part 20

161 10 0
                                    

*🤱 MAHAIFIYATA🤱*

_by_📚✍

*🌹 Ameena first lady🌹*

Dedicated to all _MAHAIFIYATA fans_

_page3⃣7⃣ to 3⃣8⃣_

Harta karaso  bai dauke idanun shi daga kanta ba.
Ganin nazeer a baya yasa Zainab itama tashiga bayan suka barwa khadija gaban itada Shaheed.
Ko kallon gefensa batayi ba ta zauna, ya tayar da motar suka tafi.
Zainab da  Nazeer sai hirar su sukeyi Amma su kamar kurame ganin ta hade fuska yasa ya mayarda hankalin sa kan driving din dayakeyi.

Private hospital taga sun shiga.
"Lallaima daga ciwan Kai saiya wani kawota hospital kuma ma private"
Ta fada a ranta.
"Ku jirani Ina zuwa" yace Yana fita daga motar.
Cikin asibitin ya shiga saigashi ya fito, da window din motar ya leka.
"Ku fito muje"
Ba musu suka fito su duka suka bishi.
Gun babban likita yakaita.
Tambayoyi yayi mata sosai tana bashi amsa saida yagama sannan ya ajiye biron hannun shi ya kalleta.
"Kinsan kinda hawan jini Wanda yake barazanar shafar zuciyar ki"
Ga mamakin Shaheed saiyaga bata razana ba saima cewa datayi.
"Eh doctor nasani"
"To Amma meyasa bakya kiyaye lafiyarki wajan sanyawa zuciyar ki tunani"
"Insha Allahu doctor zan kiyaye"
"Yakamata dai" ya fada Yana mikawa Shaheed takardar magungunan.
"Gashi nan saikuje a saimata wadannan magungunan mugani"
"Thank you doctor"
"Ur welcome"

"Tashi muje" Shaheed yace.
Zainab kuwa ranta ya baci wato duk fadan dasu Abba da uncle sukayiwa khadija batajiba kenan.

Tare suka shiga baya yanzu itada Zainab din, satar kallon Zainab tayi taga alamun ran Zainab din ya baci.
"Sorry bloody, nasan na karya alkawarin danayi Miki Amma kinsan tunani dolene a gareni"ta fada hawaye ya saukowa daga idanunta.
Ganin hakan yasa Zainab sassauta fushinta ta riko hannun khadijan.
"Nasan kina hakuri a hakan ma khadija Dan ba kowacce yarinya ce zata dauki hakurin wannan halin da kike ciki ba, Amma kodan Abba Dan Allah ki cirewa kanki wannan tunanin"
"Insha Allahu zanyi kokarin ragewa nayi Miki alkawari"
"Yauwa bloody".
Duk abinda suke fada Shaheed yanajin su har zuciyar shi yaji tausayin ta kuma yanasan yaji dalilin daya haddasa mata hawan jini tun tana karamar ta haka.

A wani katon saida magunguna yayi parking.
"Ina zuwa yanzu zan dawo" bai jira amsar suba ya fice.

Saida ya siyo magungunan sannan ya shiga shagon saida drinks, kusan minti goma say gashi ya dawo da manyan ledoji guda biyu.

Ya tayarda motar suka tafi.

Nazeer yafara saukewa sannan ya wuce dasu har gidan su Zainab.
A bakin gate ya tsaya.
Zainab ta fito zata shige yace.
"Pls shiga da magungunan nan"
Hannu tasa ta karba ta shige ta barsu shida khadija.

Waigowa yayi ya fuskance ta sosai ya harde hannu.
Saida ya kare mata kallo sannan yace.
"Bansan dalilin dayake saki tunani ba Amma koma menene hakuri zaki kara akan Wanda kikeyi yanzu, kuma Ina fatan zaki sha maganinki kafin ki kwanta"
"Eh zansha"
"Kinyi alkawari"
"Nayi"

"To sai gobe"
"Nagode sosai da kulawa"tana fada ta shige gida.
Saida yaga shigewar ta sannan ya tafi.

