*🤱MAHAIFIYATA🤱*
*_KAINUWA WRITERS✍🏻 ASSOCIATION🤝🏻_*
'''{United we stand and succeed; Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
_By_📚✍
*🌹Ameena first lady🌹*
ameenamusa881@gmail.comAmeena Musa. (first lady). @facebook
Ameenafirstlady @wattpad
_page9⃣5⃣to9⃣6⃣_
___________________
Khadijah sai jidar kaya take baji ba gani.
Jin kamar maganar mutum tayi a bayan ta, wani saurayi ne tsaye farar fata daga gani Bature ne dan baiyi kama da Hausawa ba.
Gabanta ne ya tsinke ganin shaheed a bayan saurayin ya harɗe hannu fuskar nan kamar bai taɓa dariya ba.
Saida yagama kallonta sannan ya matso kusa dasu ya kalleta sannan ya mayar da kallon nashi kan saurayin.
"She's my wife" yana faɗin haka ya kalle ta "ina jiran ku" sannan ya tafi ya barsu tsaye...Shima saurayin tunda yace "ohh sorry friend" ya tafi.
Kamar ba laka jikinta haka take tafiya suna zuwa ya biya kuɗin suka nufi gida gabanta na faɗuwa..
A cikin mota sam shaheed bai sake kula taba tuƙinsa yakeyi a hankali cikeda nutsuwa har suka je gida.
A palour ya zauna itama zama tayi tana ajiye kayan dake hannun ta, shiru tayi shikam ko kallo bata ishe shiba wayar shi kawai yake latsa wa.Ƙarfin halin yi masa magana tayi. "kayi hakuri bansan wane ne shiba kawai..."
Wani irin kallo yayi mata wanda yasa ta haɗiye sauran maganar Tata.
"Ai bance miki wani abu ba ko.."
Hakuri ta sake bashi sannan ya tashi tsaye kamar zai tafi.
"Daga yau karki sake fita ko ina, har saina baki izni...."
"To" ta amsa masa babu musu.Tunda ga wannan ranar bata sake fita ba, saidai wajan su Maryam kawai take zuwa susha hira...
Yauma zaune take suna hira da Maryam kiran zainab ya shigo.,.
Da murnar ta tadaga suka gaisa. "albishirin ki Khadijah"..
"Dalla Malama ki faɗa min menene"
"I'm pregnant"
Wani tsallen murna tayi har da ihunta dai dai su shaheed sun shigo palourn tana ganinsu ta nutsu ta daina ihun...
"Congrats zainab Amma wata nawa"
"Kin gama ihun kenan, wata uku ne fa"
"Gaskiya nayi murna sosai zainab kamar na dawo gida wlhy na tayaki rainon baby"
Dariya zainab tayi "aidama nasani da kina nan da bani da wata matsala"..
Sun daɗe suna hira sannan sukayi sallama.
Maryam ta fadawa Maryam ɗin ma tayi murna sosai "ashe wannan karon zanje Nigeria kenan"
"Aikuwa dakin kyauta"shaheed taɓe baki yayi, a zuciyarsa yana faɗin "saikace itace mai cikin"
Bashir dake taya shaheed duba wasu information a computer ya kalli Khadijah.
"Kike ta murna saura ke kenan," sannan ya mayar da kanshi kan shaheed "Yakamata ka dage mutumi na kaina lokaci yayi da zaka zama baba"Murmushi shaheed yayi sannan yace"shikenan zan dage danna fahimci idan kayi aure saika zo ka wuce kabarni a baya"
Dariya sukayi shida Bashir sannan Bashir yace "kamar kasan nagano mata a Nigeria"
"Wacece" shaheed ya tambaya."Meerah mana". Shaheed baiyi mamaki ba dan tuni ya gane Bashir tun zuwa su auran shi yagane soyayya sukeyi da meerah.
"Dama ai kungama shirya kanku Sai yau kenan aka so nasani"
"Eh ɗin malam naji kuma ka sanar dasu Dad"
Dariya kawai shaheed yayi baice komai ba.
Khadijah kuwa tuni ruwa ya cinye ta tayi shiru a wajan Maryam ce tace ""ashe mun kusa shan biki". Wata uwar harara Bashir ya doka mata sannan ya buga mata tsawa yana korar ta.
Ba shiri ta fice sum sum tabar palourn.Saida sukayi dinner sannan shaheed yace Khadijah ta tashi su tafi zata tayashi haɗa kayansa dan idan ya tafi saiya gama exam sannan zai dawo.
