42

177 11 0
                                    

🌈 *KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*

https://www.fcebook.com/kainuwawritersassociation

               *🤱 MAHAIFIYATA 🤱*

_By_

*🌹 Ameena first lady 🌹*
Wattpad @Ameenafirstlady

_page 8️⃣1️⃣ to 8️⃣2️⃣_

___________________________

Sai biyu na dare sannan khadija ta farfado, da sauri Mommy tayo kanta da tambaya.
"Khadija kin tashi, ya kike jin jikin naki"

"Da sauki mommy, Ina Abba"
Waigawa mommy tayi, saitaga harya fita Kiran doctor.

Tareda doctorn suka shigo, Zainab dai tana kusada khadija takasa matsawa.

Saida doctor yagama dube duben sa sannan yace subata magungunan ta, zuwa da safe tunda babu matsala za'a sallame su.
Tun kafin ya fita khadija take zubar da ruwan hawaye, gani takeyi kamar a mafarki Wai yau Shaheed a gidansu Kuma a matsayin Wanda zata aura, wani saban kukan ne Mai sauti ya sake kwace mata.
Saida tayi Mai isarta sannan Abba yafara magana me dauke da Nasiha da lallami.
"Bazamu hanaki kuka ba khadija Dan bamusan dalilin yinsa ba, Amma yakamata koma menene kibari mubi komai a hankali Dan babu ta yadda zamu tambayeki meya hadaki da Shaheed har saikin warke zuwa gobe kamar yadda doctor yace"

A hankali ta kamo hannun abban nata tana kuka Mai tsuma zuciya,. Cikin da kashewar murya tafara magana tana zubar da ruwan hawaye masu zafi da kuna.
"Abba bazan daina zubar da hawaye ba har saika yimin alkawari  zaka warware aurena da Shaheed a gobe..."
Zabura mommy da Abba sukayi Amma banda Zainab wacce daman tasan hakan khadija zata ce.
Shiru Abba yayi sannan ya nisa. "bazan iya haka ba khadija kema Kuma kinsan dalili, Saidai mubari goben muji idan hujjar babba ce Dole hakan ce zata faru". Yana fada ya fice daga dakin dukda daran da riga yayi a lokacin.

Mommy ce ta matso tana shafa goshinta. "kiyi hakuri khadija karki tsiro da wata fitinar, juma kome Shaheed yayi Miki karkiyi jayayya da abbanki kibashi kunya a duk hukuncin daya yanke"

"Mommy koke kikaji me Shaheed yayimin bazaki bari na aure shi ba"
"Naji khadija yanzu dai ki kwanta ki huta kinji"
Bata sake kula kowa ba taci gabada kukan ta.

Shaheed kuwa yadda yaga dare haka yaga safiya duk iya satar bacci ranar dai Saida ya kyale Shaheed yayi kwanan bakin ciki da tunani iri iri, babban abinda yake tsoro kar khadija taking yarda auran nasu Kuma tabbas yasan gaka saita faru.

Kamar yadda doctor yace da sassafe ya sallame su suka nufi gidan su khadijan na ainihi......

Da safe Meera ce taje ta tashi Shaheed sakamakon zazzabin daya rufe shi tun daren jiya.

Da kyar ya iya tashi yayi wanka ya shirya tsaff sannan ya nufi part dinsu Mamee.

Da kyar suka amsa Masa gaisuwar shi, ya fahimci hakan Saidai yasan yau me rabashi dasu sai Allah Dan tabbas yasan khadija bazata rufa Masa asiri ba.

Meerah dai school ta tafi, su uku ne kawai suka nufi gidan Alhj Ahmad bayan Abba ya tabbatar musu da suna can su duka.

Zaune suke gaba dayansu a palour, babu abinda kakeji sai kukan khadija dake tashi, tana gefe kusada mommy Zainab kuwa tana daki a kwance tana tausayin kawar tata.

Shiru na tsawon wani lokaci, Abba ne ya katse shirun Yana gyaran murya sannan yafara jawabi.
"Yau saura kwana hudu bikin nan kowa yasani Kuma mungama gayyato abokanmu da yan uwa, Amma sai gashi wata matsala ta gifta wacce Dole khadija da Shaheed ne zasu warware Mana abinda ya faru tsakanin su..."
Kallon shi ya mayar kan khadija wacce take ta faman kuka.

MAHAIFIYATAWhere stories live. Discover now