36

136 12 0
                                    

🌈 *_KAINUWA WRITERS ASSOCIATION_*🤝

'''{United we stand succeed: Our ambition is entertain & motivate the mind of readers}'''

         *🤱 MAHAIFIYATA 🤱*

_By_📚✍

   *🌹 Ameena first lady🌹*

_page 6⃣9⃣ to 7⃣0⃣_

....harta idar da sallar bataji yaron ya dawo ba, shiyasa taba idarwa tayi kwanciyar ta fara tunanin rayuwar data tsinci kanta, duk saurayin dayazo baya dadewa suke rabuwa.

Yau da sassafe su mommy da Zainab sukazo gidan, taji dadin ganinsu sosai musamman mommy data kwana biyu bata zoba.
Suna zaune a palour aka aiko kiranta, takaici ne yakamata da bakin ciki.
Mommy ce ta tilas tata saita fita..
"Mommy zuwan bashida wani amfani tunda koma waye guduwa zaiyi da zarar yaji komai"
"Eh dai dukda haka kije may be wannan Karan kiga Allah ya amsa addu'ar mu tashi maza kije". mommy ta fada tana mikar da khadija daga cinyar ta.
Badan taso ba ta shirya ta fice tanaji Zainab na tsokanar ta Amma ko kulata batayi ba ta fice.

Tun kafin takarasa taji kamshin turaren sa, Saidai bata daga kanta ta kalle shi ba, da sallamar ta ta karasa, Saida yaja lokaci sannan ya amsa mata Dan duk yagama rikicewa daga ganinta.
"Bissimilla mukarasa can".  Tayi Masa nuni da wasu fararan kujeru.
"A'a nan ma ya isa ai"
Daga haka ta gaida shi ya amsa mata cikin sakewar fuska, sai wani kallonta yakeyi duk tabi ta takura da kallon dayake mata.
"Rannan Nina aiko kizo, Saidai dayake yammata irinku Dole Saida jan aji baki fitoba, shiyasa na tafi nace na dawo tunda nagane gidan duk wayon ki"
Dariya kalmar tashi ta bata harsaida tayi murmushi.
Sosai Saida yayi kokarin sanya ta tabashi contact dinta sannan Saida ya tabbatar ya samu karbuwa yayi mata sallama Yana cewa saitaji kiranshi..
Bata bar wajan ba har Saida taga motar sa ta fita sannan ta shige cikin gidan cike da tunani iri iri a zuciyar ta..

Kwanci tashi soyayyar su tayi zurfi Sam bata kawo komai a ranta gameda shi, saima wani kaunar shi data keji yanzu.
Yauma zaune suke itada shi suna hira kamar yadda suka saba, kallanta yayi tsaff sannan yafara magana cikin nuna alamar serious zance ne.   "Khadija kusan wata daya kenan muna tare, bafa soyayya kawai nazoyi ba auranki ne ya kawo ni ba bata lokaci ba, idan har dagaske kina Sona toki bani izinin turo iyayena"..
Tunda yafara maganar gabanta yake faduwa harya gama, ta tabbatar rabuwar su yazo da zarar yaji anyi raping dinta bazai taba yarda ya aureta ba.
Hawayen da take boyewa ne suka samu damar zubowa, ganin haka ba karamin tashin hankali da rudewa yayiba. Yafara tambayar "lafiya kodai na bata Miki raine a magana, idan nabata Miki raine Dan Allah kiyi hakuri banyi tunanin zai bata Miki Raina".
"A'a Khalid baka batamin raiba ko kadan"..
"Bakya Sona ne, idan har bakya Sona bazan takura mikiba Saidai zan karaci rayuwa ta da tunanin rashinki Kuma bazan taba tunanin yaudara ta kikayi ba"

Cikin murya Mai rauni da hawaye tafara magana a hankali.  "Khalid nayi kuskuran fada maka gaskiya tun kafin soyayyar mu tayi nisa dukda hakan ya farune sakamakon duk sanda nake tare dakai kake mantar Dani duk wata damuwa"
"To fadamin meyasa kike zubar da hawayen ki akan wannan maganar".
"Khalid nasan bakasan niba budurwa bace kokuma nace labari bai sameka bane..."
Katse ta yayi ta hanyar yi mata magana. "kada kayimin karya khadija, nasani keba bazawara bace Saidai...."
Shiru yayi Yana kallon fuskar ta tagama jikewa da hawaye. "kice antaba raping dinki zan iya yarda da hakan..."
Da sauri ta waigo tana kallon shi a tunanin ta zataga wani alamar Dana sani na saninta dayayi, Saidai ma wani murmushin daya sakar mata tabbacin bai girgiza ba.
Daga mata gida yayi sannan yace. "kinyi tunanin bansani bane, kokuma kina kokonton soyayyar danake Miki bata Kai haka bane, to idan har wannan dalilin ne yasa kika kasa gabatar Dani to ki kwantar da hankalin ki ni khalid soyayyar danake Miki tafi duk yadda kike tunani"ya karasa Yana Mika mata handkerchief din dake hannun sa.
"Share hawayen ki, sannan kibani izinin turo iyayena kamar yadda na bukata a farko"
"Na amince Saidai Kuma Ina tsoron kar wani Abu ya rabamu ..."
"Wai kina nufin kar iyayena su hanani auran ki,. Hmm toki daina tunanin haka ko labarin bazasu jiba Kuma ko sunji aini zan aureki ko"
"Shikenan Allah ya tabbatar Mana da alkhairi"
"Yauwa yanzu kikayi magana"

MAHAIFIYATAWhere stories live. Discover now