🌈 *_kainuwa Writers association_*
https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation
*_🤱MAHAIFIYATA🤱_*
_By_📚✍
*_🌹 Ameena first lady🌹_*
_page 6⃣1⃣ to 6⃣2⃣_
____________________
Daga Mamee har daddy sunyi mamakin abinda Meera ta fada.
Nisawa Daddy yayi yace. "Nasan akwai babban dalilin daya sa Shaheed barin gidan nan, sannan na tabbatar bazai bar Kano ba saboda haka zamuci gabada neman sa fatana Allah yasa kalau yake""Ameen". Suka amsa Masa.....
Tunda aka sallame su daga asibiti tana daki itada Zainab bazaka tantance yanayin da take ciki ba.
Hawaye ne suka zubo mata, Zainab dake gefenta itama hawayen suka zubo mata, a hankali ta hade hannayensu waje daya tafara magana cikin rauni.
"Haba khadija koba Dan halin da kike ciki ba yakamata ki daina zubar da hawayen ki a banza, dole mu dauki kaddara yadda tazo mana, inama bake abin yafaru dake ba wlhy gara abin yafaru a kaina da ganinki cikin wannan halin"...
"A'a Zainab da ke haka ta faru dake bazan iya jurewa ba,. Gara daya faru a kaina,..
Sarkewar sa muryarta tayi ne yasa tayi shiru na wani lokaci.Goge mata hawayen Zainab tashiga yi tana cigabada bata hakuri.
"Zainab bawai Ina kukan abinda akayimin bane, Ina kukan irin cin amanar da Shaheed yayimin, Shaheed ya cuceni ya gama da rayuwata yakafawa rayuwata mummunan tarihi.. "
Tunda tafara maganar Zainab ta tsaya gabanta na tsananta faduwa,. "wanne Shaheed din kike nufi"..?..
"Shaheed nawa, Wanda ya nuna min soyayyar danake tunanin ta gaskiya ce Ashe ta yaudara ce da daukar fansa""Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, meyasa Shaheed zaiyi Mana haka.."
"Ba laifin shi bane, laifi nane Dana yarda da soyayyar shi"
"Idan kuwa hakane yazama Dole su Abba su sani.."..
Da sauri khadija ta riko hannun Zainab.." a'a Zainab karki fadawa kowa dab Allah, inaso kayimin alkawari"
"Shikenan nayi". Zainab tace badab ranta yaso ba.
A palour kuwa duk an hallara kowa yayi shiru mommy, Abba, uncle da Aunty Rahma.
Abbane yace aje a Kira khadijan da Zainab, aunty rahma ce ta tashi ta nufi dakin khadijan.
Khadija a kwance Zainab a zaune a gefenta ta tarar dasu..
"Khadija ku tashu muje palour Abba Yana San ganinki""To Aunty gani nan"
Fitar Aunty Rahma kenan suka biyo bayanta su duka biyun.
Gefen Aunty Rahma ta zauna ita kuma Zainab gefen mommy ta rakube.
Abba yayi gyaran murya yace. "Khadija sakamakon abinda ya faru dake mun shiga tashin hankali mara misaltuwa kema kin sani tunda kinga halin da muka shiga, sannan babban tashin hankali na gaba shine yadda akayi mutane suka San wannan maganar harta Kai da anfara nuna ni a waje, banaso kema ki fara fita ana nuna ku saboda haka na yanke shawarar zaki koma gida uncle dinki da zama har lokacin da mutane zasu manta da komai..."
Tsit kowa yayi har Abba yagama jawabin sa sannan khadija tace ta amince zata koma gidan uncle din nata...
Da haka suka tashi gaba dayansu khadija da Zainab suka nufi dakin su.
Gadonta ta fada kuka Mai tsuma rai takeyi Zainab ma kasa lallashinta tayi saima tayata da tayi.Har dare khadija bata daina kukan ba, Mommy ce ta turo kofar dakin ta shigo jikinta a sanyaye.
Ganin Mommy yasa khadija tashi zaune tana wasa da yatsun hannunta.Har kasa Mommy ta zauna ta kamo hannun khadija cikin nata ta fara magana cikin rauni da alamun nadama.
