part 14

161 9 0
                                    

🌈 *_KAINUWA WRITERS ASSOCIATION_*

'''{United we stand succeed; Our ambition is entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

Dedicated to my brother
'''Shafee'u Musa. {shafam}'''

     *🤱 MAHAIFIYATA🤱*

          _writing by_📚✍

*🌹 Ameena first lady🌹*

_page 2⃣5⃣ to 2⃣6⃣_

Tunda suka sauka daga mota idanshi na kansu bacin ransa yafara bayyana.

Wuce shi sukayi, hakan yasa ransa yakara baci a tunanin sa sun ganshi wulanci ne yasa suka nuna Kamar basu ganshi ba.

Da zafin rai ya Mike zaibi bayansu nazeer ya rike hannun shi yace...

Kabi a hankali karkazo kaji kunya daga baya, ita macece kuma daga gani itama batada tsoro zata iyayi maka komai a nan ta zubar maka da mutumci a gaban mutane.

Wani banzan kallo Shaheed yayi Masa sanna ya fizge hannun shi ya nufi wajan su khadija.

Khadija da Zainab tafiya suke cikin nutsuwa suna hirar su hankali kwance basuda wata damuwa,.  Mutun suka gani a gaban su kawai, Zainab saida ta tsorata.

"Uban waye yabaki damar wucewa batareda kin tsaya na rama abinda kika yimin ba". Ya fada da wata irin tsawa daya jawo hankalin mutanan da suke wajan...

Khadija itama gaba daya ranta ya baci ganin yauma ko sallama bai musu ba.    Cikeda tsana zalla a idanunta ta kalle shi tana fadin.

"Wai Kai wanne irin mutum ne, wancan lokacin ni kayiwa laifi kuma tun a lokacin na rama a tunani na shikenan bata kan kowa,. Amma tundaga lokacin kake bibiyata kana takurawa rayuwata,. Kuma na fada maka kada ka kara tareni da zancan banza tunda Kai bakada aikin yi ni inada shi,. Aikin banza kawai".  Takama hannun Zainab zasu wuce.

Gaba daya Shaheed ya fita hayyacin shi sai huci yake jikinsa har rawa yake, bin bayansu yakara yi da sauri.

Fizgo hannunta yayi ta baya aikuwa tana waigowa ta daga hannu ta zabga Masa kyawawan mari biyu, sanna ta kankance idanunta tsabar bala'i na cinta...

"An fada maka ni yar iska ce irin yan iskan da kasaba yawo dasu acikin makaranta nan,. To wlhy bari na fada maka baka Kai matsayin dazaka rike kasan takalmi naba balle hannu naba, kuma daga yau karka kara tare ni ko tsayar Dani kokuma kazo inda nake, Dan iska kawai"... Sannan tayi gaba ko Zainab bata kara kallo ba......

Tunda ta mareshi yake rike da gun zuciyar shi tana harbawa da sauri idawan shi sun ja sosai yakasa motsa Koda Dan yatsan kafarshi...

*Zanso kuga Shaheed a wannan yanayin😂😂*

Nazeer ne ya karaso ya rike hannun shi yace "muje my friend kaga mutane suna kallon mu fa"

Mutanan wajan yafara bi da wani mummunan kallo da jajayan idanuwansa,. Tarwatsewa suka farayi sunsan halin Shaheed yanzu saiya dawo kansu, kafi kiftwar ido duk mutanan wajan sun gudu ba kowa sai Shaheed da Nazeer.

Kamar mara lafiya haka yakebin nazeer   a hankali suna tafiya, saida ya sakashi a motar sannan ya zagaya mazaunin driver yaja sukabar makarantar.....

Zainab kuwa sai maimaita salati takeyi a zuciyar ta rububin mutane tabi ta gudu gida Dan tace yau Saidai su hadu da khadija a gida karma ace angan su tare😃😃😃

Ganin Zainab shiru bata biyota ba yasa ta Kira Zainab din, bugu kusan biyar batayi picking ba sai ana shida ta daga.

