*🤱 MAHAIFIYATA🤱*
_By_📚✍
*🌹Ameena first lady🌹*
*_🌈 KAINUWA WRITERS✍ ASSOCIATION_*🤝
https://www.Facebook.com/, kainuwawritersassociation
_page8⃣7⃣ to 8⃣8⃣_
...Da lallashi mommy tasa ta shirya ta nufi gidan uncle abdulmutallib, tun kafin taje zainab ta dameta da kira.
Gaba daya shaheed ya rasa sukunin shi musamman idan ya tuna a yanayin dayaga Khadijah da Khalid tabbas yasan masoya ne hakan yake daɗa sawa yake jin wani baƙin ciki da tashin hankali.
A yau su Bashir da Alhaji Kabir sukazo Nigeria bikin shaheed, tunda Bashir yaga shaheed yagane yana cikin wani yanayi saidai bai nuna masa yagane ba.
Har suka zo gida sam shaheed yakasa sakewa ga lokaci sai kurewa yakeyi amma bashida alamar shirya wa.
Bashir ne Ya kalle shi ta gefen ido sannan yayi murmushi dan yasan halin mutumin nashi akwai saurin fushi da zuciya.
Saida ya gama haɗa coffeen sa sannan ya fuskanci shaheed daketa huci shi kaɗai.
"Bazaka shirya bane shaheed ga nazeer sai kiranka yake yi kuma fa saura 1hrs a ɗaura auran kamata yayi yanzu kana cikin abokai kana farin ciki..."Bai kula shiba harya gama jawabin shi sannan ya ɗago kansa ya kalli Bashir.
"Bashir ina tunanin zan fasa auran nan kawai""Whattt.". Bashir ya fada yana ajiye cup ɗin hannun shi.
"Shaheed mai yake damunka Are You serious.."
"Yes bashir, ina cikin hankali na, kasani ina san Khadija fiyeda yadda nake San kaina saidai kuma ita na fahimci akwai wanda take so..""So what dan tana san wani, look malam ka ajiye maganar kishi da batun bakasan raini ka ajiye shi gefe ka koyawa matar ka yadda zata soka.."
Shiru yayi yana sauraron Bashir harya gama sannan yayi wani malalacin murmushi baice komai.
Bashir ɗinne ya sake cewa "saboda haka katashi ka shirya mu nufi wajan auran, sannan ka saki wannan fuskar taka plss"
Shawarar Bashir yabi ya tashi ya shige bathroom...Khadija jiki a sanyaye takeyin komai kowa ya ganta yasan tana cikin damuwa duk yadda kewayenta suke tsokanar ta sam takasa sakewa karshe ma sai hawaye ne suke barazanar suɓuce mata...
Da wayo zainab ta jata ɗakin aunty rahma ta fara yimata faɗa sosai.
"Gaskiya Khadija idan bazaki sauya ba to zanje na samu Abba na faɗa masa halin da kike ciki, wannan ai sam bai kamata ba ace kowa saiya san bakya san auran nan.."
Kuka ne yaci ƙarfin Khadijah tafara magana cikin sarƙewa.
"Zainab kiyimin uzuri wlhy nakasa manta wa da Khalid, sannan ina tunanin irin zaman dazan yi da shaheed bayan abinda ya aikata min a baya kinajin zan iya sakewa dashi harna soshi..."?
"Kinga karki sawa kanki wannan tunanin dan Allah Khadija ki manta da batun abinda ya faru a baya, saiki godewa Allah wanda ya aikata Miki aikin shi zaki aura bazai taɓa yi miki gori ba tunda yasan a yadda ya sameki sannan kuma bada yardar kiba, amma wlhy da wani kika aura ko Khalid ne watarana saiya goranta miki musamman da bashida masaniya akan komai..."
Girgiza kai kawai khadija tayi sannan ta share hawayenta...
Ganin ta saki fuskar ta yasa zainab ta jata suka koma cikin Mutane...Abokan su shaheed duk sun hallara kowa da kowa motocin dazasu tafi dasu duk sunyi ready, nazeer sai kai kawo yakeyi cikin abokan su dan shaheed kawai suke jira..
Shaheed ne ya fito cikin wata dakakkiyar shadda fara ƙal sai ɗaukan ido take hular kanshi ma fara ce ƙal, yayi shigar white komai ba karamin kyau yayiba saiya fito da asalin kyaun shi sai zuba ƙamshi yakeyi..
Nazeer ne ya kalle shi yace. "malam ka ɓata mana lokaci fa.."
