*🤱 MAHAIFIYATA🤱*
*_🌈 KAINUWA WRITERS✍🏻 ASSOCIATION🤝🏻
'''{United we stand and succeed; Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
_By_📚✍
*🌹 Ameena first lady🌹*
_page9⃣7⃣ to 9⃣8⃣_
______________________
Tunda ya koma school dan zana jarabawar shi, kullum suna makale a waya koda yaushe shaheed yana kiranta idan ya samu lokaci.
Sosai shakuwa ta shiga tsakaninsu, yanzu Khadijah ji takeyi bazata iya rayuwa ba shaheed ba lokaci da dama har mamaki takeyi tayaya takamu da soyayyar shaheed..
Shima ɓangaran shaheed ɗin yanzu yasan bakaramin kamuwa da soyayyar shi Khadijah tayiba...
Kwanci tashi ba wuya yau su daddy suka zo daga Nigeria harda Meerah, sakamakon gobene murnar kammala karatun nashi.
Anyi shagali iya shagali, shaheed yasamu kyaututtuka da karrama Wa sosai a makarantar, Daddy yaji daɗi sosai kuma yayi alfahari da shaheed sosai.
Gobe zasu koma Nigeria harda su shaheed ɗin baki daya karka so kaga murna da farin ciki da sukeyi.A daran shaheed ya ɗauki Khadijah suka fita shopping na tsarabar komawa.
Suna manne da juna duk inda tabi saiya bi bayanta, ganin tana jidar kayan babies shaheed baiyi mamaki ba dama yasan hakan ce zata faru tunda zainab ta kusa haihuwa.Saida tagama sannan shaheed yace "wannan kayan fa"..?
Kallon shi tayi sannan tace "na baby nane Mana"
Shi dariya ma ta kusa bashi wai babyn ta.
Har suka ya gama biyan kudin bai sake cewa komai ba, sannan suka nufi gida.Tuni Bashir ya sanar dasu Daddy shifa yanasan meerah, kowa yaji daɗi musamman daddy da Alhj Kabir, hakan yasa aka tsayar da rana nan da wata biyar masu zuwa...
Da sassafe jirgin su ya tashi zuwa Nigeria, sai dare sannan shaheed ya ɗauki Khadijah suka koma gidan su.
Tun a daran take lallashin shaheed yakaita gidan zainab su gaisa.
Wani kallo yayi mata sannan ya wuce ɗakin sa dan yaga alamar Khadijah harda yarinta ne ke ɗawainiya da ita..
Tunda taga yayi mata haka tasan bazai kaita bama, hakan yasa ta hakura itama ta nufi nata ɗaki..Shaheed na zaune kan kujerar dake ɗakin yaji shigowarta, sam bai kalle ta ba,
Kamar munafuka haka take tafiya kamar bata so wani ya ganta, idan shi na kanta tana kwanciya yayi murmushin mugunta, gefenta yaje ya tsaya yana kallon ta ya haɗe fuska babu alamar dariya.
"Tashi ki koma ɗakin ki Malama, zan kwanta"
Tashi tayi tana kallon shi, ganin da gaske yakeyi ne yasa Khadijah tace "dan Allah kabarni wlhy tsoro nakeji sosai" ta faɗa fuskar nan Tata kamar zatayi kuka..
Taɓe baki yayi sannan yayi tsaki yabar nan a zaune bai sake magana ba.
Saida taga ya kwanta sannan itama ta kwanta tana addu'ar Allah yasa ya kyale ta..Da safe saida sukayi breakfast sannan yace ta shirya ya kaita wajan su mommy.
Da murnarta ta rungume shi harda su yimasa kiss a gefen fuskar shi sannan ta nufi ɗaki.
Murmushi yayi yana tashi yabar palourn ya nufi ɗakin sa danya shirya.Har gidan A'i da aunty rahma yakaita, Khadija taji daɗin ganin aunty Rahma da ɗan ƙaramin cikinta..
Sai yamma yakaita gidan zainab, kamar wasu yara haka suka dinga ihun murna, nazeer ne yace "kunga ya isa haka karku wahalar min da baby na"Shaheed kam tsaki yayi yana zama sannan ya gallama Khadijah hararan dayasa ta nutsu.
Hira sosai sukeyi kamar karsu rabu, har saida sukayi sallar isha sannan shaheed yace ta tashi su tafi gida.
