🌈 *_kainuwa writers association_*
https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation
*_🤱 MAHAIFIYATA 🤱_*
_By_📚✍
*_🌹 Ameena first lady🌹_*
_page 5⃣9⃣ to 6⃣0⃣_
Yana ganin Dad ya fita ya kwanta ya lumshe idanuwan shi da sukayi Masa nauyi da zafi, kwakwalwar sa takasa daukar kalaman da Daddy yayi Masa yanzu ya kasa gasgata maganar Dad din...
"Meyasa ban mayarda khadija hargida ba? Meyasa na tafi na barta waye ya aikata mata wannan mummunan Abu....?
Wasu zafafan hawaye ne suka zubo daga idanshi,.
Bai San lokacin da Meera tazo kanshi ba saiji yayi tace.
"Yaya Shaheed meya faru lafiya...?Da dabara ya goge hawayensa sannan ya tashi zaune. "Meera wllh ina santa kamar yadda nake San kaina, inajin bazan iya rayuwa idan babu ita a kusa Dani ba, ba'a iya zuciyata nakejin Santa ba har cikin jikina, khadija itace rayuwata......"
Kasa karasawa yayi hannuwan shi sarke cikin na Meera...
"Yaya Shaheed kayi hakuri kaje ka sanar mata da soyayyar ka koma wacece nasan zata soka pls ka daina damuwa akan wannan"..
"Meerah...". Shiru yayi Dan baisan yadda zaiyi mata bayanin abinda ya faru ba, tashi yayi ya tafi part dinsa Yana tafiya Yana tangadi a haka ya karasa...Har yanzu khadija bata farka ba, itama Zainab tana can an daura mata drip.
Zaune suke a room din da aka kwantar da khadijan kowa ka gani hankalin sa a tashe yake musamman Abba...Kiran wayarsa akayi ya daga da sallama,
"Ok Alhj ganinan fitowa"Harya Kai bakin kofar fita ya waigo ya kalli khadija ya girgiza Kai sannan ya fita...
Sosai ya saki fuska ganin babban mai gidan sa dakansa yazo duba yarsa, shi kadai yazo a motar ko driver babu..
"Alhj Kai kadai kuma, baikamata kafito Kai kadai ba koni daka Kira ai zanzo na taho dakai"Murmushi yayi yace. "Karka damu aigashi harna zo ko"
Saida suka gaisa sannan yayi Masa jagora har dakin da aka kwantar da khadijan, ba karamin tausayawa khadija yayiba ganin yarinya ce kuma da alamar Tasha wahala sosai....
Saida yakusa 1hour sannan yace zai tafi.
Har waje Alhj Ahmad ya rako shi sannan yace.
"Alhj inaso ayimin alfarma ayi replacing dina da wani a wajan aiki, saboda inaso na bawa yata kulawa"
"Har na tsawon wanne lokaci kakeso dawowa""2 month"
"To ba matsala"
Da haka sukayi sallama ya tafi...Sai bayan azahar sannan khadija ta fara motsa idanuwanta...
"A hankali ta bude idanunta farare karr ta sauke a kan abbanta, da sauri ya matso kusa da ita..
Itama da hanzari tayi kokarin tashi zaune, wata siririyar kara ta saki sakamakon azabar da taji ta kasanta.."Sannu khadija, kwanta basai kin tashiba,,, Abdulmutallib jeka Kira doctor"
Har Dan gudunsa yakira doctor din suka taho tare."Abba meya sameni,..? Aunty Rahma meya kawo ni asibiti"
Babu Wanda ya tanka mata kowa ya kawar da kansa gefe.
Ganin haka yasa khadija tafara tunanin abinda ya faru.
Wani marayan kuka ta saki sakamakon tuna abinda ya faru tsakanin ta dasu Shaheed..
Kuka takeyi sosai kamar an zare mata rai babu Wanda yayi kokarin hanata.
"Shikenan Shaheed yagama Dani, ya cuci rayuwata ya yaudareni da soyayyar danake Masa" ta fada a ranta...
Aunty Rahma sai lallashinta takeyi Amma takasa daina kukan sosai takejin daci a ranta...... "Shaheed kuwa harya shiga part dinsa ya kwanta tunanin khadija yakeyi Sam yakasa yarda ba laifin sa bane,
Key din gidan da Dad ya mallaka Masa ya dauka ya fita.Bai dauki motar Shiba ya tafi a napep, har zuciyar shi ya dauri aniyar babu Wanda zai San inda yake.....
Sosai Abba yake yiwa khadija nasiha Mai ratsa jiki harya samu tayi shiru, sannan mama ta hada mata tea Mai kauri kamar yadda doctor ya umarta...
Saida suka kwana biyu a hospital sakamakon ciwan ciki daya riketa doctor yayi musu bayani "gaskiya sakamakon allurar gneiss da akayi amfani da ita shiya haddasa mata ciwan ciki Wanda yanzu dai zamu hada mata magunguna duk lokacin da ciwan ya tashi saiku neme ni"
"Doctor na wata matsala gameda ciwan cikin,"
"Eh babu karja damu, allurar ce ta jawo haka shiyasa aka hana amfani da ita""To mun gode doctor"
A ranar aka sallame su daga asibitin, itama Zainab a ranar aka sallame ta.
Abu kamar wasa yau kwanan Shaheed biyu baya gida tun daddy Yana tunanin Yana gidansu Usman harya Kira Usman da Nazeer suka tabbatar mai baya wajan su, nan fa hankalin su daddy yayi matukar tashi aka fara neman Shaheed sosai..
Wasa wasa har gidajan radio neman Shaheed Amma babu labarin sa, hankalin su Mamee da daddy yayi matukar tashi.
Daddy ne zaune a palour shida Mamee da Meera.
"Ina Shaheed ya tafi meyasa yabarmu lokacin da muke bukatar sa" Mamee ta fasa hawaye na zubo mata.
"Koma Ina ya tafi nasan zai dawo, kuma Yana dawowa zan tura shi Spain kamar yadda kika nemi shawarata"
"Dad wlhy akwai abinda yake damun yaya Shaheed....!
Saida Meera ta fada musu duk yadda tayida Shaheed rannan sannan ta Dora da. "Ina tunanin Yaya Shaheed soyayya ce sular barin shi gidan nan"