Murmushi yayi yana faɗin "gani na fito mu wuce kawai."
Ba ɓata lokaci suka nufi wajan taron masha Allah kowa ya hallara dama su kawai ake jira suna zuwa aka fara gudanar da ɗaurin auran...1 dai dai ɗaruruwan jama'a suka shaida auran Abdulmalik Attahir Hashim (shaheed). Dana Khadijah Ahmad Ibrahim.
Sannan aka daura nasu nazeer Yusuf da zainab kabeer mashi,. Mutane har ba'a magana.
Da kyar na iya hango shaheed yanata faman ƙarbar Allah sanya alkhairi bakinsa sam yakasa rufuwa tsabar farin ciki da annashuwa....Tun 4:00pm aka gama preparing din wajan dinner, har shaheed saida yazo yaga wajan yayi matukar tsaruwa da kyau..
Saida sukayi sallar isha sannan luccy makeover tafara aikinta na tsantsarawa amare kwalliya ta birgewa.
Saida ta ɗauki lokaci tana kwalliyar sannan tagama suka fara shirya wa...Cikin ƙanƙanin lokaci suka gama shirywa cikin light blue na kayan amare.
Masha Allah Sam Khadija bazaka taɓa ganeta ba kamar wata baturiya tayi harta gaji duk mutanen wajan saida suka furta masha Allah musamman ƙawayenta...Nazeer kam Sarkin zumuɗi tuni yagama shiryawa shaheed yake jira tareda manyan abokan su.
Cikin light blue din shadda bugaggiya ya shirya ya haɗu iya haduwa zam kamar shi da larabawan Sudan ta fito sak.
Yauma yana fitowa tareda Bashir nazeer ya ce "malam kai komai sai an jira ka, duba agogon ka kaga what time now"
Murmushi yayi yana duba gold Watch ɗin dake daure a tsintsiyar hannun shi wanda ya kwanta jikin lallausar fatar shi,. "Sorry nazeer banyi tunanin lokaci yaja haka ba"
Tsaki yaja nazeer yana faɗin. "eh dama mana ai bazaka lura ba"
Dariya abokansu sukayi musu sannan suka ɗauki hanyar gidan uncle ɗauko amaren su...Tun kafin su karasa zainab take kiran nazeer suna jiran su dan duk antafi su kaɗai ake jira da sauran ƙawayen su da suka rage...
Suna zuwa su zainab suka fito, shaheed kuwa ƙarbar key ɗin motar yayi yaba Bashir yayi driving ɗinsu su biyu kawai..
Tunda ta fito ya kafeta da ido duk ta haske wajan sam bai bari tagane ita yake kallo ba, saima haɗe fuska dayayi shi ala dole tsare gida.
Gani yake kamar ita ƙadai kowa ke kallo saboda haka da sauri ya buɗe mata sit ɗin baya ta shiga sannan shima ya shiga bayan.
Ganin shigowar shi ne yasa Khadija ta kalle da mamaki saikuma tafara kokarin buɗe motar ta fita.
Jin motar taki buɗewa ne yasa ta waigo tana kallon shi, kasa yimasa masifa tayi yadda taga ya haɗe fuska sannan ga wani kwarjinin shi daya saukar mata lokaci guda.
Nunawa yayi kamar bai san tana kallon shiba, saikuma ya kalle ta ya ɗaga mata gira. "Yadai kinaso ki fita ne.."
Kaɗa masa kai tayi alamar "eh zan koma wajan zainab ne..""Itama tana tareda nata mijin, sauran motocin duk maza ne aciki,.."
"Koda yake ainaga kin iya keɓewa da saurayi ko..."?
Ya faɗa yana jiyar da kanshi daga gareta..
Har cikin ranta taji maganar daya faɗa mata kuma tayi niyyar saita mayar masa da amsa dai dai da tambayar dayayi mata amma ba yanzu ba..Ba wanda ya sake magana Bashir dake gaban motar ya fara driving yana murmushin dramar su, "su kuma haka nasu salon soyayyar yake kenan". Ya faɗa a zuciyarsa..
Har suka je hall ɗin babu wanda ya sake magana cikinsu, tuni su nazeer da zainab sun shige, shima Bashir yana yin parking ya fice ya nufi hall din...
Kusan second biyar ya dauka yana danna wayarsa daga karshe ya fito daga motar ya zagaya ya buɗe mata suka jera amma babu wanda yayiwa dan uwansa magana.
Suna shiga hall din idan mutane yadawo kansu bakaramin kyau matching sukayi ba...