"Hello sis kina inane"

Zainab tayi kasa da mirya Kamar Shaheed din yanajin ta tace.   "Bawani sister malama yau kinjawo mana wuta tun kafin mu mutu"

Dariya khadija ta kusa kufce mata tace.
"Matsoraciya ce ke wlhy kizo mu tafi gida yau bazan jira a tashi ba"

"Wacce Zainab kike jira, aini tuni na tsufa a gida kuma bazan fita ba sai gobe nida makaranta kuwa sai bayan sati hudu"

Dariya khadija tayi sosai sannan tace "Nima ganin to"

Tashi tayi ta dauki jakarta ta rataya ta tafi, duk inda ta nufa ido na kanta wasu har nunata suke abin ma yafara bata haushi..

Yan makarantar kuwa kowa mamakin rashin tsoran khadija yake da kuma tausaya mata abinda zai biyo baya, haka kawai Shaheed ya wulakanta mutum inaga ya tabo shi harda su mari..

Wasu samari kuwa suna zaune daya daga cikinsu ne yace "wannan yarinyar abin tausayi ce Dan nasan makarantar nan saita gagareta wlhy"

"Aiba makaranta kadai ba zaman kano saiya gagareta  kila wlhy" inji wani dake gefe.

Tunda suka fara yafiya ba Wanda yayiwa wani magana sai sautin karatun alqur'ani  da Nazeer yasa ne yake tashi.

A haka suka karasa gida nazeer yakama hannun shi suka shiga part dinsu Mamee.

Bakowa a palourn, a kan daya daga cikin makamakan kujerun dake palourn nazeer ya zaunar dashi sannan yace. "ka gaida Mamee idan ta fito sauri nakeyi"

Ko kallonsa Shaheed baiyi ba balle ya amsa Masa  .
Kusan minti6 sannan Mamee ta sauko daga uptairs batasan Yana palourn ba ta nufi wajan  kujerun, da mamaki tace "Shaheed meya faru kadawo da wuri kuma ka kwanta a nan baka tafi part dinka ba"
Ko dago Kai baiyi ba a haka yace "nothing"

"Bangane bakomai ba bayan ga muryar ka nan har rawa take, Shaheed fadamin meya faru"

Jajayan idanuwansa ya dago ya kalleta yace  "bakomai Mamee fa"
Sanin halin Shaheed yasa ta kyale shi ta nufi wajan wayarta ta Kira Daddy "hello abban Shaheed kazo ka tambayi damuwar Shaheed ni yaki fadamin"

Daddy gabansa ya fadi yace "lafiya meya samu Shaheed din"
"Nima dai ban sani ba yaki fadamin"

"Ok ganin nan"

Tarin ayyuka daddy yabari ya nufo gida ba bata lokaci.

"A palour ya samesu Shaheed ya lumshe ido Kamar mai bacci Mamee kuma tana ta fama yasha maganin zazzabi Amma yaki dagowa ma ya kalleta.

Kansa Daddy yayo Yana fadi "lafiya Shaheed meya same ka haka"

"Zazzabi ne ya rufe sosai gashi yaki fadan ko menene silar zazzabin da alama shida wanine"
Daddy yakai hannu wuyanshi yaji zafi rau.

"Subhanallahi Shaheed waye ya tabamin Kai, ko baisan waye Kai bane fadamin waye shi a garin nan"
"Daddy..."saikuma yayi shiru yaci gabada huci.
Daddy ne yace "tunda bazaka fada ba bari naje makarantar nayi bincike koma waye saina Nemo shi dakaina na hukunta tashi wlhy" ya fada Yana mikewa.

Mamee tace "haba abban Shaheed karmu biye Masa mana sannan mu dauki mataki"

"Yaki magana to a bakin wa zamuji"

"Nazeer da Usman nasan su sunsan komai tunda koda yaushe suna tare musamman a school"

Yanajin su baice komai ba.
Sannan Daddy ya zauna....

MAHAIFIYATAWhere stories live. Discover now