AMEERATU RAYHANA(GIMBIYA RAYHANA)

314 18 1
                                    

It Episode eleventh

Bayan khairat tashiga dakinsu da shigarta kuka tafashe dashi sosai yarta bintu tazu da gudu tana tambayarta meyafaru dayake yarsu haleema na Cyprus karatun law so subiyu ne nan asmau ce tafito tana "yau koh waya dakan man yar auta "

Takwashe labari kaf taga yamasu itadayake bintu allah yafissheta bata gadi uwarta ba haleema da khairat suka biyu halinta hardai khairat asmau ce tawani irin gurnani kamar zaki tace"chab ai wallahi bazan yardaba yau sai anyi wadda ba'a tabayiba gidanga ai rashin adalcine yaza'ai yasaima bare Abu yaki saima year cikinsa saboda ta mayenceshi chab"bintu tace

"Umma don allah karki tada masifa yanzu ke sanin kanki ne cewa khairat batada kokari batada kunya"asmau tace

"Lalle ke Dan ubanki yanzu kina nufin waccan yar iskar tafini gurinki kenan kin goyi bayansu a'a lalle kema sun magance ki koh to wallahi bazan yarda ba "

Taja hannun khairat sai part din mami da shigarta ta iske raheena, da mami suna bude gifts din tafada kai tsaye taje marin raheena mami tatareta tajanye hannunta saida takusa fadowa mami tace

"Keh asmau tsaya ingaya maki baki isaba fa kice kizu har nan dakina zaki dakan man diya don wallahi yanzu baki isaba wallahi Dana kyaleki banda yanzu"

Asmau tatashi tace"ohh lalle nikika ture nafadi toh wallahi saikinyi Dana sanin abunda kika man wallahi "salame, tace
"Mtss haukar banza ai bari kiji bakida wannan bokan bakida wannan malamin don duk kika ga abunda yasameni toh mukaddari ne data allah baki isa kiman komi ba banza, jaka"tace

"Hhhhhh yeeeeehuhu nikima gayawa banza jaka hmm zakiga makumarki shakuruminki"taja hannun khairat suka wuce.

Safiya tawaye yau takasance ranar lahadi dine kwance take cikin blanket rawan dari take sosai mairo ce nanny dinta ta shigo
Dakin tana gyare gyare saita ga yanda take taje tatallafo ta tace"yarta miyasameki kike rawan dari"kasa magana tayi rawan dari, hakoranta  keyi da Sauri taje tagayo ma mami dagudu mami tafado taga halinda take ciki dasauri takira general ba'afi minti uku ba saiga shi yace tadauko hijab akaita hospital

Ba'atsaya daita ko inaba sai DIAGNOSTIC CENTRES HEALTHCARE wadda take gwarinpa da isarsu aka kaita wani daki maidauki da bed biyu aciki da shigarsu akasa mata driff duk hankakin su yatashi sai ga doctor yafito yace subiyushi suka bishi office dinshi suka zauna yace"don't worry she will be alright "duk a turanci yake tacigaba dacewa "bawani ciwobane kawai typhoid ce kedamunta kuma zataji sauki nanda kwana uku zamu sallameta

General yama doc godia suka wuce dakin da aka kwatarda ita kwance take alamon tasha alururi abba ne yace zai koma gida zai gayawa mairo tashiryo kayenda ake bukata sai baba ari yakawota tace masa"tohh shike nan alhaji "

Bayan 2hours saiga mairo rikeda kayan tea da kayan sawa

Bayan kwana guda
Doctor ne yazu dubata don harta bude ido yanzu doc yamata yajiki ta amsa sannan yagaida mami yawuce bayan fitarsa ne mami tace ita zata zataje massalaci tai sallah tafita 

Wasu securities ne nagani sunshigo hospital din su 20 sai wata mata mai kyau sai kukah take wani yaro nagani wanda bazai wuce 14 years ba kwance andaukosa  dakin da raheena aka kwantar daita nan aka shiga dashi itakoh raheena bata masan me akeba  anmasa karin ruwa ne doc yafit matar ke tambayar meke damunta yace "am your Excellency ba wani abu kedamunsa ba illa typhoid amma zaiji sauki insha'allah"tace thanks doc

Bayan kwana daya daga raheena sai yaron kadaine cikin dakin raheena na cikin bacci taji mutsin kamar kukah ake kuda Tatashi taduba saitagansa yana ta sheshekar kukah tace" uhmm brother meke damunka"yace

Allura za'ai man nikuma banaso tsoro nakeji "dariya tafashe dashi tace "kai yanzu babba dakai ke tsoron allura koni bana tsoronta"

Yace"kekikace mekikai kibarjin zafi"
Tace" ai kawai runtse ido zakai nazakaji zafiba trust me "yace tohh
Suna cikin magana saiga nurse yarufe idonsa kamar yadda tace saigashi koh har aka gama bai ji zafin komaiba nurse tatafi raheena tace"buds idonka tatafi ai nagayama bazafi ne daitaba"yace

"Wow I really like you banda friends mata amma kece tafarko sunana raheem junaido "
Tace "nima sunana raheena sheriff haka"haka fa suka dinga fira har yadauko agogonsa maikyau yabata itama haka tadauki zoben azurfarta tabasa tace masa "yazu idan katafi bazamu sake ganin junaba yace"a'ah mana kinada iPad tace"ehh"

Yace"ok mudinga magana a whatsapp "tace"kaii baruwana mami zata dakan yace kinga zaki fa yine aboye "tace toh ai bands sim "yace"kisaya mama"

Aka haka alaka tashiga tsakaninsu ta kwana biyu sosai sanda zatabar asaibitin saida sukayi alkawarin kada su mance juna koma duk abunda suke da friendship dinsu cikin iyayensu bawanda yasani koda takuma gida aboye tasai sim dayake yabata numbersa kullum sai sunyi fira tafada kaf abunda yafaro yau shima haka duk abunda yafaro dasu sai sungayawa juna komi yasani gameda itama haka yatura mata pics dinai itama tatura masa abu guda bai gayamata ba shine shidan president neba wata soyayya tashiga tsakaninsu amma duk a friend's raheem ayanzu shi tun yana karami yayi deciding ba maccen da zaiso sai ita don a yanzu sonta yashige shi sosai yasan duk halinda take ciki gidansu

Bayan shekara biyu da friendship dinsu

Raheena ce tafito daga daki suna chat dashi takara kyau ita a kullum kara kyau take kamar farin wata tana fitowa tafada jikin mami tana zuba shagwaba mami Tace "kinga bari natashi naje nai sallah kema maza kije ki aje iPhone seven dinan kece kullum waya chatting haba tace tohh mami.

Bayan ta ida tadauki iPhone dinta kiranta yayi tadauka tareda cewa "Besty friend dina yanzu tafiyarka zakai kabarni "yace

"Haba my besty kinsan badan dad da mom sun tilasta minba dabanzanyi tafiyar nan abroad ba I promise to you bazan taba mantawa dakeba "tace

"Toh naji allah yatsare "tayi hanging off ita dai raheena yanzu tanada shekara 13years aduniya tana jss 3 ayanzu

Bayan wata bakwai,tunda raheem yatafi yadaina kiranta baduriyarsa ba labarinsa duk tabi tarame ayanzu dai tasasa agefe don karatu take sosai donata son taiwasa da karatunta akan hakan

Zarah basheer

AMEERATU RAYHANA(GIMBIYA RAYHANA (Where stories live. Discover now