Mamace a kadai a palour.  "Sannu khadija, ya kan naki yanzu"

"Da sauki Mama"
"To jeki ki watsa ruwa kizo kici abinci"
"To Mama"
A daki ta samu Zainab tana bude ledar drinks din da Shaheed ya siyo.
"Gaskiya Shaheed ya kashe kudi wlhy, kinyi Masa godiya ko"
"Eh nayi Masa man"
"Mama fa tace muje mucu abinci"
"Ai saiki bari muyi wanka"Zainab tace tana shigewa bathroom.
Tana shiga wayarta tafara ring.
Khadija ta matsa zata daga.
My kawai tagani a screen din.
"Lallaima wato Zainab harwani my gareta bansani ba"
Kusada bathroom din ta matsa tace.
"Bloody ankira ki fa"
"Waye ki daga mana"
"A'a bazan iya daga wayar masoya ba"
"To waye".  Nidai Naga my a screen din"
"Ki daga nazeer ne" Zainab ta bata amsa tana daga bathroom.
"Nazeer"khadija ta maimaita a zuciyar ta.
Zainab ce ta fito tace.
"Waike nazeer dinne baki saniba kome".
"Nasan shi mana, koba nazeer din Shaheed Dina ba".
Da mamaki Zainab ta kalleta tace "Shaheed dinki, yaushe yazama naki kodai zargina ya tabbata ne"
Sai yanzu khadija tagane barontan datay, aikuwa tayi wuf tashige wanka tana dariya.
"Lallai khadija zaki fito kiyimin bayanin waye Shaheed din naki"
Wayarta ce tasake kara ta dauka tana sauya salon murya.

Nidai nace oo su Zainab an kamu😂

Waya sukeyi sosai kamar tsofaffin masoya, suna cikin yin wayar yaga Kiran Shaheed,
"Kinga Shaheed Yana Kira, Ina zuwa naji ko lafiya"
Bayan ya katse wayar yabi Kiran Shaheed din.
"Hello Shaheed ya akayi"
"Yauwa nazeer Dan Allah number khadija zaka samomin wajan kawar nan tata, naga kunyi exchange din number daxu"
"Kai Amma dansa idone wlh "
"Eh naji, nidai ka tambayar min ita pls"
"To bani minti biyar"
"Ok" Shaheed yace ya katse Kiran.
Zainab ya sake kira.
"Hello wife"
"Na'am"
"Pls taimako zakiyimin"
"To inajinka"
"Number khadija zaki bamu Shaheed Yana bukata".
Shiru tayi saikuma tace.
"To barina turo maka".
Number ta tura masa, bai bata lokaci ba ya turawa Shaheed.
Saida sukagama lunch ta nufi daki ta kwanta.wayarta ta janyo,ganin sako tayi ta bude.
"Nakira phone dinki bakiyi picking ba Ina fatan lafiya"
Murmushi ne ya kwace mata daidai Zainab tashigo.
"Keda waye kike murmushi"
"Nida abbana ne"
"Ohh"
"Zainab gobe zan koma gida fa".
"Keda bakida lafiya,kibari saikin karajin sauki".
"A'a nidai Mom ita kadaice bazataji dadin zamaba".
"Eh to hakane kuma, Allah yakaimu".

Kafin dare saida Shaheed yayi mata message kusan goma kuma duk tambayar ya jikinta yakeyi.taji dadin kulawa sosai dayake nunawa a kanta.
Shaheed kuwa Yana fitowa daga sallar Isha yacewa Usman zaije yaga jikin khadija.
"Shaheed karfa ka manta dalilin kulla alakar ka da yarinyar nan".
"Ban manta ba, meka gani".
"Naga kana wani zakewa sosai ai".
Murmushi kawai Shaheed yayi yayi gaba yabarshi a anan.
A kofar gidan su Zainab yayi parkin, sannan ya Kira layin khadija,bugu biyu ta daga.
"Hell".
"Ki fito ina waje"
"Da gaske ta fada"
"Em aikin San bazan Miki wasa ba"
"To gani nan"
Katse wayar yayi ya zauna saman motar Yana jiran fitowar ta.
"Zainab kinji Shaheed Wai Yana waje"
Itama Zainab tayi mamaki Amma saita maze.
"To kitashi kije karyayi ta jiranki"
Tashi tayi ta sana hijjabinta har kasa ta fice.
Tun daga nesa ta hango shi saman mota yanata danne danne a wayar shi, baisan ta zoba sai sallamar ta yaji.....

"Nazaci ai bazaki fito"
"A'a gashi ma na fito"
"Toya jikin naki"
"Alhamdulillahi"
"Idan fa ba sauki ki fada mukoma hospital din"
"Na ji sauki"
Saukowa yayi daga saman motar yace. "shikenan dama nazo ne naga yanayin jikin, alhamdulillahi jiki kuma yayi kyau, nizan tafi"
"To nagode sosai"
Sukayi sallama ta shige gida.

MAHAIFIYATAWhere stories live. Discover now