🌈 *_KAINUWA WRITERS ASSOCIATION_*
'''{United we stand succeed; Our ambition is entertain & motivate the mind of readers}'''https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation
Dedicated to my sweet brother
'''Shafi'u Musa. {Shafam}'''💕💞*🤱 MAHAIFIYATA🤱*
_writing by_📚✍
*🌹 Ameena first lady🌹*
_page 3⃣3⃣ to 3⃣4⃣_
Har sukaje gida ba Wanda yakara magana.
Ko parking baigama yiba Meera ta bude murfin motar zata fice.Shaheed ne ya harareta yace.
"Kinji dai abinda nafada Miki ko""Eh naji Yaya Shaheed"
Sannan ta rufe mai murfin motar yayi reverse ya sake ficewa daga gidan.
Duk iya tsokanar fadan Meera tana matukar tsoron Shaheed Dan baya yimata ta wasa idan ya kamata.
Jikinta a sanyaye ta nufi cikin gida.Khadija kuwa tunda Abba ya fara driving hankalinta ya koma kan abinda ya faru itada Shaheed.
"Me Shaheed yake nufi da ita dayayi mata wannan kyautar, kodai wani saban wulancin yake niyyar hada mata,Kai a'a da wulakanta ni zaiyi tun waccan ranar zai rama abinda nayi Masa a gaban mutane".
Haka ta dinga tunani kala kala Amma ta rasa dalilin dayasa Shaheed ya kashe mata kudi haka.
Ganin tayi shiru ne yasa Abba ya kawar da shurun.ta hanyar Kiran sunanta.
"Khadija"
"Na"am"
"Ban tambayi ya makarantar takiba""Alhamdulillahi Abba inajin dadinta sosai"
"To alhamdulillahi, yaushe zaki je gidan A'i ne" (mahaifiyarshi)
"Na dade banje ba Amma Dan Allah Abba ka kaini yanzu pls" ta marairaice murya alamun shagwaba.
Murmushi Abba yayi yace 'karkiyi kuka bari nakaiki yanzu gobe saiki dawo saboda jibi akwai school"
"To Abba nagode"
Juya akalar motar yayi suka nufi yakasai wajan A'i.
Taji dadin ganin danta da jikarta ta.
"Yaushe ka dawo ne amadu""Yau na dawo Amma tun safe"
"Shine ko hutawa bakayi ba, ka kawomin wannan fitinanniyar yar taka ta dameni"
Dariya sukayi su duka har A'in.
"Lallaima A'i abinda idan na kwana biyu banzo har kasa bacci kikeyi""Waya fada miki, bacci na nakeyi harda munshari ja'ira"
Dariya suka kuma yi.
Abbane yace "gata nan zata kwanar miki ai sai gobe zanzo na dauketa."To ka kyauta dama banda abokin hira, saigashi Allah ya jehomin ke"
Saida sukayi hira sosai har sallar magrib anan anguwar Abba yayi sannan yayi musu sallama ya tafi.Shaheed saida akayi sallar Isha sannan ya shigo palour, Meera ce kawai a palourn tana charting dinta.
"Ke bani ruwa"
Dauko Mai ruwan tayi sannan ta wuce dakinta kawai.Daddy ne ya sauko shida Mamee.
"Shaheed yaushe zakaje Lagos din ne, anyimin waya motocin sun karaso""Daddy da safe zan tafi saina dawo da yamma"
"Ok jirgi zakabi kenan"
"Eh dad bazan iya zaman mota ba""Saika shirya da wuri zansa ayi maka komai yanzu"
"To dad" sannan yayi musu sallama ya wuce part dinsa.Saida yayi wanka ya zura light blue din jallabiya sannan ya kwanta.
Tunani yafarayi akan abinda ya faru dazu."Ta fara zuwa hannu, a hankali zata gane kuranta, Dan iska zata gane me kalmar iskanci take nufi"
Murmushin mugunta yayi sannan yaci gabada tunanin duniya.Da sassafe yabi flight din safe ya tafi Lagos, ya taki sa'a motocin sun karaso ba bata lokaci ya zabi wacce yakeso.
Mercedes-Benz ce 350mblack color.
Saida aka taho da ita Kano sannan ya shima ya biyo flight na yamma ya dawo gida.Khadija ma 5:48 Abba yaje ya dauko ta.
A palour ta samu Mommy, tayi sallama sanin bazata samu mai amsa mata ba ta wuce Kai tsaye dakinta.
Yau Monday kowa yashigo makaranta harda Zainab da khadija.
