🌈 *kainuwa writers association*
*_🤱 MAHAIFIYATA 🤱_*
_by_📚✍
*_🌹 Ameena first lady🌹_*
Dedicated to
'''Shafi'u Musa {shafam}'''💘💘💘_page 5⃣3⃣ to 5⃣4⃣_
......tuki yakeyi ko gefenta bai sake kallo ba, itama bata sake kallon gefensa ba sai danne danne takeyi a wayarta...
Har sukaje rijiyar zaki bawanda ya sake magana sai tashin kidane ke tashi a hankali cikin wakar turawa.
Jin motar ta tsaya yasa khadija tago kanta, wani bakin gate tagani sun tsaya a kofarsa fita tayi ta nufi cikin gidan abin mamaki sai taga ashe a bude yake ba gateman bata kawo komai a ranta ba ta nufi cikin gidan...
Shaheed a baya ya bita, jin ya biyota ta tsaya tana kallon shi.
"Kajira ni a waje Mana meye na saika biyoni ciki"Tabe baki yayi yace.. "waya fada miki kena biyo me gidan ai kawar mommy nace itace ma ta aikani dauko ki ai"
Bata Kuma maganaba ta cigaba da tafita..Sallama tayi tana shiga palourn gidan, shiru ba'a amsa mata ba, kalle kalle takeyi ganin ba alamun mutum ta nufi hanyar fita, ta tambayi Shaheed din taji shiru...
Waigowar da zatayi taga Yana rufe kofar..Gabanta ne yayi mummunar faduwa. Me Shaheed yake nufi...
"Shaheed me kake nufi, Banga alamun mutane a nanba kuma naga kamar ka rufe kofa"
Wani shu'umin murmushi yayi sannan yayi sama da key din ya cafe..
"Kin dauka ke kadaice me wayau, nayi amfani da wayau na na kawo ki nan ko kina mamaki ne"..
"Shaheed budemin kofa na fita""Bazan bude ba, idan zaki iya ga waje nan bude Mana"
Kofar ta nufa tafara kokarin budewa Saidai har hannuwanta suka fara zafi bata iya budewa ba.
"Shaheed bana San iskanci ka budemin kofa na tafi..."
Kafin ta karasa taji ya finciko ta da karfi , bayanta ya hade da kirjin shi ya sakala fuskar shi ta wuyanta..
"Duk lokacin da kika kirani da Dan iska, inaji zuciyata tana min zafi, Amma yau zan gwada Miki nidin dagaske Dan iskan ne..."Wani uban razana tayi ta fincike jikinta takoma gefe, tuni idanunta sun fara tsiyayar da ruwan hawaye, muryar na rawa tafara magana..
"Karya kake Shaheed, a bakinka kadai kake iya furta mummunar kalmar nan Amma Nina sani bazaka iya cimin zarafi ba, duk abinda ka fada bazaka iya aikatawa ba.."
Har zuciyar shi ya yarda da kalamanta "kwarai bazan iya wulakanta kiba Amma zan koya Miki hankali". Amma a fili sai
Tabe baki ya kumayi Yana murmushi.Matsota yayi tana baya Yana fadin.
"Karki yaudari kanki khadija kece mace ta farko da zan koyawa hankali nasan daga yau bazaki sake kirana da Dan iska ba""Shaheed Dan Allah karka batamin rayuwa karka barwa zuriyata mummunan tarih..."
Jin an caka mata wani Abu a hannunta ta baya yasa ta waiga a firgice kafin tayi magana tuni taji duk lakar jikinta ta saki idanuwan suna barazanar rufewa duk kokarin ta na karsu rufe tuni ta fadi yarab kamar matatta.
"Usman meye haka mekayi mata haka"
Shaheed ya jerawa Usman tambayoyi a jere.."Kaga kwantar da hankalin ka naga tana bata Mana lokaci ne kaga a haka ai bazata iya ko magana ba"
Wani bakin ciki ne ya rufe Shaheed..
