38

137 11 0
                                    

🌈 *_KAINUWA WRITERS ASSOCIATION_*🤝

'''{United we stand succeed; Our ambition is entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation

     *_🤱 MAHAIFIYATA 🤱_*

_By_📚✍

*🌹Ameena first lady🌹*

'''Happy 2years anniversary KAINUWA WRITERS, Allah ubangiji yakara hada kanmu, 🤝🤝🤝'''

_page 7⃣3⃣ to 7⃣4⃣_

..... Daddy da kanshi yayi driving dinsu har zuwa kano.

Tun kafin su karaso Mommy da Mama sun rigasu zuwa tuni, tsawon awa biyu shiru babu wani likita daya fito daga cikin emergency room din.

Banda kuka babu abinda Mommy takeyi, sai sambatu takeyi.
A haka su Abba sukazo suka samesu cikin alamun tashin hankali.
Bakaramin tausayawa Mommy Daddy yayiba ganin yadda take kuka kamar ranta zai fita.
Saida suka Kuma Jan lokaci sannan wani likita ya fito fuskar shi sanye da farin glass,. Suna ganinshi sukayo kanshi da tambayar ya lafiyar khadijan.
Bai basu amsa ba sai cewa yayi su same shi a office.

Daddy da Abba ne suka nufi office din sukace su mommy su jirasu a nan.
Suna shiga office din suka nemi waje suka zauna, likitan ya fara musu bayani cikin kwarewa da iyawa.
"Kuyi hakuri, yarinyar ku zata samu lafiya inshallahu munyi bincike mun gano dama can tana tareda hawan jini, saigashi Kuma lokaci daya ta samu mummunar tashin hankalin daya haddasa mata zuciyar ta kusa bugawa"....
Wani irin mikewa Abba yayi da sauri Yana fadin. "bugawar zuciya Kuma doctor"
"A'a zuciyar bata buga ba tukun Saidai a kiyayi bugawar tata a kowanne lokaci, yanzu munyi mata allurai sannan mun kaita dakin hutu tareda saka mata oxygen saboda numfashin ta baya fita yadda ya kamata."
Sosai yanasu shawarwari daga bisani suka tashi suka fita.
Daddy ya tausaya musu yadda ya yaji abinda ya faru Dole su shiga wannan halin.
Ganin lokaci yaja yasa daddy yace zai tafi sakamakon Yana shirye shiryen dawowar dansa daga Spain.
Har bakin mota Abba ya raka shi Yana Masa godiya sannan ya tafi gida.

Kamar karamin yaro haka Khalid yake kuka jiyake inama baizo duniyar ba gaba daya, saboda bazai iya jure rashin khadijan ba, tunanin sa ya khadija zata kasance idan taji wannan labarin,.
Wayarshi ya jayo ya rubuta mata message duk da yasan yanzu sako bashida wani amfani a wajanta.
Tsananin ciwan Kai ne ya hana shi Koda runtsawa Dan koya rufe idan fuskar khadija yake gani cikin mayuwacin hali.
Kafin wayewar gari Khalid baisan inda kanshi yake ba, cikin tashin hankali suka nufi hospital dashi.

Cikin dare khadija ta farfado tareda sakin wani marayan kuka, tunanin makomar ta takeyi shikenan haka zata kare rayuwar ta kowanne saurayi Yana gudunta, idan kuwa hakane tirr da rayuwar yammatan da suke siyar da budurcin su ga mazan da basusan kimar suba, lallai yau takara jin tsanar Shaheed fiyeda kowacce rana, cikin kuka ta furta kalmar.  "Bazan iya yafe maka ba Shaheed, ka cuceni ka cuci iyayena....".ta Kuma fashewa da kuka Wanda ya jawo hankalin su aunty rahma da Zainab wadanda suka kwana tareda ita.
Lallashinta sukeyi sosai tareda kwantar mata hankali Amma Ina ko sauraran su batayi ba, Zainab ma kukan taci gaba dayi ganin khadijan takiyin shiru.
Saida aunty rahma ta nuna tayi fushi sannan Zainab tayi shiru khadijan ma ta sassauta da kukan, Saidai lokaci zuwa lokaci takan share hawaye.

