*🤱 MAHAIFIYATA 🤱*
_writing by_📚✍
*🌹 Ameena first lady🌹*
Dedicated to my sweet brother
'''Shafi'u Musa. {Shafam}'''💕💞_watsapp number_
08112138112
For commentsPls share
_page 31 to 32
*****
Rufe motar yayi suka tafi tare su duka ukun.Zainab da khadija suna zaune khadija tana fada mara yadda sukayi daddy kafin ya yadda ta koma, sai sallama suka ji ta bayansu.
Amsa sukayi tareda waigawa jin muryar maza ce.
Lallaima wato baiji marin danayi Masa kenan.khadija ta fada a ranta, a fili kuma tace.
"Kaga malam nace ka fita harkata Amma kaki, menayi maka dazaka dinga bibiyata Kamar wacce nice nayi maka laifi bakaine kayimin ba"Zuciyar Shaheed tafara tafasa saboda tuna abinda tayi Masa Amma saiya dake yace.
"Nasan nane da laifi yau banazo Dan fada bane, nazo ne nabaki hakuri Dan Allah kiyi hakuri hakan bazata sake faruwa ba"
Ba Zainab kadai ba har nazeer saida hantar cikinsa ya kada Dan yasan ba Dan Allah Shaheed ya sauko haka ba.
"Na hakura komai ya wuce Amma karka kara shiga sabga ta daga yau."
"Kenan baki hakura ba"?
"Nace na hakura"
"To indai kin hakura karki yankemin hukuncin karna kara shiga sabgar ki"
Jakarta ta dauka tayi gaba ko kallansu batayi ba.
Nazeer yace "ka kyaleta Shaheed zuwa jibi saika kara bata hakurin"
"Shikenan Allah ya kaimu"
***** ***** *****
Yau khadija ta koma gida a farfajiyar gidan aunty rahma ta sauketa sukayi sallama ta tafi juya ta koma gida. bataga mommy a palour ba ta wuce dakinta Kai tsaye.
Saida tagama gyara dakin sannan ta fito neman abinci.
Dakin mai aikinsu ta nufa, mama uwani.
Tana shiga mama uwani tace "lale da mutanan hijira"Khadija tayi murmushi.
"Niba hijira nayi ba ai"
"Eh Amma kin gujemu ai"
"To gashi na dawo yanzu""Naji dadin dawowar taki, yakika baro su"
"Lafiya kalau sunce a gaisheki"
"Ina amsawa""Mama uwani muje kichiene yunwa nakeji"
" Basai kin dafa komai ba akwai a binci a cooler"
"Yauwa mama uwani" tace sannan ta fita.
Kashe gari ba school saboda weekend ce, ranar Abba ya dawo daga Lagos.
Murna sosai khadija tayi daman zaman gidan bai mata dadi ba abokin hira."Abba yau muje kakaini mu zaga gari"
"To yar Abba anjima ki shirya"5:30 khadija suka fita itada abbanta su zaga gari.
Wajan shakatawa Abba ya dinga Kai khadija, daga karshe suka wuce shopping zata sayi cosmetics.
Abba kuwa zama yayi a mota yace idan tagama ta Kira wayarshi zai shigo ya biya su wuce.
Zagawa khadija yati tana jidar cosmetics saida ta gama ta juya zata nufi wajan biya, wazata gani, Shaheed ne a tsaye ya harde hannu fuskar shi dauke da murmushi Yana kallonta.
Khadija ma kallon nasa take ba karamin kyau yayiba kananun kayane a jikin shi tsintsiyar hannun shi daure da agogo mai shegen kyau.
Dauke idanunta tayi sannan ta raba ta gefen shi zata wuce.
Tare gabanta yayi yace.
"Haba khadija koba komai ai kya tsaya mu gaisa ko"
"Sauri nakeyi kabani hanya na wuce pls"Bai kulata ba saima wata tambayar ya kuma jefa mata.
"Me kika zo siya ne"
"Bansani ba, kabani hanya zan wuce ni"
"Idan Kinga nabaki waje kin wuce saikin fadamin abinda kikazo siya"Mamaki yakama khadija.
"Menene dalilin dayasa kakesan sanin abinda na siya"?.
