part 24

146 10 0
                                    

*_🤱 MAHAIFIYATA 🤱_*

_by_📚✍

'''Ameena Musa'''
*🌹Ameena first lady🌹*

_page 4⃣5⃣ to 4⃣6⃣_

______________________

Tunda ya fito daga office din nazeer yagane ransa a bace yake harya karaso.
A mota nazeer ya dinga tausar sa akan yayi hakuri khadija tana sanshi kuma ganinta da wani hakan bawai Yana nufin bata sanshi bane....
Gaba daya haushi ya kamashi gani yake ba laifin salim bane laifin khadijan ne.

Yau da azahar salim yaje gun khadija ya taki sa'a ta fito Saidai tun daga yanayin fuskar ta yagane bataso fitowan ba.
Sallama tayi Masa suka gaisa daga haka taja bakinta tayi shiru.
"Khadija waye wannan Wanda ya ganmu tare dame rannan"
"Lafiya kake tambayar waye"
"Ina San sani ne"
Shiru tayi bata basa amsa ba.
Ganin haka ya kawar da zancan.
"Meyasa baki nemeni ba khadija tun ranar fa bansake ganinki ba sai yau, yau dinma Nina nemeki".
"Ko baka nemeni ba salim nizan nemeka tunda akwai maganar danakeso muyi".
"Ok fadi inajinki"
Saida ta tattara nutsuwar ta sannan tafara yimasa bayani.

"Salim nasan bazaka yaudari kanka ba kasan bada Kai kadai nake soyayya ba, kuma lokaci yayi daya kamata na fada maka gaskiya, kayi hakuri bawai bana sanka bane Saidai zuciya ta tafi karkata ga wani daban Ina fatan bazaka dauki hakan a matsayin yaudara ba"
Tunda tafara maganar yake sauraran ta Saidai tunda ya fahimci inda ta dosa kwakwalwar sa ta daina aiki, bai San karshen zancan ba Saidai ya fahimci abinda take nufi.
Ko magana bai mata ba ya nufi motar shi, da kallo tabi shi tana tausaya Masa Dan tasan irin San salim yake mata.
Salim sake sake yayita yi a mota.
"Lallai saiya rama yaudarar da khadija tayi Masa Sam baisan wani abu hakuri ba a rayuwar sa zata gane me ake nufi da yaudara very soon"

A gida nazeer ya sauke Shaheed Dan yau yace bazai koma wajan Usman ba.
A daran ranar Shaheed ya Kira khadija, kuma a daran suka shirya kamar babu abinda ya faru tsakanin su Saidai bata fada Masa yadda sukayi da Salim ba.

Haka rayuwa taci gabada tafiya cikin yardar Allah, kawancen ta Zainab sai abinda yakaru Dan sun zama kamar wasu twins ne, Saidai har yanzu babu jituwa tsakanin ta da mahaifiyarta Sam harta fawwalawa Allah lamarin, soyayyar ta da Shaheed kuwa sai abinda ya karu.
Bangaran Usman kuwa har yanzu bai daina zuga Shaheed ba.

Shaheed ne tareda Usman a dakinsa.
Usman ya tashi zai tafi.
Ina zakaje kuma by now"
"Aika San yau kwana biyu bamuje club ko"
"Ohh I forget but kabari gobe sai muje"

"Ok shikenan sai goben zanzo mutafi"
Tunda safe yake neman layin khadija Amma a kashe har dare,  Usman yazo zasu tafi ya kuma gwada Kiran yaji busy kusan one hour,.
Yanayin sa yafara sauyawa ranshi ya baci sosai.
Usman ne ya kalle shi yace.
"Yanaga ka sauya daga Kiran waya kaji busy"
"Bazaka gane bane Usman duk lokacin Dana kirata naji busy ji nakeyi kamar da wancan banzan take waya"
"To kazo muje club din idan muka dawo saikaje ka ganta kawai"
Badan yaso ba suka tafi shida Usman.

Khadija bayan tayi sallar Isha takira Zainab suna cikin waya Kiran abbanta ya shigo.
" Zainab Ina zuwa Abba Yana kirana"...
"To Saida safe bloody" sukayi sallama ta daga Kiran abbanta.

Ganin hankalin Shaheed a tashe yasa Usman yace.
"Ka kara gwada Kiran mana"
Wayar ya kuma dauka ya danna number khadija.
Still busy.
Ai take ransa ya baci bai kara magana ba har sukaje club.
Bayan tagama waya da abba harta ajiye wayan taji karar Kira again.
A tunanin ta Shaheed ne Amma ganin bakuwar number sai tadaga bata kawo komai ba a ranta.

