gidansu hajia salame su goma ne mata biyar maza biyar babarsu itakaidai ce babansu ya aura .mata sune; balkisu wadda kezama abuja, sai hafsatu mai zama kaduna, sai zakkyya a kano take sure, sai kuma hajia salame,sai kuma yar auta aminatu a garin kano itama tame aure.Zaune suke su biyar da sauran yan uwan mamarta da babanta take away ne juices daban da ban sai snaks d.s da naman kaza suna kullawa a wata jika mai kyau gaske ana jefawa ana ajewa anrubuta welcome to the world raheena general... Curtsey :family of karakai haka ake kiran familynsu salame
Ran suna
Muatane ne sai shigowa suke antaro sosai kowa yazauna sai surutu kakeji kowa nacin masa da miyar allayahu, wasu koma pride rice sukeci wasu alala, rikeda kunun aya da zubu uwar bikice tafito tae kyau sosai lace ne hadadde mai kyau Tasha sarkar gold Tasha makeup
Rike takeda raheena a hannuMai Hoto ne yazu yadauke su hoto ansha hutuna kamar me. Itaku asmau koh fitowa batae ba, bayan angama buki waleema aka shirya kaya tatta masu wa'azi sukazu akayi aka gama kowa yaci yakoshi bawanda zai ce baici ba kowa yacika ciki dam gakuma jikka cukeda kaya anwatse gida duk ya yakuce almajirai sukazu suka share koh ina
Bayan shekara uku
Wata yarinya ce nagani sai da iduna ya rikice wani zufa ne yafara ketoh man ganin yarinyar Dan saida ruhin jikina yafita saboda jin tsoro dasauri nadau makyar kyata ina adu' ui ina cewa wa inahu min sulaimanu wainahu bismalahi rahmanu raheem, lahaula wala kuwata illah billahi aliyu azeem
Tsananin kyan yarinyar baza'ace na mutumneba shiyasa da gashin kanta baki kirin wuluk gashi yanaja harga bayanta oh my God Allah yayi hallita kwayar idunta fari tas kamar farin alli Da manya manyan idanunta kamar gold ga girarta tsa yayya baka wuluk bakinta koh pink ne idan ba mutum yataba ba zaice jambaki ne tasa ai ita vaseline dai xata sa bakinta bai bukatar jambaki amata rolling din kanta don kanta bai kitsu fatar jikinta koh kamar zabya kadan takai zabya kamar madara haka fatarta take gatada laushi tasa kaya blue nd pink Riga da wando jeans yarinyar bazata wuce 3years baTsaye naganta bakin kofar daki wasu yarane suke ta wasa tana kallonsu zuwa tai wurin su daniyar wasa sai naga gudar ta dungujeta ta tureta wadda baxata wuce 4 years tafadi (sai sannan nayarda mutumce ba jinn ba amma Allah yayi hallita masha allahu barakallahu) kuka tafara sai wadda ta dungujeta tace
"Shegiya wawiya mubama wasa da irinki tsintacciya wadda batada iyaye wuce kibamu wuri"(kai dama wannan raheena ce kyakkyawa haka) dai 2 dazuwan general tana maganar tana hararen raheena kuka take itaku, dasauri general yafada daki yadauko charjer yadinga bugunta sai ihu take tana karawa tana bazan karaba dasauri asma'u tafito saiga salame itama dasauri asmau taje ta kwace khairat tace
"Haba alhaji metama da zaka dinga dukanta haka kamar jakka"yace
"Haba asmau keyanzu tarbiyarda kika koyawa yaranki kenan na wulakanta mutane zuwafa tayi tana cema raheena shegiya tsintacciya ina tasan hakan inba gurinkiba "tace
"Lalle alhaji yau katabbatar da cewa bare yafi jininka har kazu kana dukanta Akan wannan tsintacciyar tace mata tsintacciya shegiya ai shegiyace dagaske kuma gaskiya tafada....Bata idaba taji mari har biyu masu kyau saida ta juya tace"nika Mara alhaji Akan wannan banzar "yace
"An Mara din inason kisani nima diyana ne dole in hukuntasu in tarbiyantar dasu idan sunyi badaidaiba kuma inason kisani kamar yarda suke diyana haka itama diyace garan kar insake koda wasa naji kin kara furta wannan maganar zan iya sauwa kemaki "tace
"Lahaula ina lilahi lallai sai yau nasan diyar mayu kakawo gidanka a'a dole kam alhaji baka cikin hankalinka nagani tariga da ta mayanceka ta sihirceka "yace
"Kehhh asmau shashan cinnan naka ya isheni haka "salame ce tai magana tace
"Husby na don Allah kayi hankuri ya isa haka kayi hakuri"yace
"Wallahi wifey na hakurina yakusa karewa nagaji da matar nan sabida hajia nake zama daita"Asmau tace
"Toh shegiya almakura.. .
Marinta yakarayi yace"karki kuskura kicemata shegiya data cemaki mi wallahi kedai bakida halii"Kuka ta rushe dashi tafada dakinta tadauko hijab tai zata tafi salame nabata hakuri yace ta kyaleta duk inda zata da kanta zata dawo.
Tana fita ta kwalawa baba Ari kira dasauri yazo tace gidan hajia zai kaita tafada mota basu tsaya koh inaba sai gwarinfa wani gidane nagani madai daici aka bude gate suka shiga yana Parker mota tafito dagudu tana kuka kamar uwarta ta mutu tafada fallon hajia tai sa'a tana fallow tafada ta wani irin kuka kamar wadda za'a ciremata rai hajia ta tsorata sosai ta 'aza wani yaiyi rasuwa koh accident tace"Key asmau lapia munshiga uku yau kibar kukan haka nan mana meyafaro fada man"tace
"Hajia wai dankine yakama khairat da bugu akan dai suna wasa raheena tafadi tace wai khairat ce takadata shinefa ingaya maki hajia bakiga yanda yake dukanta ba saikace jakka akan nayi magana yace sai ya sakini wai nabata masa tarbiyar yara har Mari shida yai mun masu kyau"aikam hajia tatashi ranta a bace tace
"Tab ai wallahi tallahi bazata taba yuyuwa Sam tabdi inaaa wallahi tallahi bazan yarda a dukan man jika akan bare nabarsa yadauketa yanzu kam gaskiya bazan taba yardaba sai tabar gidan"asmau sai dariyar munafurci take da hajia ta waigo ta saitayi fuskar kukah
Hajia tacigaba da cewa
"Ai bazama dole yanzu muje dole sai tabar gidan"dama sanye takeda hijab datagama sallah "Tace"asmau share hawayenki kibar kukah ai indai nina haifeshi toh dole yabi umarnina muje"
Taja hannunta sai mota aka bude masu gate
Comment if u like it
To be continue in episode 8Zarah basheer
YOU ARE READING
AMEERATU RAYHANA(GIMBIYA RAYHANA (
RomanceThis story is about,a princess a beautiful princess named Rayhana she is the daughter of king of Dubai . she was kidnapped by the maids of the house when she was a baby some one in the family gives her ransom money to kidnapped her and take her per...