🌈 *Kainuwa Writers Association*
*🤱MAHAIFIYATA 🤱*
_By_
*🌹Ameena first lady🌹*
Wattpad @Ameenafirstlady_page 7️⃣9️⃣ to 8️⃣0️⃣_
Tun kafin su karasa daddy ya Kira abban khadija ya sanar dashi suna hanya tareda sirikin su, abban yace suma suna gidan shida mommy.
Zainab ce zaune tareda khadija tana ta faman lallashinta tayi ko light makeup ne Amma firr Taki saima kuka data farayi tana tuna da Khalid din ta ne da babu Wanda zai tilas tata saima tayi kwalliya.
Zainab cikin fushi ta nufi palour, ga mamakin ta saita ga abbu da mama (iyayenta) suma duk a palourn.
"Sannu da zuwa mama da abbu"
"Yauwa Zainab, Ina khadijan"..?Aunty Rahma ce tace. "khadija na can tana kwalliya yau angon nata zaizo"
"A'a aunty ba kwalliya take ba nayi nayi da ita tayi ko light makeup ne Amma takiyi""Wannan wanne irin shashancine khadija ta tsira Wai, shikenan baza'a fada mata magana taji ba, bari naje na sameta tunda ita kunnen Kashi gareta". Aunty Rahma ta fada tana fada kamar zata ari baki.
Tana shiga dakin ta iske khadija a zaune ta rafka tagumi sai hawaye take, ga kayan da Zainab ta zabo mata Dan tasaka nan a gefe batada alamun shiryawa.
"Khadija wato bazaki dauki shawarar danake baki kullum ba ko, nasani ban isa na saki kona hanaki ba Amma ko bakomai yakamata ki shirya kodan kar iyayenshi suyi tunanin wani Abu, tunda harda su yake tafe.."
"Allah aunty kiyi hakuri, wlh ba Ina nufin baki isa kisani bane, jinakeyi gabana na faduwa Sam bansan zuwan su kwata kwata, Amma zan shirya Dan Allah karkiyi fushi Dani"
Jikin anty Rahma yayi sanyi dan ta fahimci yadda khadijan takeji Saidai ba yadda zasuyi Dole su hakura ayi auran kodan bakin mutane.Da taimakon aunty rahma ta fara shiryawa, light makeup tayi tasaka wani light pink din materials riga da skirt, sosai ya amshe ta tayi kyau sosai kamar wata sarauniya sakamakon gyaran jikin da suka sha itada Zainab.
Saida tagama Shirin sannan aunty rahma ta fice ta turo mata Zainab Dan karta cigaba da kukan ta bata kwalliyar.
A palourn Mama, Mommy, aunty rahma sai uncle Abdulmutallib daya shigo yanzu.
"Inasu abban khadijan naga tare kuka fita ai"
"Eh sunje dauko A'i Wai zata zo taga sirikinta kinsanta da rigima"..
"To Allah yasa su karaso kafin su alhj attahir din su zo" mama tafada.Kafin su Alhj attahir su karaso, su Abba harsun dawo tareda A'i.
Palourn ya cika sai hira suke cikeda nishadi, babu Wanda ba hallara ba a palourn.
Zainab da khadija kuwa suna daki, Zainab nayi mata Nasihar karta bada iyayensu a wajan mutanan nan ta nuna batasan wanna auran.
A mota kuwa Shaheed kamar ruwa ya cinye shi, Sam baya saka musu baki a hirar da suke.
Daddy ne ya waiga bangaren Shaheed din jin yayi shiru.
"Shaheed ya kayi shiru, ko akwai matsala ne"
Carab Meera ta amshe zancan. "a'a daddy babu wata matsala Yana tunanin yadda zai tsara jarumar tashi ne..."?
Wata uwar harara ya maka mata tayi saurin tsuke bakinta tana kallon gefe danma karya bugeta.
Daddy dariya yayi yace "Wai hakane Shaheed.."?
Mamee ce ta shigar Masa "rabuda ita Alhj tsokanar shi take". Sannan ta waiga bangaren Shaheed. "Shaheed bafa kayi mata tsarabar komai ba.."
"To kodai mutsaya yayi mata bai kamata ango yaje hakaba..""No Dad muje kawai gobe zan koma ai, sainayi mata kaga yanzu dare ne gaisawa kawai zamiyi"
"To shikenan hakan ma yayi ai"
Da haka daddy ya mayar da hankalin shi kan driving din dayakeyi.