Make kafada yayi ya tabe baki.
"Oho kawai naji Ina San sani ne"Wani kallo tayi Masa sannan ta kawar dakai gefe alamun bazata fadaba kenan.
"Ashe zamu kwana anan"
Shiru tayi bata kulasa ba.
Ganin tana bata musu lokaci ne yasa ya karasa kusa da ita har sunajin numfashin juna.
Gaban khadija ya fadi tayi tunanin wani abu zai mata.Hannu ya Mika Kamar zai taba wuyanta, ta runtse idanuwanta, kusan second8 ta bude saitaga Yana kallan ta.
Gira ya daga mata sannan ya kalli saitin hannun shi yace.
" Keken siyayyar zaki bani, nagani da kaina"Hannun nashi tabi da kallo sai lokacin ta lura ashe kasa yayi da hannun.
Ba musu ta saki, ga mamakin ta sai yayi gaba dashi abinsa.
A baya tabishi taga mai zaiyi, saitaga Yana jibgar wasu cosmetics din Yana zubawa Kamar ba kudi zaisa ya biya ba,bata gama mamakin taba saida taga ya koma bangaran dogayan riguna.
Saida ya jibgi kaya Kamar wacce zata bude Dan karamin shago sannan ya nufi wajan biyan kudi.
Tare gabanshi tayi sannan tayi kokarin cewa.
"Kaga nifa bance maka Ina bukatansu ba, idan ma Ina bukata tare nake da abbana zai biya kudin kabar kudin ka bana bukata"Tsayawa yayi saida tagama sannan yace.
"Ai bance bakida kudin biyaba, kuma ni dakaina zanyiwa Abba bayani yadda zai gamsu"
"Dan Allah karka nuna kasanni ma a gaban abbana pls kabani zan biya dakaina"Make kafada yayi yace. "Well tunda bakyason Abba yasani kawai ki karba"
"Yaya Shaheed Ina kayi naketa nemanka...."
Maganar Meera ce ta makale ganin Shaheed da wata kyakkyawar yarinya."Sannu"Meera tace
Murmushin yake khadija tayi ganin Kamar yarinyar da Shaheed tace
"Yauwa sannu"Hade fuska Shaheed.
Meera kum ta kalleshi tace.
"Yaya Shaheed nagama siyayyar""Kije ki jirani gani nan"
"To"Wajan biyan kudin ya karasa, khadija batasan nawa ya biyaba Amma tasan ba kananun kudade bane.
Bayan angama zuba kayan a bag ya Mika mata yace "gashi"
Kin karba tayi.
"Idan kika karba hakan zai tabbatar min kin hakura da laifin danayi Miki kenan, sannan zan wuce bazan nuna na sanki ba"
"Idan baki karba kuma nasan baki hakura ba, sannan zanje na fadawa Abba soyayya mukeyi dake, nayi Miki laifi na baki hakuri kinki hakura".Kallon fuskar shi tayi taga da gaske yake zai iya, sai ta karbi kayan tayi gaba abinta ko godiya batayi Masa ba.
A waje ta samu Abba ta shiga motar.
"Yar Abba kingama siyayyar shine baki kirani ba"?
"Eh Abba da kudi a account Dina dasu nayi amfani"
"Kin tabbatar"
"Eh abba""Amma baki fadamin kin tahoda ATM card dinki ba"
"Yana jakata ai na taho dashi fada maka ne banyi ba"
"To shikenan"
Motar ya tayar suke tafi.
Shaheed kuwa tana fita yayi wani shu'umin murmushi sannan ya koma wajan daya ajiye Meera tana jiranshi.
Saida ya biya kudin suka shiga mota sannan Meera tace.
"Yaya Shaheed wacece wacce naganku tare""Bansani ba"yace Yana wani cin magani.
Tabe baki tayi tace
"Koma wacece dai saina fadawa Daddy da Mamee"Burki ya taka da karfi, meeray ta tsorata sosai.
"Munafuka wlhy idan kika fada musu saina karya ki kuma saikinyi dakin sani""Wlhy bazan fada ba dama tsokanar nakeyi"
"Oho kima fada munafuka kawai"
Yaja motar suka tafi.