part 2

304 16 0
                                    

_Typing_

        *🤱 MAHAIFIYATA🤱*

_Writing by_

    *🌹Ameena first lady🌹*

_page3⃣ to 4⃣_

......hira sukayi sosai tsakanin da da uba har lokacin sallah ya gabato hakan yayi sanadiyyar katse hirar tasu sukayi alwala suka fita masallacin rugar dake manne a jikin gidan nasu.
Bayan sun idar da sallar Amadu ya fito daga masallacin zai tafi gida idanuwan shi suka sauka kan wasu yammata dake dibar ruwa a jikin borehole din da akayiwa rugar.
Yammata ne kyawawa dasu su uku a tare suka dauki ruwan nasu suka nufi hanyar gida,duk da haka idanuwan shi nakan wacce yaji an ambaci sunan ta da Maryam.
  Haka ya taho gida cikeda dasan sanin wacece Maryam din domin shi a take yaji yasamu matar aure a nan.....
Bayan yagama cin abinci ya fuskanci mahaifin nashi yace
"Awu wacece Maryam a rugar nan "
Awu yayi shiru na wani lokaci sannan yace "matar aure ce ko kuma budurwa,idan matar aure ce bazan Santa ba amma idan budurwa ce zan iya saninta"
Amadu yace "e to da alama budurwa ce tunda naga dibar ruwa takeyi a tuka tuka"
Awu yayi murmushi nasu na manya sannan yace"Maryam kake nufi yar gidan malam lawan ai yarinya ce mai hankali da nutsuwa kuma zan iya cemaka kaff rugar nan banga yarinya mai kunya Kamar ta ba"Amadu yace "to gaskiya Awu nifa naganta inaso"
Awu ne yai saurin cewa "to kuma ya zakayi da karatun naka da bakaso ka hadashi da aure"
Amadu yayi shiru Dan yasan Awu tsokanar shi yakeyi...

  Sosai Amadu ya kamu da San Maryam amma harya gaji da yiwa Awu magana kullum maganar dayace yaje ya nemi yardar yarinyar,kuma gashi ranar daya fara tarar Maryam din ko tsayawa ma takiyi tsabar kunya abin ma ya  bashi haushi..
Ranar wata juma'a ne Amadu ya samu mahaifin nashi yace shifa yanaso ya koma jibi saboda hutun makarantar shi ya kare Amma gashi har yanzu baiji matsayar zancan nashi ba.
Awu ne ya taushe akan su bari su dawo daga masallaci zaije gurun mahaifin ita Maryam din,sannan Amadu ya yarda..
Awu yasamu mahaifin Maryam kuma yace ya yarda zaiyiwa Maryam din maganar da kansa yaji ta bakinta.
Ansha wahala sosai kafin Maryam ta yarda amma duk da haka bata bari sun hadu da Amadu ba cewar ta bazata iya wannan abin kunyar ba, a ganta da saurayi a tsaye suna zance ba.
  
Amadu haka ya koma makaranta bayan an tsaida magana akan daya kammala karatun nasa nan da wata takwas mai zuwa za'ayi bikin.

    Amadu ya koma makaranta Yana ta tunanin wannan kunyar ta Maryam ko haduwa bata bari sunyi ba, to koma dai menene a haka yake santa...
Saura sati hudu kacal Amadu ya gama karatun gaba daya yanzu haka jarabawa suke shiyasa ya zama busy Koda yaushe Yana school Amma mama hajara kanwar maman tashi dayake hannunta itace taketa kai kawo a harkar bikin an hada lefe ba laifi,ankai rugar tasu mutane sai San barka sukeyi.

