part 1

780 29 2
                                    

*Typing*

*🤱MAHAIFIYATA*....🤱

_Na_

*🌹Ameena first lady*🌹

_page1⃣ to 2⃣_

Tafiya suke a hankali kamar bazasu taka kasaba amma kana kallon su kasan suna tareda nutsuwa kowacce rike take da littafi a hannunta tabbacin daga daukar lecture suke.
Khadija yakamata musamu waje me iska mu zauna mu huta gashi ke ko abinci ma bakici ba
Kallona naikai gun wacce aka Kira da Khadija,farace mai matsakaicin tsayi idanunta farare karr sai dogon hanci da karamin baki,suffar fulani sak ya bayyana a tareda da ita Koda ban tambaya.
Khadija magana fa nakeyi kinyi shiru kuma kinki tsayawa nifa gaskiya nagaji da wannan shirun naki yakamata ace kin rage yawan tunani ace mutum Yana tafiya ma bazai daina tunani ba,nikam nagaji da tafiya idan kinga dama ki taho muje mu zauna!
Tunda ta fara maganar ko uffan Khadija bata tanka mata ba har tagama mitar tata ta nufi wajan wasu kujeru ta zauna a kasan wata bishiya" ganin haka yasa Khadijan ta bi bayanta suka zauna.
Shiru sukayi na tsawon minti biyar can dai Khadija tafara goge hawayen da suka zubo batareda ta bari kawar tata ta gani ba, Zainab na rasa laifin da nayiwa MAHAIFIYATA takasa yafemin nabi duk hanyar dazan bi amma nakasa samun amsar irin laifin danayi mata na tsawon rayuwata "kuka ne yaci karfinta hakan yasa tayi shiru da zancan nata.
Zainab tarasa me zata cewa kawar tata shiyasa ta kyaleta tayi kukan me isar ta Dan ko itace a wannan halin abin zatayi gani take saima yafi haka.
Kusan 3minutes sannan Zainab tayi karfin halin cewa.
Khadija yakamata zuwa yanzu ace kin saba da halin Mahaifiyar ki kinyi hakuri watarana sai labari kiyi hakuri kadaina kukan haka indai baso kike nima zuciyata ta karaya ba.
Share hawayen tayi sannan ta Mike tace shikenan Zainab nizan tafi gida saboda banci komaiba kuma kinsan bazan iya cin na capteria ba.
To amma wazai kaiki gida tunda naga driver naki baizo ba" kibari kawai mu tafi tare sai Bala yayi dropping dinki mu wuce.
Mikewa itama tayi suka jera suna hirar su.


*************
A kofar gate din gidan suka tsaya"saura ki bari gobe nayita jiranki a school cewar Zainab.
A'a bazaki jiraba kawata zanzo da wuri amma kicewa mama tabaki dambun Naman nan irin na rannan ki tahomin dashi Dan Allah.
Zainab tace to zan fada mata uwar kwadayi.
Khadija ta fita tana dariya Dan tasan halin mutuniyar tata akwai korafin tsiya yanzu saitaitayin tsokane tsokenan zance......
"Kamar kullum yauma a gajiye tashiga gida"gabanta ne ya fadi ganin mommy a palour; haka tashiga da sallama duk da tasan ba amsa mata zatayi ba. "Sannu da gida mommy"tayi wucewar ta dakinta.
Tana shiga ta fada saman bed ta rushe da kuka bakin ciki shin wannan wacce irin rayuwace ace kaida Mahaifiyar ka amma Kamar abokan gaba,kwatakwata bata samun kulawar da uwa take bawa danta hasalima ko magana ta fatar baki bata hadasu.
"Shin laifi tayi mata kokuwa kiyayya ce" tarasa dalilin wannan mummunar kiyayyar da take fuskanta daga mahaifiyar tata"
Kuka tayi harta godewa Allah sannan ta tashi ta fada wanka a bathroom din dake makale a bedroom din nata..

**************
_WACECE KHADIJA_

Alhaji Ahmad Sada shine sunan mahaifin khadeeja Dan asalin kauyen walarbe ne dake cikin garin garo a jahar kano fulanine na daji duka kauyen gida uku ne manya kowanne gida Yana waje waje acikin mahaifin Alhaji Ahmad me suna ibrahim suna kiranshi da AWU tsohone shine babba a rugar tasu shiyasa suke girmama shi duka rugar yazama shine babba a rugar tasu tareda matar sa me suna Aisha suke kiranta da A'i dansu guda daya a duniya shine Ahmad tunda Ahmad ya girma yakai shekara 8 a duniya shine suka maida hannun kanwar A'i da take aure a cikin birnin Kano a nan yayi karatun sa har secondary ya karanci business hakan yasa ya tafi makarantar gabada secondary yaci gabada karatun nasa...

*****************
"Amadu kana nufin bazakayi aure ba kome kake nufi"
Awu zanyi aure amma inaso na gama makarantata tukun amma yanzu bazan iya hada karatu da aure ba yanzu,
"Awu yace to shikenan amma dai wannan halin narasa ne ka dauko saidai ka kawo hujja mai kyau Saidai muce Allah yakaimu lokacin.
."Ameen Awu"

***************

_muje zuwa yanzu aka fara_🤝🤝🤝

MAHAIFIYATAWhere stories live. Discover now