"Hi" taji muryar wata budurwa a bayanta, waigawa tayi taga da ita take....
"Hi" ta mayar mata da murtani. "Amma pls bangane da wacece nake magana ba"
"Ai bazaki ganeni ba"
" Ko Meyasa
"Amma nayi"
"Sanin wacece bashine yasa na kirakiba nayi mamakin ace kina nan a kwance amma saurayin ki Yana club by now"

"Saurayi na kuma"
Khadija ta fada da mamaki sosai a tareda ita..
"Yanaga kinyi mamaki ba kece wacce Shaheed attahir Hashim zai aura ba duk dai na ba'a yi auran ba ko"
Bata bata amsa ba saboda gaba daya bakin ciki ne ya cikata.
"Eh nice Amma bana tunanin nawa Shaheed din kika gani"
"To tunda baki yarda ba shikenan sai anjima"
Harzata katse Kiran khadija ta tsayar da ita.
"Pls kozaki iya fadamin wanne club ne"
Kwantancen club din tayimata sannan ta katse Kiran.
Da sauri ta tashi tadauki hijjabinta tana kallon agogo 8:5pm Amma bata fasa fita ba.
"aikuwa idan ta tabbata Shaheed ne lallai ya yaudareta dayace bazai kara zuwa club ba kuma ba ita bashi tunda bazai daina wannan mummunar dabi'ar ba.
Napep ta tare tayi Masa kwatance suka tafi.

Usman ne yacewa Shaheed "wlhy Kai dai kaji kunya, yammata nawa ne suke like maka Amma baka kulasu wayayyu yan birni masu kudi da aji Amma kaki ka makalewa wacce bata sanka batasan kanayiba, kuma karka manta irin abubuwan da tayi maka ta wulakanta ka ta mareka a gaban yan makaranta Amma duk manta" yaja tsaki Yana zukar taba abinsa.
Da alama maganar Usman tayi tasiri a gunsa.
"Usman Ina Santa Saidai dole zan cireta a Raina kuma maganar rama abinda tayi min ai ban fasa"

Wata budurwa ce Tasha bleaching ta matso kusa da Shaheed cikeda kwarkwasa kana ganinta kaga gogaggiyar yar duniya......
Napep na sauketa tace yajira ta yanzu zata fito sannan ta shige club.
Bata ganin komai saboda yanayin kalar hasken kwan fitilar dake wajan mata da maza sai sheke ayarsu sukeyi da badala abinda yafi bata haushi mata sunfi mazan yawa tsabar rashin aji.
A can tsakiyar mutane tagano Shaheed da wata kamar zasu shigewa juna, tsakanin kishi karara ya bayyana a fuskar ta ranta ya baci, jiki a sabule ta karasa wajan.
Sai saukar mari budurwar taji a fuskar ta waiga da zafin nama.
Ganin macece yasa ta Mike ta fara aika mata da maganganu na rashin mutumci.
"Akan me zaki mareni Dan kawai kin ganni tareda da wannan Wanda bai gama wayewa ma a harkar ba shi...."
Bata karasa ba khadija ta kuma bata wani marin.
fitilar mai haske wajan ya gauraye dashi anan ta lura da yawan mutanan wajan.
Waigawa tayi bangaren Shaheed Wanda ya kame kamar mutum mutumi.
"Amma Shaheed kabani mamaki, a aikin banza kake zuwa irin wannan wajan kana zubar da kimar ka da darajar ka, ban taba yarda da sanin duniyar taka yakai hakaba kuma Inaso kasani daga yau babu soyayya tsakani na dakai Dan bazan iya soyayya da Wanda baisan darajar mace ba"
Juyawa tayi zata tafi ya tare gabanta.
"Ki saurareni khadija ban..."
"Bazan saurare kaba Shaheed Dan niba yar iska bace, dazan cigabada tsayawa a nan ba"

Babu abinda Shaheed ya tsana irin a kirashi da Dan iska, ranshi yayi matukar baci ya dago jajayan idanuwansa.
"Mekike nufi dake ba yar iska bace, kenan ni Dan iska ne ba". Ya taka yakarasa daf da ita har saida gabanta ya fadi.
"Kalmar iskanci kika sani a baki Amma zakiyi mamaki akan wannan kalmar da kike jifana da ita"
Tsaki tayi ta wuce ta gefen shi ta.
Har taje gida tana zubar da hawayen bakin ciki shikenan ta rasa Shaheed dinta Dan batajin zata iya rayuwa dashi a haka.

Shaheed kuwa tana fita ya dafe kanshi dayake sara Masa, ganin haka Usman ya jashi suka tafi gida.
A mota Usman yadinga bashi hakuri da ziga shi.
"Kaga irin abinda nake fada maka ko, ai gashi yanzu ka gani".
Bai tanka Masa ba Dan bayajin zai iya magana a lokacin sakamakon yadda garin yake juya Masa.......

MAHAIFIYATAWhere stories live. Discover now