Shaheed kuwa yau a makare yazo tunda ya shigo kallo ya koma kanshi saboda motar daya shigo da ita.
Wadanda suka San kudin motar mamaki ne ya cikasu Amma ganin Shaheed ne aciki sai suka daina mamaki sunsan yafi karfin hakama,wadanda basu San kudinta ba kuwa sai binta ido kawai sukayi.Ko su nazeer bai nema ba ya nufi gun khadija.
Zainab na hango shi ta tashi tabar wajan Dan haryanzu tsoron shi take.
Khadija kuwa ko gezau batayi ba harya karaso.
Yayi sallama ta amsa Masa taci gabada abinda takeyi.
Saida tagama ta dago ta kalleshi, bakaramin kyau yayiba ya birgeta ba laifi saboda Shaheed akwai tsafta.
"Na manta banyi maka godiya ba rannan, thanks"Harta gama Yana kallanta saida tagama sannan yayi murmushi yace.
"Ur welcome, but ai tun alokacin yakamata kiyi godiyar""Banga dama bane ai dama ba rokar ka nayiba"
"Ohh hakane fa baki rokaba nayi, Amma aikin karba ko"ya fada Yana cigabada murmushi mai khayatar wa."Me kake nufi da Amma na karba, Koda na karba aiba using zanyi dasu ba, zan dawo maka da kayanka"
Murmushi ya kumayi yace.
"Malama karya kikeyi ba wani bakiyi using dasu ba, bayan wannan watch din harda shi a cikin kayan"Kallan agogon hannun ta tayi taga Wanda abbanta ya siya matane.
Ganin Yana murmushi ne tagane tsokanar ta yakeyi.Tsaki tayi ta koma ta zauna.
Usman da Nazeer neman Shaheed sukayi saida aka nuna fada musu anganshi da wata yarinya sannan suka gane Yana tareda khadija kenan.A wajan suka sameshi shida khadijan kowa yayi shiru.
"Ashe kana nan kabarmu munata nemanka" inji Usman.
"Eh Ina nan ga wacce akace tana ta nemana shine nazo naji ko lafiya take nemana"
"Take nemanka kuma"? Nazeer ya tambaya da mamaki.
"Zanyi maka karya ne gatanan ai saika tambayeta kaji""To Amma Banga motar kaba ko a kafa kazo ne"
"A'a itace tace karna kara zuwa da waccan motar tagaji da ganinta Wai shine na sake wata"
"Wacece kenan"cewar nazeer
Khadija ya nuna da hannu yace "gata nan"
Mamaki ya gama cika khadija takasa magana ma kwata kwata.Nazeer ne yakasa shiru yace.
"Yaushe kuka shirya kanku bamu saniba, sai ganin ku mukayi tare""Jiya muka shirya a jiyan ma har yawo mukayi tare shinema tace batasan kalar waccan motar saidai na sauketa, nikuma bazan iya barinta ta hau ta hayaba, shine mukaje ta zabamin wata motar"
Kasa danne abin tayi ta Mike Dan tagaji da jin wannan uwar karyar dayake shiryawa da alama kuma sun yarda.
"Kai Shaheed karkayi tunanin Dan na karbi kayan jiya a hannun ka hakan Yana nufin zaka samu damar fadar kowacce irin magana, zan dawo maka da kayanka saika fita harkata"
Ana haka Zainab ta karaso wajan duk taji abinda khadija ta fada mamaki ne takamata yaushe akayi haka Amma khadija bata fadamata ba.
Mutane hankalinsu yafara dawowa wajan, wasu na fadin "wadannan sun fara halin nasu maga Wanda zai hakura acikinsu.
Murmushi Shaheed yayi ko gezau baiyiba ba daganin mutane dama gaka yaso, matsowa yayi dab da ita yace.
"Khadija a yadda mukayi dake jiya munyi dake zaki bayyana soyayyar mu a gaban yan makarantar nan Kamar yadda kamar yadda haduwar mu mukayi a gabansu, meyasa ganin su zaisa ki sauya shawara khadija, why"?
Tunda yafara maganar mamaki ya bayyana a fukar yan makarantar musamman wadanda marin da khadija tayiwa Shaheed akayi a gabansu.
Zaiban, nazeer, duk mamaki suke, Amma banda nazeer dan yasan komai.Idanuwan yan makarantar khadija take kallo da alamar. Kowa ya yarda da maganganun Shaheed din.
Innalillahi kawai take maimaitawa a ranta saboda yagama daureta da jijiyoyin jikinta gashi ba damar ta karyata tunda sun yarda.