part 19

163 9 0
                                    

*🤱 MAHAIFIYATA 🤱*

_Writing by_📚✍

*🌹 Ameena first lady🌹*

Dedicated to my sister
A'ishat Musa (initial lady)

'''special thanks for all MAHAIFIYATA fans'''💐💐💐

_page 3⃣5⃣ to 3⃣6⃣_

*_typing_*....📲

Mutanan wajan ne suka fara fadin Albarkacin bakinsu kowa da abinda yake cewa.
A haka mutanan suka baje sai zainab, nazeer, usman saikuma khadijan da Shaheed.

Zainab ce ta karaso kusada khadija tace."yakamata mu tafi gida angama lecture yau"

Ko magana batayi ba ta fara tafiya, Shaheed yabita.
"Rashin yin maganar ki kadai yabani amsar abinda nakeso naji"

Waigowa tayi tayimasa wani banzan kallo ta watsar sannan taci gabada tafiyarta.

Zainab ma binta tayi a baya ko driver basu jiraba suka hau napep.

Harsukaje gidan su Zainab bata kula Zainab ba, ganin haka yasa Zainab tayi mata magana.
"To nikuma laifin menayi da aka ki kulani"
"Bansani ba"khadija tace.
Zainab tace:.  "Kinga lokacin da kuka sasanta kanku bansani ba sai yanzu zakizo kina borin kunya tunda kinsan baki fadamin ba"

"Amma Zainab kin bani mamaki kinfi kowa sanin halina meyasa zaki yarda da zancan Shaheed"
"Khadija Nima da farko banyarda ba Amma danaga baki musaba shiyasa na yarda Amma pls yanzu fadamin meya hadaki dashi"

Labarin komai khadija ta bata sannan ta Dora da cewa.
"Bansan dalilin dayasa Shaheed yayimin haka ba, nasan kila yayine danya wulakanta ni"

"Nasan dalilin"Zainab tace
"Menene dalilin fadamin"khadija ta tambayeta.
Yanzu dai Kinga Kira drivern ki kice a nan zaki kwana inyaso mayi maganar kafin mu kwanta"

"To bloody"sannan takira driver tace karyaje daukar ta yau.

Ganin ta tafi yasa Shaheed juyawa gun su nazeer.
"Kuzo mu tafi ko"
"Yakamata kaje kabata hakuri kaga ranta ya baci"inji nazeer.
"Kyaleta kawai zamu hadu gobe"

Sunyi mamakin ganin motar daya sauya musamman nazeer dashi har yanzu a tunanin shi khadija ce tasa ya sauya motar.

A bakin titi ya saukesu ya wuce gida.

Da murmushi ya shiga part dinsu Mamee, Mamee na zaune tagama waya da Daddy saiga Shaheed ya shigo Yana murmushi.
"Yau kuma da murmushi kashigo ko wani abu ka kulla"

"Bakomai Mamee, kawai gateman ne yabani dariya" ya waske.
"Gateman ya kyauta yasa rabin Raina dariya"
"Mamee I'm hungry" ya fada Yana wani sauya fuska.
"Ohh my dear go and eat, ga shi can tun dazu na shirya maka shi a dining"
"Wow thanks Mamee"

Suna dinner su duka Amma banda daddy Wanda yaje Spain gun abokinsa alhj kabeer.

"Mamee yaushe dad zai dawo daga Spain"?     "Jibi zai dawo"
"Allah yakaimu".    "Ameen" ya tashi ya wuce part dinsa.

Bayan sun idar da sallar Isha mama ta leko dakinsu tace abbu yace su fito dinner (mahaifin Zainab).

Abbu ne yace"khadija yaushe kikazo gidan ne"
"Abbu tare muka dawo da Zainab"
"Zainab dinma banganta ba ai saiyanzu"
Barka da dawowa sukayi Masa sannan suka fara dinner.
Tare suka tashi zasu wuce daki abbu ya dakatar dasu dacewa "Ina zakuje"
"Mun koshi abbu bacci zamuyi"
"To shikenan kuje gobe zamu fita tareda ku duka".
Tsalle sukayi su duka suka rungume abbu suna murna.
Mama ce tace "Kai banasan shashanci ku wuce ku kwanta sai goben".  "A'a ba ruwanki nida yayana ne kibarsu suyi murnar su"

Dakinsu suka tafu bayan sunyiwa su abbu sallama.
Saida suka kwanta sannan Zainab ta waigo gun khadija tace "kinsan dalilin dayasa Shaheed yayimiki haka a school"?
"A'a saikin fadamin"khadija ta fada ko kallan inda Zainab take batayiba.
"Yakamata ace kingane manufarsa,Amma sai kika kasa gane Shaheed sanki yakeyi yarasa ta yadda zai biyo Miki shiyasa ya biyo Miki ta haka ya bayyana Miki a gaban yan makaranta"
Da sauri khadija ta kalli Zainab, shiru na wani lokaci sannan tace.
"Na yarda da maganar ki Saidai bazan taba yadda Shaheed ba saboda kece wacce kika sanar Dani waye Shaheed, baya taba yafewa Wanda yashiga gonar shi gashi Kinga irin wulakancin danayi Masa kina ganin duk zai yafemin ne sannan ya nuna soyayya a gareni batareda wata manufa ba"?
"Hakane Amma nida ke babu Wanda zai tabbatar da Shaheed ya manta da waccan maganar har saikin karbi soyayyar shi sannan zamu gane"inji Zainab.
"Amma kinsan bazan taba San Shaheed ba ko"
"Nasani Nima ba Ina nufin lallai kiso Shiba kawai kinuna kin amince daga nan zamu gane menene shirinsa akanki"
Shiru khadija tayi sannan tace.
"To shikenan zan gwada nayi amfani da shawarar ki"
"Atoh Saidai kiyi a hankali kar kuma azo Shaheed ya sace zuciyar ki". khadija tasan Zainab tsokanar ta takeyi shiyasa ta juya bata kulata ba.

Yau khadija ta tashi kanta  namata ciwo Amma haka Tasha magani suka tafi school.....
Har suka fito lecture ta farko kanta bai daina ciwo ba kamarma an karamara wani ciwan.
"Zainab zanje na samu waje na zauna kaina sosai yake ciwo wlhy"
"Sorry bloody naga alama muje mu zauna Dan Nima bazan iya zuwa ko Ina nabarki ba"
Suna zama suka hango Shaheed da Nazeer yau Usman baizo ba.
Karasowa sukayi da sallama Zainab ta amsa musu.
"Ki tashi muje a dubaki baidace ki zauna da cuta hakaba"
Mamaki ne yakamata itada Zainab.
Zainab din ta kalla taga alamun ba itace ta fada Masa ba.
"Bana bukata Nasha magani"
Zainab ya kalla yace.
"Ku same mu a mota Zainab keda ita" yatashi suka tafi da Nazeer.

"Babu inda zani da Shaheed" khadija tace.
"To idan baki saki jiki dashi ba ta Yaya zamu gane nufin nashi"
Shiru khadija tayi tana tunanin gaskiyar zainab fa.
"Zanje Amma Saidai idan harda ke"
Murmushi Zainab tayi tace naji tashi muje.
Shida nazeer suna mota suka hango su khadija tana tafiya a hankali kamar bazata taka kasa ba.

.......

MAHAIFIYATAWhere stories live. Discover now