Kamar zatayi kuka zainab ma sam bataso tafiyar Tata ba, saida yace zai barta gobe ta dawo sannan ta saki ranta..
A Mota haka ta dinga surutu, shikam murmushi kawai yake wanda shi kaɗai ne yasan ma'anar yinsa.
"Haba my ornament, sai magana nake tayi amma kai naga murmushi kakeyi ma abinka"
Sai yanzu ya kalleta sannan yace "to shikenan na daina, amma dakin adana surutun naki, gobe saikiyi min shi"
"Gobe kuma.."?
Gira ya ɗaga mata sannan yace "eh haka nace" yaci gaba da driving ɗinsa.
Itama bata sake magana ba har sukaje gida.Tun a palour ya wuce ɗakin sa, saida yayi wanka kamar Yadda ya saba sannan yaji shigowar Khadijah.,
Harta zata kwanta taji ya kirata "my breath"!
"Na'am my ornament"
Ta faɗa tana gayara zamanta..
A hankali ya tako har kusa da ita sannan ya fuskance ta.
Hannuwanta ya kamo cikin nashi, sannan yafara murzawa a hankali cikin salo da dabara.
Gaban Khadijah ne yafara faduwar me hakan yake nufi yau kuma.
Bata karasa tunanin nata ba taji ya sake kiranta sunanta cikin murya mai taushi.
Wannan karan kasa amsa tayi, jin yayi shiru yasa ta ɗago dara daran fararan idanuwanta ta kalle shi, saurin ƙasa tayi da kanta ganin idan shi a kanta.
"Khadijah meyasa bakya sona, meyasa bakyajin tausayi na, meyasa kika kasa yafemin laifin danayi miki".Tunda yafara maganar me dauke da tambayoyi yasa Khadijah tafara zubar da hawaye Masu zafi.
"Dan Allah Khadijah ki tausaya min, ki yafemin nasan nine da laifi amma dan Allah ki yafemi..."
Cikin kuka ta dakatar dashi.
"A'a shaheed wlhy bakada laifi, bakaimin komai ba, kuma karka zargi kowa da shine ya aikata min haka, dan haka kadaina zargin kanka da kaine kayi raping ɗina."Cikeda da mamakin kalamanta yake kallonta kenan tasan bashi da laifi.
"Me kike nufi kenan, kina nufin kinsan banida laifi"
Daga kai tayi alamar eh sannan ta ɗora da "dan Allah kadaina amsa laifin da sam babu shi a rayuwata"
Bai san lokacin da mike tsaye ba, "karki cemin ba'a yi raping ɗinki ba Khadija, a haka nake sanki kuma bazan taɓa dana sanin auranki a haka ba"
Cikin kuka take tabbatar masa da abinda dayake tunani.
"Meyasa haka, meyasa kika sa nake zargin wasu mutane daban, meyasa baki fadi gaskiya a gaban su Abba ba,"
"Kaine ka ɗaure kanka a gabansu abba, amm.."Dakatar da ita yayi sannan yayi hanyar fita.
"Shaheed katsaya kaji dalilin daya.."
"Bana bukatar jin dalilin iya wannan ma yayi" ya faɗa yana ficewa..
Saman bed ta faɗa tana sake rushe da kuka sosai, shaheed ma dakinsa ya yashiga ya kwanta saidai sam bacci yakasa daukar shi, tunani yakeyi akan mutanan daya saka ake ta faman basu wahala ashe sam basuda laifi dole gobe yaje yasa a sake su sannan yabasu hakuri.Kamar kullum yauma haka ta haɗa breakfast tana jiran fitowar shaheed, saidai har kusan 10:00 bai fito ba, hakan yasa ta nufi ɗakin shi.
Zaune yake da waya a hannun shi, yaki shigowar ta amma bai ɗago kai ba balle ya kalleta.
"Am.. food is ready"
"I'm full" ya furta mata kawai.
Duk yadda taso yaci abincin ki yayi karshe ma ya fice yabar gidan.Tunda ya fita bai dawo ba dawowa ba har wajan Azhar, sannan ta tura masa message zataje gidan zainab.
"Karki sake ki fita"
Ya dawo mata da amsa.Kusan kwana huɗu kenan shaheed ya fita harkar ta, kullum saitayi kuka harta godewa Allah meyasa duk lokacin da take nuna masa so yake wulakanta ta ne.
Yau kam tagaji gara ma taje fadawa su Abba kila ya fahimce ta..