🌈 *kainuwa writers association*
*_🤱 MAHAIFIYATA 🤱_*_By_📚✍
*🌹 Ameena first lady🌹*
_page 5⃣1⃣ to 5⃣2⃣_
Kuka takeyi sosai harda shesheka, wayarta ta zaro daga kasan pillow ta Kira number abbanta.
Daga can bangaren Abba Yana ganin kiran khadija ya daga da murmushi a fuskar sa, jin yadda muryar ta ta dishe da alamu kuma kuka takeyi.
"Yar abba,meya sameki"
Fashewa da kuka ta kumayi.
"Abba Dan Allah ka dawo ka nemomin MAHAIFIYATA, idan kuma ni marainiya ce nasani Dan Allah Abba pls".
Takara tana sarkewa.
"Kiyi shiru Yar abba, yau Friday, inshallahu Ina nan tafe ranar Monday kuma karna kara ji kince ba MAHAIFIYARKI bace ita...."
Hakuri da Nasiha yaci gabada yimata harya samu tayi shiru sannan yayi mata sallama akan zai dawo ranar Monday.....Zainab ta Kira nanma tayi mata Nasiha dukda haryanzu tanajin haushin khadijan da taki daukar shawarar ta.
Kashe gari tun safe Shaheed yake aikin turawa khadija message Saidai kamar yadda yayi tsammani ba reply.
Yanzu ma khadija na kwance a palour tunanin Shaheed ne ya fado zuciyar ta, wani murmushi tayi har zuciya.
"Lallai Shaheed ya damu da ita meyasa takasa hakura nema Wai..? Meyasa take yaudarar kanta akan zata iya rabuwa da Shaheed bayan tasan bazata iyaba, lallai zata hakura Amma sai lokacin data dibar Masa ya cika saita tabbatar zai sauya halinsa tukun"Da wannan tunanin ta tashi ta nufi dakinta..
Har dare bataga giftawar Mommy ba, dakin mama uwani ta nufa Dan tambayar lafiyar mahaifiyartata.
"Mama uwani sannu da aiki"
"Yauwa khadija, an fito kenan".
"Eh tun dazu Ina palour Saidai ban giftawar Mommy ba shine nace barina tambayeki ko lafiyarta klau"
"Eh to dazu natanta ta fito ina tunanin dai kalau take"
"To Mama uwani nizan je na kwanta kafin akira sallah"
"To ayi bacci lafiya"
Ta nufi dakinta ta kwanta.....Da la'asar driven tana zaune a palour still driven ta ya shigo ya tsugunna.
"Bala ya akayi"
"Dama cewa nayi narina sanar Miki, mahaifina ne bashida lafiya shine aka kirani ake fadamin shiyasa nazo na sanar Miki abani izini zanje gida""Haba bala mahaifi fa kace tayaya zan hanaka zuwa, karka damu kaje kawai zan dinga hawa napep Ina zuwa school din, Kuma Allah yabashi lafiya"
"Ameen nagode, ga key din motar"
Karba tayi tana cewa ya jirata.Kudi basa tace yayi hakuri ba yawa, yayi kudin mota dasu, sannan yayiwa mahaifin nasa sannu..
Godiya yayita zubabawa sannan ya tafi.
Taji tausayin shi sosai dukya bi ya rude.....Har dare bataga Mommy ba Amma bata sake tambayar kowaba taje
Shaheed kuwa tunda khadija taki daukar wayar shi, sannan taki yarda su hadu yafara tunanin. "kodai da gaske khadija kallon Dan iska takeyi masa, indai kuwa hakane ya tabbatar bazata hakura ba Dan yafi kowa sanin halin khadija".
Da wannan tunanin bacci ya sace shi....Yau Sunday yanayin garin sun tashi da iska dukda daman damuma ce Amma Sam ba hadari sai iska mai dadi da take kadawa.
Khadija kuwa yau tatashi cikin farin ciki kamar wacce aka biyawa hajji.
Tunani takeyi meyasata cikin farin ciki haka kodan gobe abbanta zai dawo ne...?Har la'asar taje tayo shopping, abbanta bai kirata ba.kiran wayar shi tayi.
Bayan sun gaisa tace. "Abba ka fasa dawowar ne"
"A'a khadija gobe on my way tomorrow inshallah"
"To Abba Allah yakaimu"
"Ameen yar Abba"
Tayi Masa sallama ta kashe wayar.Tunda ta fita shopping din saida akayi sallar magrib sannan ta nufo gida...
Bayan tayi sallar magrib ta Haye saman bed ta kwanta..
Kwantawar ta kenan taji alamun anbude kofar dakinta..