"Haba Usman nifa bawani abu zanyi mata ba inaso ne tagane yadda kalmar take batamin rai Amma Amma..."
Bai karasaba saboda yadda yakejin zuciyar shi tana zafi.."Amma Shaheed kabani mamaki, ai banyi tunanin kaidin wawa bane sai yau, tayaya zaka samu damar dauko irin wannan macen koba khadija bace kace Wai bazaka iya mata komaiba, ni kabarni tunda Kai bazaka iya ba..."
Tunda yafara maganar idanuwan Shaheed suka fara canza kala tsabar bakin ciki da kishi..
Da bango ya gwara Usman sannan ya had a wuyanshi ya matse da bango.
"Kai waye dazaka taba khadija, wlhy ko hannunta baka isa ka taba ba idan kuwa ka kuskura ka aikata irin wannan laifin to wlhy zan manta abotar dake tsakaninmu zan hukunta ka irin hukuncin da ba'a tabayiwa wani Dan iska ba"Sakinsa yayi sannan ya nufi wajan khadija, ya rasa yadda zaiyi bashida zabi da ya wuce ya dauketa ya nufi mota da ita...
Usman Shaheed na sakin shi ya gudu daki ya rufo kansa Yana maida numfashi...
***** ***** ******
Hankalin mommy yafara tashi ganin khadija har 9:00pm bata dawo ba da farko ta share Amma a zuciyar ta hankalin yana kan yarta guda daya tilo..
9:34pm hankalin Mommy yagama tashi ko zama takasa, wayarta ta dauko takira number hajiya salamatu bugu biyu ta daga muryarta da alamun bacci.
"Hajiya Ina khadija ko a nan zata kwana ne hankali na yatashi naji shiru"
"Wacce khadijan, aini tunda muka gama magana akan zaki turo a karba Miki kayan bawanda yazo karba"
Damm gaban Mommy yafadi..
"Kina nufin khadija yata batazo wajanki ba""A'a niba Wanda zo hajiy.."
Katse wayar Mommy tayi, takira layin Zainab karona farko..
"Hello"
"Khadija batazo nanba"Jin muryar Mommy yasa Zainab mikewa sosai, abinda mommy ta tambayeta ne ya dada saka gabanta faduwa.
"Batazo ba mommy lafiya kuwa.."Itama kafin takasa mommy ta kashe wayar..
Jagwab tafada kan kujera hawaye suka fara saukowa daga idanunta..
"Me yake Shirin faruwa da yarta ne meyake faruwa kardai ta salwantar da rayuwar yarta"
Zumbur ta Mike tafara Kiran layin khadija karo na farko a rayuwar ta..
Switch off wayar..Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un tafara maimaitawa.
Shaheed kuwa Yana fita daga gate din yafara tunanin yadda zaiyi da khadija, bazai iya zuwa da ita gida ba kuma bazai iya kaita gida ba Dan yasan zuwa yanzu mutane suna nana kofar gidan ana tunanin Ina ta tafi...
Ganin kafafun mutane sun fara daukewa dabara ta fado Masa..
"Zuwa gobe allurar da Usman yayi mata zata saketa,"
Fitowa yayi ya duba ko Ina ya hango wani gida ba'a gama Shiba Saidai ankai linter dabarar shice tabashi yakaita a ajiye zuwa gobe yasan idan ta tashi zata koma gida..
😂😂 Shaheed waishi yayi dabara, wannan kam ba dabara bace🤔🤔🤔
Haka kuwa yayi ya dauketa ya nufi cikin wajan ya ajiyeta sannan ya fice ya shiga motar shi ya tafi...
Duk Wanda mommy tasan khadija zata iya zuwan gidan shi takira shi bata nan, har A'i ta Kira tsohuwar ta fashe da kuka..
"Yanzu Maryam kiyayyar da kikewa yar nan hartakai ki salwantar da ita, to wlhy bari na Kira Amadun ya dawo ku nemomin jikata atoh"Ta kashe wayar tana kuka.....