"Bansan da wanne baki zan nemi yafiyarki ba ta wajab nuna kyama sa tsana dakuma hantarar ki danayi ba, Saidai hakan bai taba rage soyayyar danake Miki ba saina karuwa da takeyi, wlhy khadija Ina sanki kamar yadda kowacce uwa takesan yayanta, duk wani Abu danake Miki sakamakon wani banzan dalili nawa bai taba gusar dake daga Raina ba, amma yanzu nayi kuskure Wanda bazan iya gyara Shiba, Saidai na baki hakuri, kiyu hakuri ki yafe...".
Tun kafin takarasa khadija ta rufe mata baki tana kuka .
"A'a Mommy uwa bata taba neman yafiya a wajan yayanta, a Koda yaushe kallon MAHAIFIYATA nake Miki ban taba canja kallona a gareki ba, nima Mai laifi ce ki yafemin".
"Khadija ban taba kallon ki a Mai lefi ba, kuma inaso daga yau kallona a matsayin mahaifiyarki hakan zai tabbatar min kin manta da komai."
"Dama can kallon MAHAIFIYATA nake Miki Mommy"
Murmushi Mommy tayi sannan ta shafa gefen fuskar ta tace.. "shikenan daughter kiyi addu'a kafin ki kwanta"
"To Mommy Saida safe"Kafin mommy ta fita Saida ta waigo ta kalli khadija na tsawon sakanni sannan ta fice.
Ajiyar zuciya khadija ta saki sannan hawaye ya zubo mata Wanda takasa tantance na farin ciki ne kona bakin ciki...
Zainab kuwa da ta dade da bacci batasan wainar da ake toyawa ba."Mamee ki kwantar da hankalin ki Yaya Shaheed za'a ganshi very soon"
Mamee dake kwance zazzabi ya rufe ta da kyar ta iya magana a hankali. "Meerah nakasa samun sukuni har sai anga Shaheed, babban abinda yake daga min hankali Rashin samun wayar shi ba'a yi""Mamee muci gabada trying number zamu sameshi inshallahu"
Mamee bata kara magana ba sai rufe idanuwanta kawai tayi.
Wayarta ta dauko ta sake trying number cikin sa'a wayar ta shiga da tsakanin murna sosai Meera tace. "Mamee wayar Yaya Shaheed ta shiga Saidai baiyi picking ba"
Jin abinda Meera ta fada yasa Mamee ta tashi ba shiri.
"Kira daddyn ku ki sanar dashi".
Daddy ta Kira ta fada Masa ba bata lokaci ya sanar da yan sanda aka shiga trying location din da wayar take.Ba karamin ramewa Shaheed yayi ba yunwa hade da ciwo su suka sa yayi mummunar rama.
Yana ganin kiran Meera yaki dagawa Dan baya bukatar komawa gidan yanzu har saiya gama hukunta kanshi akan abinda yayiwa khadija.
Location din ya tabbatar wa daddy Shaheed Yana gidan daya mallaka masa.
Yayi zurfi cikin tunanin yaji alamar nocking, muryar daddy yaji Yana Masa magiyar ya bude Masa.
Ba kwari jikinsa yaje ya bude, gaban daddy ya fadi ganin muguwar ramar da dansa yayi.Komawa kujera yayi ya zauna.
Daddy ma yabi bayansa.
"Shaheed wanne irin Abu ne ya sameka kayi irin wannan ramar"Shiru yayi bai bashi amsa ba.
Lallabashi Daddy yayi dakyar ya yarda yabi shi zuwa gida shima Saida ya fada Masa rashin lafiyar Mamee.Dakyar kukan Mamee ya tsaya tunda taga Shaheed dinta.
"Me kakeso mayarda kanka Shaheed, kanaso kamayarda kanka maraya bayan kanada iyaye""Duk ba wannan ba yanzu, Shaheed nagama yanke shawara zaka koma Spain wajan Alhj Kabir da zama, saboda zakafi sakewa tunaninka ya dawo hankalin ka ya kwanta kayi karatu cikin kwanciyar hankali"
"No Dad I can't". Tun shigowar da yayi abinda yace kenan.
"Kayimin alkawari bazaka bijirewa wannan maganar ba Dan Allah Shaheed"
Mamee ta fada tana zubar da hawaye.
"Zanje to Amma pls Mamee stop crying"
Murmushi Mamee tayi Kawai.