🌈 *_kainuwa writers association_*
https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation
*_🤱 MAHAIFIYATA 🤱_*
_By_📚✍
*_🌹 Ameena first lady🌹_*
_page 6⃣7⃣ to 6⃣8⃣_
Hafsat ce wata kawar su ta karaso kusada su fuskar ta dauke da fara'a, zama tayi kusada khadija tana mata magana cikin tsokana. "khadija kusan 2weeks bakizo school ba why"
"Bakomai hafsat, na danyi cuta ne but gashi nazo yau ai""Ohh sorry na manta fa ya jikin naki naji labari ya baza ko Ina a school Wai anyi raping dinki ko..."?
Ba khadija kadai ba har Zainab Saida cikinta ya kada tsabar mamakine ya bayyana a fuskokin su musamman khadija.
"Sorry idan ranki ya baci, Amma Nima a school din nan naji Saidai ki toshe kunnuwan ki a makarantar nan kam"
"Kinga bama San munafurci da gulma, idan kinsan haka zakiyi Mana just ki tashi kibamu waje". Zainab ce ta iya karfin halin fada mata magana.
Tabe baki hafsat tayi. "tofah! Daga fadan gaskiya sai masifa, to Allah ya kyauta Dan angana dake tunda abinda kowacce mace take takama dashi ke kin rasa"... Saida tagama fadar maganganun ta sannan tayi tafiyar ta ta barsu cikin bacin rai.
Har Zainab ta Mike zata bita khadija ta riko hannun ta tana girgiza mata Kai hawayen data makale suka samu damar zubawa.
"Kyaleta Zainab gaskiya ta fada ai, koma menene anriga angama Dani, bazan iya mayarwa da duk Wanda ya jefeni da irin wannan maganar martani ba, ki kyaleta kawai"
Dafa kafadarta Zainab tayi "kiyi hakuri khadija Dan Allah karki sa wannan a ranki harya hanaki karatu"Da lallashi Zainab ta shawo kan khadija sannan suka nufi wajan daukar lecture.
11:00am suka fito daga lecture, tun kafin su karasa wajan zaman su, taji ana Kiran sunanta bata waiga ba Dan muryar namiji taji.
Tare gabanta yayi Yana mata wani banzan kallo "Dan Allah malama kinaji ana kiranki baki amsa ba, ai munji komai kaf makarantar nan ba Wanda baisan anyi Miki fyade ba shine zaki wani disga ni to ba sanki nake ba Dan Banga me zanyi da ragowar yan iska ba kilama dama can kinabin mazan yanzu ne ya fito fili aikin banza kawai"...Duk masifar Zainab kasa Koda motsa baki tayi Dan itama maganganun sun shige ta sosai....
Da kyar ta iya danne hawayen ta suka cigabada tafiya kamar marasa laka.....
Har sukaje gida Zainab bata iya ba khadija hakuri ba Dan ta rasa ta Ina zata fara ma.
Suna zuwa khadija tace zata wuce gida yanzu mama taso ta hanata Amma firr taki yarda. Dole mama ta kyaleta ta tafi.
Tana fita Zainab ta fara kuka sosai Dan itama kawai daurewa tayi batayi a gaban khadijan ba Dan karta karya mata zuciya.Khadija kuwa da kuka tashiga palour, Aunty Rahma kasa gane kanta tayi, tayi lallashin harta gaji ta kyaleta.
Har la'asar sannan uncle Abdulmutallib ya dawo. Aunty Rahma ta sanar dashi halin da khadijan take ciki ko abinci takasa ci.
"Kiramin ita"
"To"
Kiran khadija tayi ba musu ta biyo bayanta har dinning table din.
"Khadija Meyasa bakici abinci ba"?
"Babu komai uncle"
"A'a akwai komai, ki fadamin inhar kinaso hankalina ya kwanta"
Kuka ne ya kufce mata har Saida tayi Mai isarta sannan ta Masa abinda ya faru a school da maganganun da aka fada mata.
"Dan Allah uncle ku kyakeni da karatun na hakura gabadaya dashi, zanci gaba da zaman gida har ranar da Allah zai fito min da miji..."
Duk jikinsu yayu sanyi uncle ne ya fara mata magana cikin nutsuwa "shikenan naji bakyasan karatun, kuma tunda kikace bakyaso ko kinje bazakiyi ba, saboda a hakura zan Kira Abba na fada Masa kin kwantar da hankalin ki"
"To Uncle"
"Yanzu ki samu abinci kici kinji ko"
"To"
Badan taso ba haka tadan ci abinci kadan.Uncle ya fadawa Abba komai kuma shima ya yarda Saidai yace a sama mata koda makarantar passion designer ne kuma ta yarda da hakan.