       ***************
Ranar lahadi aka daura auran Amadu da Maryam A rugar walarbe kuma a ranar aka tafi da Maryam can cikin birnin Kano gidan mama hajara mijinta ya yanki waje ya ginawa Amadu anan suka tare.
Shekarar su shida6 da aure Allah ya azurta su da haihuwar ya mace kyakkyawa sosai Dan tafi iyayen nata kyau nesa ba kusa ba ranar suna yarinya taci sunan Khadija murna a gurin kowa ba'a magana.
Saidai kuma wata sabuwa kwata kwata Maryam bata bawa khadeeja kulawa ko kadan hasali ma ko inda khadeeja take Maryam bata kalla ko nono sai anyi da gaske take bata hakan ya bawa kowa mamaki amma sai suka dauki hakan  akan watarana zata daina Amma abin Kamar ana dada tunzura ta....
Shekarar Khadija biyu da haihuwa Allah yayiwa kakanta Awu rasuwa sunsha kuka sosai sakamakon babban rashin da sukayi..
A daidai lokacin ne Amadu yasamu aiki a _VINCY COMPANY_ wato kamfanin hada takalma da jakunkuna ba karamin murna sukayi ba.
Ba'a dade ba ya fara gini a unguwar yakasai gida mai shegen kyau kowa yanata Sam barka da wannan ginin daya fara...

  Angama gini yayi tsari da kyau sosai anan ya dauko mahaifiyar shi A'i ya dawo da ita nan gidan daya gama tareda da dan mama hajara Abdulmutallib Wanda yake karatu. a B.U.K .

.....rayuwa na tafiya haka nasarori na kara samuwa ga Amadu Wanda yanzu ya zama manager na company _vinci_ Yana samun kudade sosai,ya biyawa mama hajara da A'i mahaifiyar shi dashi kanshi hajji sunje sun sauke farali..

Yanzu shekarar Khadija 6 a duniya Amma tsana tsakaninta da mahaifiyarta Maryam sai abin daya karu harta kai Khadija Koda yaushe tana wajan A'i batasan akaita gun mamanta ko kadan tsoranta takeji sosai, Dan akwai watarana da Maryam din tana zaune a palour itada  Alhj Ahmad a zaune Khadija ta shigo da gudu tayi kan mahaifinta tana wasa, cikin wasan tace "Abba ina sweet Dina dakace zaka siyomin"
Alhj Ahmad yace "jeki gun mommy ki karba nabata ta ajiye miki" a hankali ta nufi gun mamanta tace "mommy ina sweet dina" aikuwa Kamar jira take ta daga hannunta ta kwadawa Khadija mari tana ta fada"Dan ubanki ajiya kika bani koni sa'arki ce dazaki ce nabaki sweet dinki"taja dogon tsaki tabar palon
Alhj Ahmad ne ya fita da ita Yana lallashinta yaje gun Abdulmutallib yace "Abdul zoka fita da Khadija kasiyo mata sweet Dan Allah"Abdulmutallib yace "to Alhj Amma sweet takewa kuka hk Kamar an doketa kodai itada mamanta ne"
"Eh" cewar Alhj Wanda ranshi yayi mugun baci, "Allah ya kyauta"Abdulmutallib yace Yana tafiya....
Tun daga wannan ranar khadiha ta kiyayi mamanta kwata kwata ta daina shiga gunta sosai, da tadawo daga school gun A'i take wuce abinta Dama sai yamma take dawowa,

       *************
Khadeeja yammata yanzu shekarar takwas a duniya Amma sai wayo d kokari saidai batada yawan surutu tanada miskilanci, acikin wannan shekarun Uncle dinta Abdulmutallib yayi aure Alhj Ahmad ne yayi Masa gini a sharada  , matar shi Rahma akwai mutumci ga San yara hakan yasa khadeeja take yawan zuwan wajan su tayi kwanaki acan.
Haka Alhaji Ahmad ya sake saban gini a  unguwar G.R.A, A'i kuna suka barta a yakasai....
Sam A'i taki yarda a barmata Khadija cewarta su tafi da ita kila hakan yajawo su saba da mahaifiyarta Maryam idan sukaga ba idon kowa...
Khadeeja tasha kuka haka suka koma g.r.a...

           _Ku biyoni a sannu kuji yadda za'a kare_🏃‍♀🏃‍♀🏃‍♀🏃‍♀🏃‍♀

MAHAIFIYATAWhere stories live. Discover now