44

150 14 0
                                    

*🤱MAHAIFIYATA🤱*

_By_📚✍

*🌹Ameena first lady🌹*

🌈 *KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*

'''{United we stand and succeed; Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

_page8⃣5⃣ to 8⃣6⃣_

Khadija tana shiga ɗaki da kuka ta ta ƙarasa jikin zainab,.
"Meya faru Khadija, koya Miki wani abu ne...." Zainab ta tambayeta a tsorace...
Girgiza Kai tayi,.  "A'a zainab baimin komai ba saidai na shirya zama cikin ƙunci da bakin ciki a gidan shaheed...."
"Kar kice haka Khadija, shaheed yana sanki bazai taɓa wulakanta kiba.."
Bata sake cewa komai ba taci gabada kukan ta me tsuma xuciya.

Shaheed kuwa ko a jikinsa, nazeer ne dake gefensa ya kalle shi yace.  "Shaheed kana ganin bakayi kuskure ba kuwa.."
"Kuskuren mefa.."?
Ya tambaya.

"ni ganina lallaɓa Khadija yakamata kayi, baka bi mata ta haka ba, tayaya zaku fahimci juna kuna irin wannan..."
Murmushi yayi sannan ya juya ya kalli nazeer dake gefensa.   "Nazeer gaskiya yadda nakejin kaina Kamar na riga na zama mijinta bazan iya lallaɓa ba, Dan hakan zaisa taga Kamar da gaske banida gaskiya sannan kuma zata iya raina ni..."
Dariya nazeer yayi sosai "lallai shaheed har yanzu kana nan da halinka na kafiya da shegen isa, you will never change"..
Ko kallan sa shaheed baiyi ba yaci gabada driving ɗinsa yana murmusawa....

Khadija kusa har lokacin kwanciya bacci yayi har zainab tayi bacci saboda gajiya, Amma ita Sam takasa baccin.
Kewa tareda tsabar tausayin kanta na rashin masoyin ta Khalid ne ya hanata bacci.
Kamar an tsikareta ta dauko wayarta dake kan stool tafara Jero numbobin Khalid dake cikin kwakwalwarta...
Cikin sa'a ta samu wayar ta shiga har xuciyar ta taji daɗi duk tasan ba lallai ya ɗaga ba Amma ko iya hakan zaisa taji daɗi.

Lokacin Khalid na kwance yana kallon picture ɗinta dake screen ɗin kan wayarsa. Duk wanda yasan Khalid ɗan kwalisa bazai iya gane shi ta farar ɗaya ba saboda tsabar ramar da yayi.
Kamar a mafarki yaga numbern Khadija, kama bazaiyi picking ba saikuma ya ɗaga zuciyar shi a karye...
Kusan mintina biyu suka ɗauka Babu wanda yayi magana.,. Khalid ne yafara magana cikin karyewar murya da ƙunci.
"Kiyi hakuri Khadija nasan na karya Miki zuciya nasa ƴan uwana sun muzantaki amm..."
Katse shi ta hanyar dakatar da zancan nasa da sauri.   "A'a Khalid ba laifin su bane, ba sanka sukeyi shiyasa bazasu so jikokin su su rasa tushe me kyau ba saboda haka karka ga laifin su nima wlhy har xuciya ta ban kullaci komai ba kodan soyayyar danake maka bazan ga baƙin suba.."
"Nasa ni Khadija, Amma inaso ki sani mutuwa ce kaɗai zata iya rabani da soyayyar ki, saboda haka bazan iya jurar gani ko jin labarin zaki auri wanina ba, zan bar ƙasar jibi..."
Ba karamin faɗuwa gaban Khadija yayiba jin Khalid ɗinta zaiyi Nisa da ita.....
"Dan Allah Khalid karkayi nesa dani, bazan iya jurar tafiyar kaba."
"Koban tafi ba Khadija, zamana bazai ƙareki da komai saidai ma ya sake jefa kawunan mu a cikin wani hali, shiyasa dole zan tafi.., Amma kafin nan inaso na sake ganink.."
Wata faɗuwar gaba ce ta ziyar ci zuciyar ta, bazata iya yimasa musu ba, Amma wacce hanyar zatabi su haɗu, Dan itama tana mutuka san Sanya shi cikin idanuwanta.