Abu kamar wasa Zainab taki yarda da auran nazeer tun ana fadan harsun koma nasiha khadija ma harta gaji dayi mata fada. Yau Abbu dakansa yaje ya samu Abban khadija ya fada Masa komai. "Wannan ai shashanci ne, shikenan kuma Dan khadija bazatayi aure yanzu ba itama saita ce bazatayi ba, bazai yiyuba zanzo na sameta zanyi mata fada karja damu Abbu"
Da haka suka rabuda abbu ya tafi gida.
Kamar yadda Abba yace zaije da yamma ya shirya ya tafi gidansu Zainab dakansa.
Mama ce da Abbu sai mommy da Abba Zainab na kasa a zaune tun kafin a fara mata fadan tafara kuka.
"Zainab naji shashancin da kike aikatawa, to bazamu yarda da wannan ba itama khadijan kaddara ce ta sanya bazamu hada kuba, itama kawar taki baza taji dadin ace saboda ita zaki bijirewa maganar iyayenki ba...."
Tun Abba Yana fada harya koma nasiha har Saida ta amince da maganar nazeer sannan Abba da Mommy sukayi musu sallama suka nufo gidan uncle.....Karatun Shaheed ya fara nisa, sosai yake kokarin mayarda hankalin sa wajan karatun gabadaya makaranta tagane irinsu Shaheed ake Kira gifted and talented.
Saidai har yanzu damuwa na nan fal zuciyar shi soyayyar khadija kamar yanzu ya fara ta.
Zaune suke da Bashir a dakinsu sau magana yake Masa Amma shiru baya bashi amsa.
Waigowar da zaiyi yaga Sam hankalin Shaheed bama a kansa yake ba.
Tabo shi yayi sannan ya dawi da kallonsa gun bashir din Yana daga Masa gira alamun menene.
Bashir da yanzu ya gama yiwa Shaheed uzuri ya matso kusa dashi. "Shaheed dukda bakasan fadawa kowa abinda yake damunka Amma yazama Dole ka rage ko Yaya ne, duba yadda ka mayarda kanka kamar wani maraya haba Dan Allah"
Ya karasa maganar cikin bacin rai.
Shima Shaheed din matsowa yayi kusada bashir din Yana dafa shi Dan ya tabbatar babu Wanda ya damu da damuwar shi kamar bashir Dan ba tun yau ba take kokarin cireshi a damuwa.
"Bashir kayi hakuri bawai naki daukar shawarar ka bane, babu yanda zanyi na cire damuwa a Raina Dan bazan iya ba...."
Da haka har Saida ya fada Masa komai tundaga haduwar shi da khadija har rabuwar su.
Jinjina Kai bashir yayi ya dago kansa "lallai Shaheed Dole ka damu Dan bakaramin so kake mata Saidai Kuma ka aikata kuskuran da bakada wata mafita a wajanta, Saidai dukda haka ka manta da wancan maganar har kaci gabada rokar Allah hakan zai rage maka wata damuwar."
"Shikenan I will inshallahu"
Da haka suka fara hirar su bashir na bashi labarin zuwan shi America sosai Shaheed yake nishadi harda murmushin sa Mai kayatarwa.Tun daga wannan ranar Shaheed ya rage damuwa dukda bai cireta duka ba Amma ya fara daina yawan tunani dayake a da, sosai yafara kiba fatarshi ta canza yazama kamar yadda yake da.
***** ***** *****
Maganar Zainab kam tayi nisa sosai har angama magana an saka ranar biki wata takwas masu zuwa ranar Zainab taci kuka sosai..
Khadija kuwa yanzu damuwar ta hartafi ta baya sakamakon yadda kowanne saurayi ke bacewa da zarar yaji abinda ya faru da ita.
Bangaran karatu ma uncle ya nema mata wata Mai kyau ita da Zainab Dan itama cewa tayi tunda khadija bataso itama bazatayi ba.Har khadija ta dauri aniyar bazata kara yadda da wani saurayin ba zataci gabada zama a haka Dan gudun bacin rai....
Yauma Kamar kullum ta dawo daga islamiyyar da uncle ya sata ta yamma. Tafiya takeyi a hankali cikin nutsuwa kamar yadda take.
Harta shiga ta zauna yaro yayi sallama ana Kiran wacce tashigo yanzu.
Da sauri khadija tace "Kai kace ba wata da tashigo yanzu"
Dan kar Aunty Rahma taji tazo tayi mata Dole saita fita.Yaro ya fita ya fada Masa, murmushi saurayin yayi daman yasan za'ayi hakan Dan wannan kalar matan manya ce.
Kudi ya bawa yaron sannan ya shiga motar sa ta tafi cikeda daukar wa kansa alkawarin saiya dawo tunda ya gane gidan.Khadija kuwa ganin yaron bai dawo ba hakan yayi mata dadi sosai ta cire hijjabinta tayi alwala.....