🌈 *_kainuwa Writers association_*
https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation
*_🤱 MAHAIFIYATA 🤱_*
_by_📚✍
*_🌹 Ameena first lady🌹_*
*Welcome back home my dear brother*💓
Dedicated to
'''shafi'u Musa {shafam}'''💕💞_page 5⃣5⃣ to 5⃣6⃣_
A'i na mita ta lalubo lambar abban khadija, saida ta kusa katsewa sannan ya daga cikin nutsuwa yayi sallama ganin mahaifiyar shi ce ..
"Dole naji hankalin ka a kwance, matarka ta salwantar min jikata Amma saboda ta shanyeka ka kasa sata ta Nemo maka yarinya...."
Damm gaban Abba ya fadi..
"Nifa bangane abinda kike fada ba, wacce yarinya ce ba'a ganiba A'i"
"Auu, bata fada maka ba kenan, to khadija ce aka nema aka rasa ,kuma wlh na baku nanda safiya ku nemomin jikata idan bahaka ranku saiya baci matuka..."ta katse wayar..
Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, Abba yaketa maimaitawa tunda A'i ta fada Masa gaba daya jijiyoyin jikinshi suka daina aiki....
Karfin halin dauko wayar shi da hanzari inspector na police, bugu biyu aka daga..
"Hello inspector"
"Alhaji Ahmad lafiya Kira da wannan daran"
"A'a ba lafiya yarinya tace ba'a gani ba tun kafin Isha kuma bana kasar Amma da sassafe zanbiyo flight na dawo"
"Subhanallahi, bakomai karka damu Nima kamar yata ce, ka turomin hotunan ta saimu turawa abokan aikin mu na anguwa anguwa may be saceta akayi"..
"Ok zanturo yanzu"
Kashe wayar yayi, mintina kadan ya tura masa picture dinta...
Hankalin kowa yagama tashi musamman Abba da Mommy, a daran Aunty Rahma da Zainab suka je gidan sai baki suke ba mommy Amma Ina hawaye kawai takeyi...
Har Shaheed yaje gida bai shiga part dinsu ba ya wuce nashi Kai tsaye ya kwanta akan cusion .
Lumshe idanuwan shi yayi, Amma fuskar khadija ce kadai a idanuwan shi, ita yake tunawa lokacin da take yimasa magiyar karya cutar da rayuwar ta...."
"Idan nabar khadija, a cikin waccan wajan banyi mata adalci ba fa"..
Wuf ya tashi ya dauki key ya fice.."Shaheed Ina zakaje cikin daran nan"
"Mamee...". Saikuma yayi shiru yakasa magana.
"Yanzu Shaheed bazaka daina wannan mummunar rayuwar taka ta zuwa club ba, duba lokaci kagani 2pm kowa yana hutawa Amma Kai sai yanzu kake fita club,. To wlhy zan fadawa mahaifinka gyara ka koma Spain din gaba daya dazama, dama kaine bakasan zuwa Amma yanzu wlhy baka isa ka ki yarda ba, shashasha kawai". Ta tafi tabar shi...
Tsaye yayi kwakwalwar shi ta tsaya cak..
Jikinshi ba kwari ya koma part dinshi....
Kwanciya yayi a lumshe idanuwan shi.
"Bazan iya yafewa kaina ba idan har wani Abu ya samu khadija bazan iya yafewa kaina ba"
Ya fada Yana dafe kansa...___________________
7:00am jirgin su Abba ya sauka, inspector dinne dakansa yaje dauko sa, gabadaya hankalin sa a tashe sai zufa yakeyi..
"Ka kwantar da hankalin Alhj, dazarar mun ganta zamu sanar dakai kabar wayarka a kunne, mun yada hotunan ta gun ma'aikatan mu sannan ana duba kowacce mota idan zata wuce, idan ma saceta akayi zamu ganota...
Sai yanzu Shaheed ya tuna ya kunna wayarta lokacin dazai fito daga kangon yasan tabbas da anyi tracing number ta za'a gano inda take, sai lokacin yaji hankalin sa yadan kwanta...
Har gida inspector yakai Abba yana kwantar Masa da hankalin shi akan yayi hakuri zasu ganta...
Mommy da Maman su Zainab da Aunty Rahma duk suna zaune a palour Zainab kuma tana daki tana kuka A'i ce take ta faman lallashinta.
"Kiyi hakuri Zainab, za'a ganta Amma wannan kukan bazai rage Miki komai ba Saidai yasa Miki ciwo".."A'i da akwai abinda yafi kuka a yau danayi shi"
"To Allah ya baiya Mana ita, ko a raye koma a mace ne"..
Wani wawan tsalle Zainab tayi ta fashe da saban kuka.
"Idan kuwa gawar khadija aka gani to wlhy Nima bana tunanin zan iya rayuwa, saboda Dan Allah A'i kidaina fadar wannan kalmar mara dadin ji"
A palour ma mommy kukanta yaki tsayawa, tunanin ta idan tarasa khadija zatayi da rayuwar bayan duk duniyar nan babu abinda takeso bayan ita...
Tunanin ta ne ya katse jin sallamar Abba, kowa ya ganshi yasan hankalin sa ba'a kwance yakeba..
Ido suka hada da Mommy ya aika mata da wani irin kallo me tattare da gargadi...
Harkusa da ita ya karaso, cikin kakkausar murya yace.
"Wlhy duk abinda ya samu yata to wlhy bazan kyaleki b.. "
Bai karasa ba yaji karar wayar shi..
Sunan inspector yagani, hannun sa na rawa ya daga Kiran....
"Hello Alhj anganta muna asibitin Ameer city clinic and maternity"
Kafin inspector ya karasa Abba ya fice Yana fadin "gani nan"..
Uncle Abdulmutallib ne yabi bayanshi,
"Yaya anganta"..
"Eh suna asibitin Ameer city clinic and maternity"
Harya juya Yana fadin bari naje na sanar dasu zamu biyo bayanka.
"Abdulmutallib"
"Na'am Yaya"
"Karku zomin da Maryam"Ya fada Yana shigewa motar sa....
_Dan Allah kuyi hakuri da wannan inada uzuri ne pls_👏