Da sassafe mommy da Abba sukazo asibitin, ganin hankalin Khadija yadan kwanta yasa suma sukaji nasu hankalin ya kwanta,       A ranar aka basu sallama tareda gargadi sosai.
Gidan uncle suka wuce Kai tsaye har Zainab din.

Saura sati biyu bikin Amma har lokacin Zainab taki yarda aci gabada yimata gyaran jiki sannan ta daina shan duk wani magani da aka bata sannan da anfara maganar bikin zata fara kuka sosai ita a lallai Saidai a daga bikin.
Khadija kuwa dama tunda abin yafaru babu Wanda ya sake tilas tata shan magani gyaran jikin ne dai ganin Zainab taki yarda yasa aka lallashi khadija akan tabari ayi musu tare sannan ta yarda aka cigaba.

"Alhj meyake damunka ne tunda ka dawo naga kamar kana cikin damuwa da tunani". Mamee ta tambaye shi tana Mika Masa drink a cup.
Saida yagama sha Sannan ya ajiye cup din Yana kallonta. "kwarai kuwa Mamee, ko harkin manta labarin dana baki akan yarinyar Alhj Ahmad.."?
"A'a ban manta ba, Amma mezai sa kasa abin a ranka, tun naga aikaje ka duba Mai jikin, sannan kuma bakaine silar cutar tata ba"
"Gaskiya ne Saidai bansan dalilin dayasa nakejin abin a Raina ba, Wanda harya ja nafara wani tunanin daban"
"Tunani Kuma...? Wanne irin tunani kenan.."?
Ta tambaye shi tana Mika hankalin ta gareshi..
"Hajiya Dole duk Wanda yaga yarinyar da mahaifiyarta saiya tausaya musu, sannan kuma shi kanshi Alhj Ahmad din yagama Shirinsa tsaff dukya raba invitation din bikin yarsa, kina ganin yanzu bazai ji kunya ba kuwa idan biki yazo akaga banda Yar tasa"
"Zaiji kunya sosai, sannan kowa zai tausaya musu ga abinda akayiwa khadijan sannan ga wannan matsalar tabiyo baya"
"Shine dalilin dayasa na yanke shawarar idan Shaheed ya dawo ya maye gurbin Wanda zata aura...."
"Haba dai Alhj kaima kasan haka bazata taba faruwa ba,".
"Meyasa.."?
"Saboda kasan halin Shaheed bazai yarda ya auri bazawara ba, sannan tayaya mu zamu shawo kansa ya auri wacce bayaso"
"Duk wannan ba matsala bace, Shaheed dai mu muka haifeshi saboda haka kibar komai a hannuna gobe zanje wajan Alhj Ahmad din mu tattauna maganar, Shaheed Kuma kar Wanda ya fada Masa har saiya dawo"
"Shikenan Allah ya tabbatar da alkhairi".
"Ameen" Daddy ya amsa mata

Ganin message din Khalid yakuma tayarwa da khadija hankali, tunanin ta a wanne irin hali yake yanzu, tasan irin San da Khalid yake mata bazai iya jure rashin taba, lallai tasan yanzu Yana cikin mawuyacin hali, kamar yadda ta tsinci kanta duk wuya bazata iya cire San shi a ranta ba.

Kamar yadda Daddy yayiwa kansa alkawari safiya nayi dakansa yaje gun Abban khadija,. Sun dade suna tattauna maganar sannan abban yakira uncle Abdulmutallib da abbu (mahaifin Zainab). Suka amshi maganar hannu bibbiyu.
Daddy bai baro gidanba Saida ya bayar da dukiyar aure sannan ya nufo gida cikeda murna.

Duk sun hallara a palour sai kukan khadija kawai akeji bayan koro bayani da Abba yayi.
"Kiyi hakuri khadija, bawai Dole zamuyi Mikiba mun duba irin halaccin da Alhj attahir yayi Mana ne, sannan bazamu tozarta a idon mutane, inaso kiyimin biyayya akan wannan maganar"
Da kuka ta amsa ta amince Kuma Allah ya dawo dashi lafiya duk da batasan inda yajeba.

MAHAIFIYATAWhere stories live. Discover now