Juyowa tayi Dan a tunanin ta mama uwani ce..
Kamar an tsokareta ta tashi ganin mahaifiyar ta..Kasa ta sako ta tsugunna gabanta na faduwa jikinta har rawa yake..
Mommy saida tagama karewa yartata kallo sannan tace..
"Ki tashi ki shirya yanzu kije rijiyar zaki gidan Hajiya salamatu ki karbomin sakona, kice Nina turo ki"
Wannan itace ranata farko da magana ta mutumci ta shiga tsakanin su, hakan yasa bakin khadija har rawa yake yi.
"To Mommy, am..Amma driver na bayanan Saidai ki hadani da naki muje"
"Tun farko wannan dalilin ne yasa nakasa sakewa dake, saboda banasan raini, Amma gashi tashin farko zaki nunamin ban isaba"....
Da sauri tafara bata hakuri..
Tsaki tayi ta fice daga dakin...Wani wawan tsalle khadija tayi ta fada saman gadonta, tayi saurin lalubo wayar Zainab...
"Zainab yau mommy tayimin magana," tafada kukan murna na subuce mata...
"Da gaske khadija". Zainab itama ta fada da murna..
"Eh mana yanzu haka ma aikena tayi rijiyar zaki gidan kawarta, gashi drive na baya nan, pls idan driven ki Yana nan nazo yakaini"
"Wlhy baya nan yau kwana biyu kenan, Amma ke kinsan gidan"
"A'a Saidai nasan matar"
"Khadija kawai kidaina bata lokaci kije ki hau napep kafin dare yayi""To Zainab"
Katse wayar tayi da dauki hijjabinta ta saka da dauki wayarta ta fice...
A palour ta samu Mommy ta tsugunna tace "mommy na tafi saina dawo"
"To" kawai mommy tace mata...Tunda sugama waya da Zainab,. Zainab har zata ajiye wayar saikuma wata dabara tazo mata, murmushi tayi sannan ta danna wasu lambobi..
Daga can bangaren Shaheed da Usman suna zaune a bakin masallaci yaga Kiran Zainab, tunda yaga Kiran yasan dalilin..
"Hello Shaheed, yanzu khadija takira ni Mommy ta aiketa rijiyar zaki wajan kawarta hajiya salamatu ,kuma driven ta bayanan, pls kaje ka kaita daga nan saika bata hakuri"
"Thanks Zainab"
Yafada Yana katse Kiran .
Usman ya fadawa,. "kaje ka daukota zan jiraku a rijiyar zakin". Yafada Yana kashewa Shaheed ido...
Da alamu akwai fa abinda su Shaheed zasu kulla🤔🤔🤔🤔
....tafiya takeyi harta karaso bakin titi, saikuma ta tuna batafa taba zuwa rijiyar zaki ba.
Wayarta takuma cirowa ta kiran Zainab..
"Zainab bani address din rijiyar zaki"
"Rijiyar zakin ce baki saniba kome..?
"A'a bantaba zuwa ba ai"
"Kawai...?Kafin ta karasa taga wata red din mota ta Parker..
Glass din motar ya sauke a hankali Shaheed tagani a wani kallonta kamar bai taba ganinta ba..Ba karamin bugun zuciya yajiba da ganinta, tayi kyau dukda ba kwalliya a fuskar ta Amma tamishi kyau sosai, take wata sabuwar soyayyar ta ta rufe shi...
"Zainab Ina zuwa zan kiraki"
Ko amsa bata tsaya jiba ta katse Kiran...Ko kallon shi batayi ba ta dauke kanta kamar bata ganshi ba...
Fitowa yayi ya zagayo, ya tari gabanta ya harde hannu..
"Har yanzu fushin ne baki gama ba, kin ganni kin wani share zakice baki ganni bako"
Bata kula Shiba hakan yasa tadan tabe baki.
"Kinga darefa nayi, nibawai wajanki nazoba, hajiya salamatu ce tace nazo na daukeki tunda tayimin kwatance nagane kece ai"Shiru Zainab tayi tana tunanin karya Shaheed yakeyi "Amma idan karya yakeyi Yaya akayi yasan inda zani". Sam bata kawo Zainab ce ta fada maiba..
"Kingama dare fa yi yakeyi ankusa Kiran Isha, idan zaki Bismillah"
Ya fada Yana bude mata sit din gaba..Ba musu ta shiga.
"Ok bazaki saki fuskar takiba, dukda nasan kinyi kewata shine kike wani makewa"
"Surutu zaka yi na fitar maka a motar ka, kokuma tafiya zamuyi". Tafada tana hararan sa..
Cije lebensa yayi, sannan yayiwa motar key.....