Tunaninta ne ya katse jin muryar shi Kamar zaiyi kuka.
"Dan Allah Khadija karki hanani sake ganinki a rayuwata plsss"
Haka kawai ta tsinci kanta da amincewa.

"Allah ya kaimu..."
Sun sha hira sosai har saida tafara jin bacci sannan sukayi sallama.

Saida suka gama wayar sannan tafara tinanin tayi wautar amsa masa, dukda tasan Khalid baisan  gobe ne ɗaurin aurenta ba  tayaya ma zasu haɗu kuma a ina, tasan ko zainab bazata goyi bayanta ba saboda haka shiru zatayi bazata faɗawa kowa ba....
Batayi mamakin ganin Miss call din shaheed ba saidai ko damuwa batayi ba ta juya tafara baccin ta.

Shaheed kuwa ransa yagama ɓaci,. "dawa yarinyar nan take waya haka".
"Da saurayin ta Mana,  Babu ƙawar dazata kirata by this time". Wata zuciyar tashi tabashi amsa.

Harzai sake kiranta saikuma ya kashe wayar tashi gaba ɗaya.

Yau takamata ɗaurin aure, duk ɓangarorin suna cikin busy,.
Zainab ce ta shigo ɗakinsu tasamu Khadija kwance Bata da niyyar tashi ta shirya su fits.
"Haba Khadija ki tashi mana, mutafi kinsan fa munbar ƙawayenmu a can gidan uncle abdulmutallib suna jira, kuma kinsan acan zamu shirya ko bai kamata mu muzauna ba..."
Khadija da sai yanzu ta kalli zainab jikinta a saɓule tace.

"kije kawai zanzo na sameku"
"Shikenan nina tafi". Ta faɗa tana ficewa daga ɗakin....

Saida ta kusa mintina goma da tafiya kiran Khalid ya shigo wayar Khadija.
Ba Bata lokaci yakira ta yace yana sit room.

Jiki a sanyaye ta ɗauki mayafi ta nufi sit room, mommy kam batasan wainar da Khadija take toyaba tana cikin mutane..

Idanuwan shi a kanta harta karaso ta zauna,.
Ita kuwa tausayi da tsabar tsorata da ramar da yayi sune suka sa taji hawaye suna kokarin zubo mata ba karamin juriya tayi wajan iya ruƙe suba.

Kasa tayi da kanta Dan karya gano karayar da zuciyar tayi yakasa jurewa.
"Na dameki da kallo ko.."? Ya tambayeta yana wani murmushi wanda yafi kuka ciwo.
"Kiyi har yanzu ji nake Kamar kallon karshe nake Miki..". Sosai kalaman nashi suke tasiri a zuciyar ta.

Daga karshe yayi mata fatan alkhairi ya mike ya fice..
Hawayene yake ta faman zubo mata takasa tsayar dashi, ko kallon gift din daya kawo mata Bata yiba tabi bayan shi itama.

Turus tayi ganin shaheed a tsaye a bakin room din, fuskar nan Kamar bai taɓa dariya ba.
Waigawa tayi da sauri hanyar da Khalid yayi har kusa ficewa daga gidan, sannan ta kalli shaheed da shima yabi motar da ido, kasa motsawa tayi itama Dan a yanayin data ganshi ba karamin kwarjini yayi mata ba.
Ko inda take baisake kallo ba ya nufi motar shi ya fice.

Jiki a sanyaye itama ta shige gida.
Mommy ta shigo dakin tasameta tana kuka sosai.
"Khadija meya faru, ko wani abu shaheed ɗin yayi Miki.."
Girgiza Kanta kawai tayi.
"Tome yafaru naga dai shine yazo nemanki ai,.."
"Babu komai mommy.."
"Tome yasaki kuka haka."

"Mommy kinfi kowa sanin banasan auran nan,"

"Shine ya saki kuka, kiyi hakuri kowanne mutum da kaddarar sa wannan itace kaddarar ki Khadija.., kiyiwa mahaifin ki biyayya karki tayar da wannan maganar ta bakyasan shaheed kinji".

Cikin kuka ta amsawa mommy....

MAHAIFIYATAWhere stories live. Discover now