"Amma ai zaka dinga zuwa time by time"
"Eh abbu"
"Shikenan Allah yabaka Sa'a"
"Ameen Abu" sannan Khadijan ta tashi suka tafi.
Saida tagama haɗa masa kayan sannan tace "Yakamata ka kira nazeer ka tayasu happy"
Ɗan taɓe baki yayi "ke duk kinbi kin damu kamar kece mai cikin, koda yake dama kinfi zumuɗi akan wani abu daban"
Bata sake magana ba tayi masa sallama ta tafi ɗakin ta.
Da sassafe ya fito zai tafi yayi mamakin ganinta haɗa masa breakfast, zama yayi yagama kintsa cikinsa sannan yayi mata sallama ya fice.Har wajan motar shi ta raka shi, kamar ya fasa tafiyar haka taji amma tana kallo yaja motar ya fice...
Tunda ya tafi exam ya tsare shi shiyasa baizo gida ba saidai yana kiran Khadijah sosai dan yanzu harta fara sakin jiki dashi suna waya sosai,..
Sam Khadijah bata iya kwana ita kadai dan tsoro sosai takeji hakan yasa take kwana tareda Maryam kafin dawowarsa gida..
A yau shaheed ya dawo gida danya samu interval harna sati ɗaya shiyasa ya dawo.
Taji daɗi sosai na dawowarsa saidai bata nuna masa ba, sai dare sannan suka nufi part ɗinsu.
Sun daɗe suna kallo a palour sannan ta tashi tace zata je ta kwanta.Cikin dare yauma ta tashi tsoro ya hanata komawa baccin, a hankali takejin kamar motsi a ɗakin,..
A firgice ta tashi ta fice daga ɗakin, tana tsaye a palour tana tunanin ina zata je a wannan daran, tunawa tayi ashefa shaheed yana gidan.
Bata tsaya wani tunani ba ta nufi ɗakin nasa a tsorace...Kamar a mafarki yaji ana nocking a ɗakin shi, tashi yayi ya zauna yana kasa kunne. Kwarai kuwa ɗakin shi ake bugawa to amma waye a wannan lokacin.
Tunawa yayi da Khadijah da sauri ya tashi jin an sake bugawa da karfi..
A hankali ya buɗe, "ita ɗin ce da gaske amma meya kawo ta a wannan daran ya faɗa a ransa.
Bai gama tunani ba yaga harya shige cikin dakin..
Saida ya rufe ɗakin Sannan ya jiyo ya yako inda take zaune kan kujerar dake dakin sai sharar hawaye takeyi..Haɗe fuska yayi sannan yace "lpy kika baro ɗakin ki acikin daran nan"
Cikin kuka ta faɗa masa ita tsoro takeji "gaskiya ba zan iya kwana ni ɗaya ba"
Shiru yayi sannan ya koma saman bed ya kwanta, ganin bata da niyyar tasowa ta kwanta ne yasa yace. "come and sleep"
"A'a zan iya kwanciya ma nan". Ta faɗa tana kallon kujerar.
Tsaki yayi yace "this is my room saboda haka kibi command ɗina ko kuma ki fice min a ɗaki"..
Jin ya ambaci ta fice masa a ɗaki yasa tayi saurin hawa gadon ba shiri.
Cikin ƙanƙanin lokaci bacci ya sace ta.
Shima shaheed ɗin bacci sa yayi abinsa hankali kwance..Da sassafe ta tashi ba shaheed dan tuni ya fice a ɗakin, dakinta ta koma ta shirya sannan ta nufi part ɗinsu momma...
Tunda ga wannan ranar takoma kwana ɗakin shaheed, sam bai taɓa yimata komai ba dan yayi alƙawarin har sai ta saki jiki dashi sosai tukun zan bari wani abu yashiga tsakanin su..
Yanzu Khadijah ta shaku da shaheed har bataso yayi nesa da ita, sabo mai karfi ne yashiga tsakanin su dan yanzu har hira sukeyi tare babu ɓacin rai..
Yau zai koma shiyasa Khadijah takeyin komai kamar mara lafiya, saida ya shirya sannan tafara hawaye.
Shima kamar karya tafi amma ba yadda zaiyi watanni biyu kawai suka rage masa saboda haka yafara lallashinta.
Da kyar ya samu tayi shiru sannan ya ta rakashi har wajan motar sa, harya fice suna dagawa juna hannu...Dan Allah kuyi hakuri da wannan yau.
Samun haɗu a next page✍🏻✍🏻